APC ta zargi PDP da tayar da rikici a Hadeja
Mataimakin dan takarar Gwamnan Jihar Jigawa a karkashin Jam’iyyar APC Barista Ibrahim Hassan Hadeja ya nuna damuwa kan kai masa hari da ya zargi magoya bayan Jam’iyyar PDP da yi a garin Hadeja. A wata sanarwa da y araba wa manema labarai a Dutse a shekaranjiya Laraba, Barista Ibrahim Hadeja ya ce an samu tashin […]
Mataimakin dan takarar Gwamnan Jihar Jigawa a karkashin Jam’iyyar APC Barista Ibrahim Hassan Hadeja ya nuna damuwa kan kai masa hari da ya zargi magoya bayan Jam’iyyar PDP da yi a garin Hadeja.
A wata sanarwa da y araba wa manema labarai a Dutse a shekaranjiya Laraba, Barista Ibrahim Hadeja ya ce an samu tashin hankali da ya jawo kone gidaje a kauyen Gishnayo da ke karamar Hukumar Kirikasamma, inda ya ce “Mutum hudu sun samu mugun rauni suna kwance a Babban Asibitin Hadeja.”
Shaidu sun ce rikici ya barke ne lokacin da dan takarar Sanata na PDP a mazabar Hadeja Adamu Sarawa wanda shi ne Shugaban Majalisar Jihar a yanzu ya bude ofishin kamfe dinsa.
Barista Ibrahim ya yi zargincewa “dimbin ’yan bangar siyasa dauke da miyagun makamai sun rika tayar da hankalin jama’a a yankin. Mutane yankin sun rika tambaya yaya za a bude ofishin kamfe saura awa 48 a dakatar da kamfe,” inji shi.
Ya ce wannan ya sa jama’a tunanin cewa PDP ta rasa tagomashi, don haka ne ta koma ga dabarun tayar da hankalin jama’a tare da jawo yadda za a kasa gudanar da zabe cikin kwanciyar hankali.
“Duk da yarjejeniyoyin zaman lafiya da aka sanya wa hannu a bukukuwa masu kayatarwa a sassan kasar nan, ya nuna wasu daga cikin wadanda suka sanya hannu suna rikon sakainar kashi ga batun gudanar da zabe cikin kwanciyar hankali,” inji shi.
Ya ce tayar da hankali da magoya bayan PDP suka yi a Hadeja lokacin bude ofishin kamfe na Sarawa ya tabbatar da cewa sun yi watsi da yarjejeniyar zaman lafiyar.