Arda Turan ya koma FC Barcelona
Kulob din FC Barcelona ya saye dan kwallon Atletico Madrid na Sifen Arda Turan a kan Fam miliyan 24 kuma tuni dan kwallon ya kammala sanya hannu a kulob din na Barca. Sai dai matsalar da dan kwallon zai fuskanta ita ce zai shafe akalla wata shida ba tare da ya yi wa kulob din […]
Kulob din FC Barcelona ya saye dan kwallon Atletico Madrid na Sifen Arda Turan a kan Fam miliyan 24 kuma tuni dan kwallon ya kammala sanya hannu a kulob din na Barca. Sai dai matsalar da dan kwallon zai fuskanta ita ce zai shafe akalla wata shida ba tare da ya yi wa kulob din kwallo ba saboda takunkumin da Hukumar kwallon kafa ta Sifen ta kakaba wa kulob din na saye da kuma sayar da ’yan kwallo na tsawon shekara biyu. Don haka sai a watan Janairun badi ne dokar hana kulob din amfani da ’yan kwallon da ta saya za ta kare.
Arda Turan, dan asalin Turkiyya, mai kimanin shekara 28, ya bayyana farin cikinsa na canza sheka zuwa Barcelona ne a wata hira da ya yi da wani gidan rediyon Sifen a ranar Talatar da ta wuce. Ya ce duk da yake sai a watan Janairu zai fara murza leda a kulob din, amma muhimmin abu shi ne yadda ya samu damar komawa kulob din na Barca.
Sai dai kulob din na Barca ya kammala shirin aika dan kwallon zuwa kulob din Galatassaray ko na Fenerbahceda ke Turkiyya a matsayin aro don kada dan kwallon a kwashe lokaci mai tsawo yana zaman benchi kafin watan Janairun 2016.