‘APC za ta lallasa PDP a zaben 2015 a Bauchi’

Mai neman tsayawa takarar dan Majalisar Tarayya daga mazabar Bauchi a karkashin Jam’iyyar APC Alhaji Yusuf Ibrahim Bauchi ya ce jam’iyyarsu ta APC, za ta lallasa PDP a zaben Gwamnan Jihar da na Shugaban kasa a badi, sakamakon yadda PDP ta gaza samar da kayayyakin more rayuwa ga ’yan Najeriya.Alhaji Yusuf ya bayyana haka ne […]

‘APC za ta lallasa PDP a zaben 2015 a Bauchi’
‘APC za ta lallasa PDP a zaben 2015 a Bauchi’

Mai neman tsayawa takarar dan Majalisar Tarayya daga mazabar Bauchi a karkashin Jam’iyyar APC Alhaji Yusuf Ibrahim Bauchi ya ce jam’iyyarsu ta APC, za ta lallasa PDP a zaben Gwamnan Jihar da na Shugaban kasa a badi, sakamakon yadda PDP ta gaza samar da kayayyakin more rayuwa ga ’yan Najeriya.
Alhaji Yusuf ya bayyana haka ne lokacin da yake zantawa da Aminiya kan yadda aka gudanar da aikin ba da katin zabe na dindindin, inda ya ce tun daga1999 zuwa yau babu abin da PDP ta tsinanawa ’yan Najeriya sai talauci da kama-karya saboda rashin iya gudanar da mulki.
Ya ce PDP za ta fuskanci kalubale mai yawa a zaben 2015, sakamakon yadda ta gaza kare rayuka da dukiyoyin ’yan Najeriya.