Arahar kosai

Arahar kosai Wani Bafulatani ne ya samu mahaifinsa ya ce masa: “Baffa, ina da tambaya! Wai da Wudil da Ladin Makole wacce kasuwa ta fi arahar kosai ne?” Bayan dogon nazari da tunani sai ya amsa da cewa: “To, in dai arahar kosai ne, wannan hai Wudil, amma in dai ka saya a borka ka […]

Arahar kosai
Arahar kosai

Arahar kosai

Wani Bafulatani ne ya samu mahaifinsa ya ce masa: “Baffa, ina da tambaya! Wai da Wudil da Ladin Makole wacce kasuwa ta fi arahar kosai ne?” Bayan dogon nazari da tunani sai ya amsa da cewa: “To, in dai arahar kosai ne, wannan hai Wudil, amma in dai ka saya a borka ka dongoli yagi ne, wannan aradu ai hai Ladin Makole.”
Daga Khaleel Nasir kiru, 07069191677

An ki cin biri…

Wata mata ce tana a gaban motar fasinja, sai direban ya ce mata: “Gaskiya danki yana da muni sosai.” Ina kuma sai ta yi fushi, ta koma bayan motar tana zage-zage sai wani tsoho ya ce mata: “Me kike wa zage-zage? Sai ta amsa da cewa: “Wai direba ne ya ce wa dana yanada muni.” Sai tsohon ya ce mata: “Kin mare shi kuwa? Ta ce: “A’a.” Sai ya ce mata: “Kawo birin da ke hannunki in rike maki, ki je ki mare shi.”
Daga Zaidu Ibrahim Barmo Jibiya, 09035601692

Furen karya

Wani ne aka gayyace shi daurin auren abokinsa kuma bai je ba. Washegari sai suka hadu da angon suka gaisa, sai ya ce: “Kai, amma daurin auren nan naka na jiya ya yi mutane. A lokacin nan ina ta miko maka hannu don mu gaisa amma saboda yawan mutane ba ka gani ba.” Shi kuwa angon sai ya yi murmushi ya ce masa: “Allah Sarki, ai ba a daura auren ba ma, an daga sai wani makon mai zuwa, shi ya sa ma na zo domin in sanar da kai.”
Daga Abdullahi Lawal danbaba kayauki Katsina

Marigayi

Wani saurayi ne ya amso albashinsa Naira dubu goma da dari biyar, maimakon ya je ya biya bashin da aka biyo shi, sai ya ki. Ya je ya dauki budurwarsa zuwa kantin sayar da kayan shafe-shafe, aka zuba mata duk abin da take so cikin leda ta yi tafiyarta. Da ya zo biyan kudi, sai aka ce am ba ta kayan shafe-shafe na Naira dubu goma da dari biyu. Bayan ya biya sai aka tambaye shi sunan da za a rubuta a rasidin, sai ya ce a rubuta ‘MARIGAYI.’
Daga Amiru Bakori, 07068147933