APC: Tafiya maganin gari mai nisa
Yau da gobe ba su bar komai ba, ga shi yanzu kudurin da jam’iyyun da suka yi hadaka don ganin sun dunkule wuri guda don kafa wata sabuwar jam’iyya, Alliance for Democracy, APC cikin watanni hudu, sun kawo karshe, sa’annan kuma hakarsu ta kusa cimma ruwa. Wadannan jam’iyyu sun fahimci muhimmancin fara shiri da wuri […]
Yau da gobe ba su bar komai ba, ga shi yanzu kudurin da jam’iyyun da suka yi hadaka don ganin sun dunkule wuri guda don kafa wata sabuwar jam’iyya, Alliance for Democracy, APC cikin watanni hudu, sun kawo karshe, sa’annan kuma hakarsu ta kusa cimma ruwa. Wadannan jam’iyyu sun fahimci muhimmancin fara shiri da wuri game da gagarumar tafiya mai nisa da ke gabansu, ba su kuma tsaya yin bori da sanyin jiki ba. A harkar rayuwa mutum bai bukatar yin guzurin abubuwa biyu idan zai tafi sabon wuri, domin kuwa zai same su baja-baja a can: wadannan abubuwa kuwa su ne masoya da makiya, ko kuma a ce mahassada.
To wannan sabuwar jam’iyya ta wadatu da dukkansu tun daga ranar da aka tsuguna, aka haife ta. Ta samu daukaka da tagomashi daga jama’a a ko ina a fadin tarayyar kasar nan, ta kuma zame tamkar gamzakin da ya yi wa kyakkyawar safiya shamaki. A wani bangaren kuma fitowar wannan sabuwar jam’iyya ya kada hantar wasu, da yawa kuma sun razana ainun ganin cewa watan shan kunyarsu ne ya tsaya, domin dubunsu za ta cika, kuma karshensu ya zo. Cikin dan lokaci kankane sai ga shi nan jam’iyyar ta fi tsufa bakin jini, manyan ‘yan adawa kuma ba su kaunarta sai ka ce mutuwa. Saboda haka nan babu irin abin da ba su yi ba don a tabbatar an kai ta kasa.
Tun daga lokacin da jam’iyyun hadakar suka faro tafiyarsu a watan Fabrairun wannan shekarar ba su sassauta sassarfar da suke yi don kai wa ga nasara ba. Sun yi ta taka-tsantsan da dukkan ka’idojin da dokokin zabe suka fayyace game da dunkulewar jam’iyyu da sunan wata jam’iyya daban. Da yake wannan shi ne karo na farko na yin haka a tarihin siyasar kasar nan, sai wadancan jam’iyyun hadakar suka shiga kaffa-kaffa da sharuddan da ya kamata kowaccensu ta bi don samun amincewar hukumar zabe ta kasa baki daya, wacce ita ce ke da alhakin yin rajistar.
Da farko dai jam’iyyun sun amince a tsakankaninsu game da narkewar ko waccensu don tsiyayewa cikin wata jam’iyya guda, inda za su daskare da wani sabon suna. Baicin haka nan kuma sun tsara tambari da launuka da kuma alamar sabuwar jam’iyyar da suka radawa suna All Progressibe Congress, APC. Daga nan kuma sai kowacce jam’iyya ta yi babban taro na kasa a lokuta daban-daban, inda ’ya’yanta suka amince da batun narkar da jam’iyynsu da kuma dunkukewarsu cikin sabuwar jam’iyya da suka yi amanna da sunanta.
A yanzu wadannan jam’iyyun sun dauki matakin karshe na kammala dukkan sharuddan da hukumar zabe take bukata kafin yin rajistar: watau aikewa da takardun bukatar haka, wadanda shugaba da sakatare da kuma ma’ajin kowacce jam’iyya suka sanya wa hannu. Sannan suna tsumayin jin ta bakin hukumar zaben ce, wacce cikin kwanaki 30 daga ranar 5 ga watannan, sa’ilin da aka gabatar da takardun, za ta yi nazarin bukatun, idan kuma aka ji shiru, ba ta ce komai ba bayan karewar wannan wa’adin, to rajista ta tabbata.
Masu iya magana sun ce ba hawan ba saukar. Jam’iyyun adawa sun dukufa, ka’in da na’in don neman kafar da za su iya kurdawa don yin amfani da hukumar zabe ko kuma kotuna wajen dakile kokarin jam’iyyar na samun rajista. Babbar barazanar da jam’iyyar APC ta fara samu ita ce ta wata jam’iyya mai lakani kusan irin nata, wacce ake kira African Peoples’ Congress, APC da ta fito neman rajista daga hukumar zabe, jim kadan bayan jam’iyyun siyasa uku sun bayar da sanarwar kafa tasu. Ita dai wannan jam’iyyar ta biyu rajista ce kawai take nema, ba kaman waccan ta farko ba da jam’iyyu uku ne ke kokarin dunkukewa wuri guda. Hukumar zabe ta ce ba za ta yi wa APC ta biyu rajista ba, ita kuma jam’iyar ta garzaya kotu don kalubalantar matsayin hukumar zabe game da batun rajistar. Dangane da haka ne ake fargabar cewa gwamnatin jam’iyyar PDP na iya tankwara hukumar zabe ta nemo wani laifin da za ta shafawa wadancan jam’iyyu don hana su rajista, duk kuwa da cewa shugabannin hukumar sun saba laya cewa babu wani mahalukin da ya isa ya hana hukumarsu yi wa jam’iyyar APC ta farko rajista, muddin ta cika ka’idojin yin haka.
To amma ai ‘yan adawa cewa suke yi idan an san wata ba a san wata ba, karar da waccan jam’iyyar da aka hana rajista ta shigar gaban kotu na nan, ba ta kau ba, kuma ana iya amfani da ita don raba gardama tsakanin jam’iyyun APC ta farko da ta biyu, ta hanyar kin yi wa dukkansu rajista. An ce maso abinka ya fi ka dabara, duk irin sammako da kokarin da jam’iyyun hadaka suka yi don neman rajista ba su iya hana bullo da wata kutungwila don a kawo masu cikas game da haka. Ta ko ina aka dubi batun yi wa jam’iyyar APC rajista sai a fahimci cewa hakan zai yi tasiri ga zaben 2015, domin kuwa rashin adalci daga hukumar zabe, ko kotunan da suka saba hada baki da ita, zai iya kawo babbar jidali a kasar. Jam’iyyar APC dai ta yi doguwar tafiya kuma ya kamata a ce ta kai garin da ta dosa, komai nisa da sarkakiyar da ke bisa hanyarta kuwa.