APO-7: Wasika daga Barzahu (2)
Allahu Akbar! Allah Ya jikan Gamji mazan jiya. Allah Ya jikan Janar Murtala. Ka ji sojan da ba a taba yin kamarsa ba cikin ’yan Arewa. Da Arewa ta taba samun kanta cikin irin wannan halin, shi ya jagoranci ’yan uwansa sojoji daga wannan sashi na Najeriya suka fitar mana da kitse daga wuta. Ba […]
Allahu Akbar! Allah Ya jikan Gamji mazan jiya. Allah Ya jikan Janar Murtala. Ka ji sojan da ba a taba yin kamarsa ba cikin ’yan Arewa. Da Arewa ta taba samun kanta cikin irin wannan halin, shi ya jagoranci ’yan uwansa sojoji daga wannan sashi na Najeriya suka fitar mana da kitse daga wuta. Ba son duniya, ba tsoro.
Yau babu irin wadannan manyan mutane. Ka duba abin da ya shafe mu. Mai ba Shugaban kasa shawara a kan tsaro – wanda kuma a karkashinsa Hukumar SSS take – Basakkwace ne dan uwanmu. Hasali ma, jikan Shehu ne. Shugaban ’Yan sandan Najeriya Bazamfare ne dan uwanmu. Mataimakin Shugaban kasa dan uwanmu ne. Haka shugabannin majalisun tarayya biyu, duk ’yan Arewa ne. Akwai gwamnonin jihohinmu na Zamfara, Kano, Katsina, Yobe da sauransu. Wani mai sharhi har ya ce, “Ga Sarkin Musulmi. Ga Gwamnan Neja. Lokacin da aka kai harin bam a Madalla, nan da nan ya je wurin yana ba da hakuri. Da kyar Sarkin Suleja ya sha da Gwamnan ya sauke shi don kawai bai gan shi a wurin ba lokacin da ya zo. A kanmu kuwa da sauran mutane kamar Mamman Shuwa, kowa ya yi shiru. Amma da an taba duniyarsu ne kamar mukaminsu ko siyasarsu da sun cika duniya da babatu.” Allah Ya shirye su da mu baki daya, don mu ma mabiyansu ba kanwar lasa ba ne.
Don haka ba mamaki idan mu karabiti aka kashe mu aka kira taron ’yan jarida aka gaya wa duniya cewa wai wasu ’yan Boko Haram da aka tsare wurin SSS sun tsegunta musu cewa mu ’yan Boko Haram ne, wai muna da miyagun makamai, wai an zo a tone makaman sai kawai muka bude wa jami’an tsaro wuta. Ashe da aka gaya musu haka, da ba su aiko da ’yan sandan ciki suka yi bincike ba, don su tabbatar da gaskiyar abin da aka gaya musu kafin su auka mana? Ashe haka hukuma ke yaki da Boko Haram? Ina ka’idojin yaki da sojojin Najeriya ke da’awar suna bi? Ina kwarewarsu da babban hafsansu Ihijerika ya ce ya cimma cusawa a cikinsu?
In dai irin wannan aika-aikar ce da karyar hukuma, mun san ba a kanmu aka fara ba. Duk wanda ya biya jami’an tsaro a Najeriya, to, abin sauki ne a Najeriya su biya masa bukatarsa sannan su tafka wa duniya karyar cewa wanda suka zalunta mai laifi ne. Muna tuna lokacin da ’yan sanda suka auka gidan Shata a zamanin Shagari saboda yana hamayya da wani shugaban NPN a tsohuwar Jihar Kaduna. Hujjar da suka bayar a lokacin kamar wacce suka bayar ne yau a kanmu. Daga baya, Shata ya yi masa wakar zambo a wakar Hauwa Maituwo yana cewa:
An ce akwai igwa hudu dakina
Akwai mashin gan kana akwai gurnet
Wai har ina da bam, inji ‘yan sanda
Da injin kudi gidan Mamman Shata
Kai ku zo nan ku bincika su ku gane su.
A 2006, akwai “Apo-6”, samarin Ibo shida da ’yan sanda suka harbe da dare a kan titin Abuja suka yi musu sharri wai ‘yan fashi ne. Tunda su sun fito daga kabila ce shafaffiya da mai, wacce take da jaridu da kafofin watsa labarai, sai duniya ta dauki dumi tilas hukuma ta kama ’yan sandan da suka kashe su ta hukunta su.
Allah dai kawai ya san mutum nawa suka iso wurin nan ta hanyar sharrin jami’an tsaro a Najeriya. Wasu an bi musu kadinsu, wasu kuwa sun tafi a maho. Ga mu a nan, ba mu da iko mu bi namu kadin. Dama, koda kuwa muna raye ne ba abin da za mu iya yi. Amma sai ga shi Allah Ya kawo mana agaji ta fannoni masu yawa.
Za mu fara da godiya ga ’yan jaridar da suka yi maza suka binciki gaskiyar al’amarinmu, suka gano zuki ta-mallen da Hukumar SSS ta gaya wa duniya. Muna kara godiya kuma muna fata za su ci gaba da sa ido kan sha’aninmu. Mun yi murna da yau da safen nan suka kwarmata labarin shirin da jami’an tsaron ke yi na shuka bama-baman karya a ginin da aka kashe mu a cikinsa don su nuna wa duniya mu ’yan ta’adda ne.
Haka muna mika godiyarmu ga abokan sana’armu, shugabannin kungiyar masu keke-NAPEP na Abuja da suka fito karara suka nuna wa duniya cewa mu din nan mambobinsu ne masu sana’a kuma wadanda ke dauke da katin shaidarsu. Hakika, sun sauke nauyinsu a wannan lokacin. Saura su cika ladarsu ta hanyar tabbatar da sun ci gaba da yakin bin kadinmu har ranar da hukuma za ta sa a kama wannan soja da jami’an da suka kashe mu kuma suka raunata ’yan uwanmu.
Sannan muna godiya ga makwabtanmu na Apo kuarters da suka fito suka shaida wa duniya kyawon halinmu, suka ce mu ba ’yan iska ba ne. Hakika sun nuna sun girgiza da aikin ta’addancin da aka yi mana. Mun gode Allah Ya saka musu da alheri.
Muna godiya ga ’yan majalisarmu na tarayya da suka tsaya kan maganarmu, suka karbi gawarwakinmu, suka mai da su gida, aka binne mu cikin mutunci. Muna fata dayanmu da ya rage wanda ba a mika shi ga ’yan uwansa ba, za a samu ’yan uwan nasa su karbe shi don shi ma ya samu a yi masa sutura ta Musulunci a binne gawarsa.
Hakika, wannan kokari da mutane daban-daban suka yi ya nuna cewa duk da ba mu da gata a raye, an nuna mana gata a mace. Ya kuma nuna akwai sauran rahama a zukatan mutane. Mun lura cewa a cikin sharhin da ake yi a yanar gizo, mun samu ambaliyar tausayawa har daga wadanda ba addininmu daya ba. Amma abin takaici, akwai wadanda kabilanci ya yi wa kanta a zuciyarsu suna nan suna ta faman taya gwamnati da jami’anta danne gaskiya. Gaskiya kuwa curin mai ne cikin ruwan tsala.
Bayan godiya ga al’ummar da suka tausaya mana, akwai magana kwakkwara da muke son mu gaya wa wadanda suka ci zalinmu. Wallahi, tallahi, Allah ba zai bar su ba ko da kuwa sun fi karfin hukuma ta hukunta su domin mukamansu da dalilan siyasa. Yau da gobe, karyar Allah ne komai gudunsu za ta kamo su. Ga mu nan a barzahu tare da wadanda suka aikata aiki irin nasu. Matsiyatan kullum azaba suke sha, na safe daban, na yamma daban.
Misali, mun ga wadanda a duniya, a can baya, suka sa aka kashe wasu mutum takwas, na tara ya tsere, wadanda suke fuskantar tuhumar yanke kan wani wanda ya baci Manzon Allah (SAW). Suka kai yaran nan daji, suka yayyanka su gunduwa-gunduwa suka cika buhuna tara don su nuna sun kashe duka taran. Ba a kai shekara ba, duk manyan jami’an da aka hada baki da su aka yi wannan danyen aikin suka halaka. Babbansu, Allah Ya dauki ransa a hadarin jirgin sama lokacin da zai je garinsu. Haka aka rika tsinar naman jikinsa, ana sawa a cikin buhu, aka je aka binne, duniya ta rabu da mugun iri. Ba a jima ba, wanda yake biye masa shi ma Allah Ya kashe shi, aka same shi bokare kamar kaguwa a bakin gadonsa, ya mutu shi kadai sai da aka balle dakin aka fitar da shi. Haka dai Allah Ya bi su daya bayan daya, sai da Ya tara su a nan Barzahu. Ga walakiri nan na tikar shegu yau sama da shekara goma sha biyar.
Akwai kuma wanda ya faru kwanan nan lokacin da aka yi zaben 2011 aka samu bayin Allah a kauyukansu aka yi ta kashewa. Ai ba a cika shekara biyu ba, Allah Ya dauki fansa. Allah Mai saurin hukunci.
Don haka muna da yakinin cewa wadanda suka shirya kashe mu da wadanda suka yi kisan, karyar Allah da sannu za ta kama su. Za su iso nan, a yi mana shari’a a wurin da ba mulki, kudi, lauya ko ’yan uwa da za su kare su. Wannan lamarin haka yake a kowace kasa, a kowane zamani.
A karshe, muna da nasiha da za mu yi wa wadanda ke kan mulki. Su san cewa duk abin da suka yi Allah na ganinsu kuma zamaninsu takaitacce ne. Don haka su yi wa ’yan Najeriya adalci ba tare da la’akari da mukaminsu ko dukiyarsu ko kabilarsu ko addininsu ba. Dukkanmu Allah ne Ya halicce mu kuma wurinSa kowa zai koma. In sun iso wurinSa, za su iske aikinsu jibge yana jiransu: In hairan, hairan; in sharran, sharran. Da shi za su zauna, har abada.
Kuma a sani, abin da ya same mu, zai samu kowa ta hanya daban-daban, kowa da hanyarsa da zai iso nan:
Ajali ga wadansu doki
Wasu ko ajalinsu zaki
Wasu ko su mace a tafki
Wasu ko ajalinsu daki
Shi zubo musu ba a kan sani ba.
Duk da cewa an kashe mu ne don talaucinmu, ko kabilarmu ko rashin galihunmu, su ma masu gwamnati su san ba za ta bar su ba. Yau da gobe ba ta bar Fir’auna ba, kamar yadda ba ta bar nagari ba:
Dubi dai Fir’auna wai shi
Ke dagawa ba kamar shi
Har cikin ruwa ne ta bi shi
Bai haye ba ta makare shi
Bai kai ga abin da yai nufi ba.
……………………………
…………………………….
Yau ina Sarkin Musulmi?
Bello ko Abdulsalami?
Musa ko Abdulkarimi?
Sun wuce wannan mukami
Ba a san daya wanda zai rage ba.
Allah Ka gaggauta halaka azzaluman da suka kashe mu. Ka rushe mulkinsu. Ka aiko musu da bala’i, su da masu goyon bayansu. Allah Ka cin musu duk inda suke, ko a gidajensu, ko a mota, ko a sama, ko a ruwa. Na Annabi ya ce, amin.
Ku na raye akwai aiki a gabanku. Ku muke tausayawa ba kanmu ba. Mu kam mun wuce kuma daga dukkan alamu Larabarmu ta yi kyau. Jira kawai muke Juma’ar ta yi Ubangiji Ya hada mu da mafificin halitta, mu sha Alkausara daga hannunsa mafi albarka. Ku ne muka bari cikin halin ha’ula’i. In kun fid da tsoro kuka tashi tsaye ku yi rayuwa ta karama, ’ya’yanku su girma cikin mutunci. In kun ki, kuka biye wa duniya, ku ci gaba da rayuwar kaskanci. A karshe, mutuwa ta zo ta iske ku cikin wannan hali, ku rika nadamar da ba za ta amfane ku ba. Ubangiji Ya yi gaskiya da Ya ce:
“Ka ce: “Hakika mutuwar da kuke gujewa za ta riske ku, sannan a dawo da ku ga Masanin abin boye da na bayyane, Ya ba ku labarin abin da kuka kasance kuna aikatawa.”
Allah Ya jikan matattunmu. Ku kuwa da yake kuna da sauran numfashi, Allah Ya kyautata rayuwarku, Ya sa ku cika da imani. Tsira da Aminci su tabbata ga Manzon Tsira, Muhammadu cikamakin Annabawa da alayensa da sahabbansa baki daya.
Assalamu alaikum,
Sa hannu:
Ga sunayenmu da jihohin da muka fito a duniya
1. Suleiman Imran (Katsina)
2. Mamman Abdullahi (Katsina)
3. Ashiru Musa (Katsina)
4. Nura Abdullahi (Katsina)
5. Ahmed Musa (Zamfara)
6. 8. Nasiru Adamu (Zamfara)
7. Buhari Ibrahim (Kano)
8. Musa Damaturu (Yobe)