Me Tinubu ya yi da za a sake zaben shi —Atiku
Atiku ya ce abin tambaya shi ne, “Shin mme Gwamnatin Tinubu ta yi da ’yan Nijeriya za su kara zaben ta?”
Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar, ya mayar da martani kan furucin Sakataren Gwamnatin Tarayya, Sanata George Akume, wanda ya ce ’yan Arewa su hakura da neman kujerar shguaban kasa a 2027, sai 2031 idan Tinubu ya kammala wa’adinsa na biyu.
Aminiya ta ruwaito George Akume na cewa ’yan Arewa ’yan Jam’iyyar APC mai mulki da ke son neman shugabancin kasa su hakura zuwa 2031, saboda a cewarsa, yanzu lokacin mulkin ’yan yankin Kudu ne, don haka su jira sai Tinubu ya kammala wa’adinsa na biyu.
Ya kuma bukaci Atiku, babban abokin hamayyan Tinubu a zaben 2023 daga babbar jam’iyyar adawa ta PDP ya hakura ya jira 2021.
Akume ya ci gaba da cewa idan Allah Ya nufi tsohon mataimakin shugaban kasan da zama shugaban kasa zai zama, ko da yana dan shekara 90 ne.
- Yadda dillalai ke zagon ƙasa ga shirin tallafin kayan noma
- NAJERIYA A YAU: Yadda Cin Zarafin Mata Ya Zama Ƙarfen Ƙafa A Najeriya
Amma a martanin Atiku, ya bayyana cewa zabin shugaban kasa abu ne da ke hannun ’yan Nijeriya zu zabi wanda suke so.
Ya bayyana kalaman Akume a matsayin rashin adalci, domin a halin yanzu, ’yan yankin Kudu sun mulki Nijeriya na tsawon shekara 17 ne — takwas a karkashin Obasanjo, biyar a hannun Jonathan da kuma hudu a hannun Tinubu — idan aka kwatanta da ’yan Arewa da suka yi shekara 11, uku na Yar’Adua da takwas na Buhari.
Atiku ta hannun kakakinsa, Paul Ibe, ya kara da cewa hakan rashin adalci ne, yana mai bayyana cewa zabin shugaban kasa na hannun ’yan kasa yake, sai kuma irin shugabancin da gwamnati mai ci ta yi.
Paul Ibe ya ce, abin tambaya shi ne, “Shin mme Gwamnatin Tinubu ta yi da ’yan Nijeriya za su kara zaben ta?”