APC za ta fafata da NNPP a zaɓen ƙananan hukumomin Kano

APC ta ce dukkanin masu sha’awar takarar su kai takardar nuna sha’awa ga ofishin jam’iyyar da ke ƙananan hukumominsu.

APC za ta fafata da NNPP a zaɓen ƙananan hukumomin Kano

Screenshot

Jam’iyyar APC ta ce babu gudu ba ja da baya wajen shiga zaɓen ƙananan hukumomin Kano da za a gudanar a ranar 26 ga watan Oktoba mai zuwa.

Kakakin jam’iyyar APC a Kano, Honorabil Ahmad S. Aruwa ne bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Alhamis.

A cewar Aruwa, bayan karɓar rahoton kwamitin da ya tattara shawararwari don shiga zaɓen, jam’iyyar ta yanke hukunci shiga zaɓen a matsayinta na jam’iyya mai mulki a Nijeriya.

Sanarwar ta kuma umarci dukkanin masu sha’awar tsayawa takara da su kai takardar nuna sha’awa ga ofishin jam’iyyar da ke ƙananan hukumominsu daga ranar 12 zuwa 14 ga watan Satumba.

Idan za’a iya tunawa a kwanakin baya Jam’iyyar APC ta Jihar Kano ta kafa wani kwamiti ƙarƙashin jagorancin Rabi’u Sulaiman Bichi, domin duba yiwuwar shigar jam’iyyar zaɓen ko akasin hakan.

Sai dai a jiya Laraba kwamitin ya miƙa rahotonsa, inda jam’iyyar ta amince za ta shiga a fafata da ita a zaɓen ƙananan hukumomin da ke tafe.

Tags