APC za ta iya kawar da rashawa kuwa?
A ranar Alhamis din makon jiya ne jam’iyyar All Progressibe Congress, APC ta gabatar da daftarin manufofinta guda goma a Abuja don yakin neman zaben shekara mai zuwa wadanda suka hada da kirkiro hukumomin ’yan sandan jihohi da bayar da ilmi kyauta a dukkan matakan koyarwa da kuma yaki da rashawa, ba sani, ba sabo. […]
A ranar Alhamis din makon jiya ne jam’iyyar All Progressibe Congress, APC ta gabatar da daftarin manufofinta guda goma a Abuja don yakin neman zaben shekara mai zuwa wadanda suka hada da kirkiro hukumomin ’yan sandan jihohi da bayar da ilmi kyauta a dukkan matakan koyarwa da kuma yaki da rashawa, ba sani, ba sabo. Akwai kuma batun samar da guraben aiki guda 20,000 a kowace jiha da farfado da aikin gona da inganta dabarun samar da gidaje da kyawawan dabarun tsaron kasa da kare lafiyar jama’a. Sauran su ne rarraba wa fakirai miliyan ashirin da biyar Naira dubu biyar-biyar kowane wata don su tayar da komada da kuma bayar da alawus ga wadanda suka kammala yi wa kasa hidima.
Babu shakka wadannan kyawawan manufofi ne, ko kuma alkawura da za su sosa wa talakawa inda ke yi musu kaikayi, za su kuma iya shafa musu mai a baki ganin irin halin matsin da ake ciki wanda ke sa mai kudi na kara kudancewa matalauci kuma na kara talaucewa. Ana iya cewa jam’iyyar APC ta yi tunani mai zurfi game da haka, musamman ma ganin cewa ita ce mai dakin da talakawa ke ciki, ta kuma fi sanin inda yake yoyon ruwa da kuma dabarun yabewa.
To amma idan aka yi la’akari da kyau game da wadancan manufofin, sai a fahimci cewa bambancin da ke tsakaninsu da na sauran jam’iyyun dan kalilan ne, bai taka kara ya karya ba. Yawancin jam’iyyun kasar nan ba su tunanin hanyoyin fadada harkokin tattalin arziki yayin tsara manufofinsu, sun fi sha’awar bin hanyoyin karfafa tattalin arzikin wasu kasashe sa’ilin da tasu ke tsiyacewa. Ba su bin ingantaccen tsarin da zai tallabi masana’antun kauyuka da za su sarrafa amfanin gona kafin a kawo su manyan birane don samar da kayayyakin da za a wadata kasa da su, irin wadanda ake shigowa da su kullum daga wasu kasashe. Ta haka ne ake sayo kayayyakin da aka kekkera da nufin rarrabawa ga matasa da matan da ba su da aikin yi wai don a dakushe masu kaifin fatara alhali kuwa ana iya kekkera su a nan cikin gida don dimbin matasan da ba su da aiki su samu abin yi, sa’annan kuma masana’antumu su habaka. Wannan ne ke sa masana’antun kasar Turai ke bunkasa, ’ya’yansu ba su zaman banza, wadanda ma ba su da abin yi suna samun alawus din da zai hana su shiga halin kaka-nika-yi.
To amma duk da cewa wannan babban matsala ce, akwai guda biyu da suka dame ta, suka shanye. Wadannan kuwa su ne rashin ingantaccen shugabancin da zai tserar da kasar daga kangin Yahudu da Nasara, wadanda ke amfani da shugabanninmu wajen satar dukiyarmu, suna tsibewa a bankunan kasashensu, hakan kuma na kara karfafa tattalin arzikinsu. Abu na biyu kuma shi ne rashawar da ta yi kaka-gida, aka kasa kai ta kasa, kuma duk wanda ya ce zai yi galaba a kanta sai ta ga bayansa. Wannan al’amari ya kazanta a Najeriya, har ma idan mutum bai shiga cikin sabgar rashawa ba, sai a mayar da shi wani bagidaje, santolabi, wanda bai son ci gabansa da na iyalansa. Abin da ke sa jama’a na dawowa daga rakiyar gwamnatocin da suka taba dankar ragamar mulkin kasar nan shi ne rashin tabukawarsu wajen yakar masifar rashawa. Shi ya sa talakawa ke tabbatar da cewa ai rashawar ce ta kai shugabanni matsayin da suke, to ta yaya mutum zai yaki uwargidarsa?
Mun sha jin ana cewa shugabannin wasu gwamnatoci da suka shude tamkar waliyyai suke, ba su dulmuya hannayensu cikin baitul-mali ba, amma gwamnoninsu da manyan jami’an gwamnatocinsu ko gafiya ba ta kai su sata ba. Idan da shugabannin gwamnatocin kasar nan na dagewa wajen sanya idanu kan na kasa da su, wanda duk ya yi, a yi masa, komai fadin ofishinsa da girman kujerarsa, ai da ba haka ba. Ai sallah daga liman takan baci, kuma mutanen Sin na cewa idan kifi zai baci daga kai yake fara rubewa.
Matsalolin kasar nan dai sanannu ne, kuma idan da jam’iyyar da ke bisa mulki ta ga dama da a gobe-goben nan za a magance su, a kawar da su dungurungum, Najeriya ta komo sabuwa, ba ruwanta da fitintinun zamani. Ai kusan dukkan abubuwan da jam’iyyar APC ta warware a matsayin manufofinta na inganta matsayin Najeriya da kyautata wa ’ya’yanta ba wanda ya sha bamban da na jam’iyyar PDP mai ci, amma ga shi nan ba a rabu da Bukar ba. Wai shin shugabannin dukkan jam’iyyun ba daga cikin talakawa suke fitowa ba? Ai kowace al’umma takan samu warki ne daidai kugunta, watau shugabannin da ke da hali da ra’ayi irin na mutanensu.
Manufofin jam’iyyar APC sun burge talakawa, kuma idan har za ta samu shugabannin da za su yi tsayuwar mai daka wajen aiwatar da su, ba tare da biye wa Yahudu da Nasara ba, to ba makawa za ta kai kasar gaci; amma fa sai idan ta daura damara da yaki da rashawa da wadanda suka daure mata gindi. Idan ba haka ba kuwa, ita ma za ta rikide, ta zama tamkar PDP, domin kowane gauta ja ne, sai dai bai shiga rana ba.