Arbeloa ya yi wa masu sukar Mbappe martani

Makomar Arbeloa a ƙungiyar na fuskantar rashin tabbas, musamman ganin yadda Barcelona ke jan ragamar gasar La Liga da tazarar maki tara.

Arbeloa ya yi wa masu sukar Mbappe martani

Kocin Real Madrid, Alvaro Arbeloa, ya fito ƙarara ya kare tauraron ɗan wasan Faransa, Kylian Mbappe, kan suka da jifan rashin kataɓus da ake yi masa bayan fitar da ƙungiyar daga gasar Zakarun Turai ta Champions League.

A bayan nan dai ana zargin Mbappe da sakaci wajen bayar da taimakon kare gida a wasan da suka sha kashi a hannun Bayern Munich, inda Jamusawan suka yi nasara da jimillar ƙwallaye 6-4 bayan sun doke Madrid 4-3 a wasa na biyu.

Sai dai Arbeloa ya yi watsi da wannan zargi, yana mai cewa ɗan wasan ya bayar da cikakkiyar gudunmawa a dukkan ɓangarori na wasa.

“Babu abin da zan zargi Kylian da shi. Ya taka leda da ƙwarewa, ya zura ƙwallo a wasanni biyu, kuma ya kasance barazana ga abokan hamayya,” in ji kocin.

Ya ƙara da cewa Mbappe ya taka rawar gani har ma a ɓangaren kare gida, yana mai cewa ya gamsu da yadda ya taka leda a wasan.

Ana iya tuna cewa an rage ’yan wasan Madrid zuwa goma bayan jan katin da Eduardo Camavinga ya karɓa a minti na 86, lamarin da ya bai wa Bayern damar zura ƙwallaye biyu a ƙarshen wasa.

Duk da haka, ana ci gaba da ɗora wa Mbappe laifi, musamman daga wasu magoya baya da ke ganin bai taka rawar da ta dace a tsaron baya ba.

Mbappe, wanda ya ci ƙwallaye 40 a dukkan gasa a kakarsa ta biyu a Spaniya, zai sake jiran samun wata damar a kaka ta gaba domin cika burinsa na lashe gasar Zakarun Turai, wanda shi ne dalilin zuwansa Madrid daga PSG.

A gefe guda, makomar Arbeloa a ƙungiyar na fuskantar rashin tabbas, musamman ganin yadda Barcelona ke jan ragamar gasar La Liga da tazarar maki tara, yayin da saura wasanni bakwai kacal a kammala kakar.

Sai dai kocin ya ƙi yin tsokaci kai tsaye kan makomarsa, yana mai cewa lamarin ba ya hannunsa, amma ya jaddada cewa babu buƙatar wani babban sauyi domin dawo da ƙungiyar kan turba mai kyau a kakar gaba.