Arewa ce matsalar kanta, maganin na hannunta — Wazirin Katsina

Dole mu dauki matakan da suka dace domin kare gobenmu.

Arewa ce matsalar kanta, maganin na hannunta — Wazirin Katsina

Sanata Ibrahim M. Ida, Wazirin Katsina mamba ne a Kungiyar Kare Muradun Arewa, (Arewa Consultative Forum —ACF).

Dattijon hamshakin dan kasuwa a zantawa da Aminiya, ya bayyana tushen matsalolin da ke fuskantar Arewa a yanzu ya kuma ba da shawarar yadda za a samar da mafita:

Lura da abubuwan da suke faru a yanzu, me za ka ce shi ne dalilin da ya jawo Arewa take fama tashin hankali a ’yan shekarun nan?

Akwai manyan dalilai guda biyu daya na tarihi kuma dayan na faruwa saboda yanayin da muka samu kanmu a ciki.

A tarihi, mun yi imani koyaushe cewa abubuwa za su kula da kansu.

Komai ya zo haka Allah Ya kawo, mun dogara sosai ga al’adunmu, ban-gaskiya da Allah Shi ne Mai iko a kan komai kan salon rayuwarmu.

Ko da lokacin da ake cewa abubuwa sun sauya ba za su iya ci gaba kamar yadda suke ba, ba mu yi shiri don yadda za mu karbi sauyin nan gaba ba.

Kullum muna tunanin alhamdulillah nan gaba za ta kula da kanta amma hakan bai taba faruwa ba.

Abubuwan da suka faru yau suna faruwa ne saboda mu kammu ba mu shirya ba da gaske, kuma kullum gaba-gaba suke yi, misali akwai alaka a tsakanin yawan mutanen da muke bukatar kula da su da albarkatun da suke akwai.

Alal misali, lokacin da mutum bai yi aure shi kadai ne daga shi sai bakinsa. Amma da zarar ya yi aure kuma suka haifi ’ya’ya, abubuwan da zai kula da su sun karu.

Abin bakin ciki, a Arewa mun yi imani cewa yalwar kasarmu da yanayi mai kyau za su ci gaba har abada.

A da, ruwan sama yana kai lokacin da ya saba zuwa ana samun damina mai kyau ana yin noma da girbi komai yana da kyau, kuma sauyin yanayi, ko da yake akwai, bai yi tsanani ba, saboda haka bukatun kasar noma ba ta da yawa.

Za mu iya samun damar barin wani wuri da noma mu koma mu yi noma a wani wurin.

In aka yi la’akari a tsawon lokaci, kodayake, ana samun habakar yawan jama’a wadanda yawansu ya zarce karfin arzikinmu.

Wannan ya haifar da gibi — mun samu karuwar mutane da yawa fiye da albarkatun da za su iya tallafawa wajen tafiyar da dawainiyar rayuwansu, ciki har da samar musu abinci, gidaje da ilimi da sauran bukatu na yau da kullum.

Yawan jama’a yana karuwa sosai, yayin da albarkatunmu karuwarsu ba ta kai yadda za ta iya biyan bukatun al’ummarmu ba.

Na biyu kuma, a lokacin da ake gudanar da gwamnatin tsakiya, wato lokacin akwai shiyya-shiyya, an samar da hukuma daya wacce za ta iya tsara wa yankin gaba daya abubuwan da suke bukata.

Duk da haka, wannan ya wargaje da kutsen da sojoji suka yi a 1966, kuma yayin da aka kirkiri wasu jihohi, tsare-tsare sun zama rarrabuwa kowace jiha Albarkatu sun fara raguwa yayin da ake kara karkatar da su zuwa sassan da ba su da amfani.

Mun kasance muna tunanin gaba, amma al’umma da yankin sun daina shirin gaban.

Yayin da yawan jama’a ke karuwa, sauyin yanayi ya rage yawan albarkatun da ake samu a kasa, kuma kwararowar hamada ta kara mamayewa.

Sannan samar da ingantattun ababen more rayuwa kamar -lantarki, ruwa, hanyoyi da makarantusun tabarbare.

Kayayyakin gine-gine suna da alaka kai-tsaye da samar da ayyukan yi, kuma yayin da noma ya ragu, mun kasa habaka masana’antu wadanda za su iya samar da ayyukan yi ga ma’aikatanmu da za su yi ayyuka don habaka tattalin arzikin kasa.

Samar da wutar lantarki ta ragu, masana’antu ba za su iya bunkasa ba, ci gabansu ya gaza yin tasiri don ba lantarki, kuma hakan ya haifar da rashin aikin yi.

An mayar da hankali ga ayyukan gwamnati, wanda haka ya rage kwarin gwiwar mutane don zama masu kirkirar abubuwan gina kasa, masu fa’ida da kasuwanci.

Wannan yanayin kuma ya haifar da samar da wuraren da ba gwamnati ya jawo an samu — wuraren da babu makarantu, babu asibitoci, ko tsarin tsaro.

Yayin da wadannan wurare suka girma, suka zama wuraren kiwo da ayyukan da ba su dace ba.

Tashin hankalin da muke fuskanta a yanzu bai faru cikin dare daya ba; ya ginu ne sannu a hankali.

Ko dai ba mu lura ba, ko kuma ba mu yi zaton cewa abubuwa ba za su warware kansu ba.

Yayin da yawan jama’a ke karuwa, yawancin matasa suna ganin babu wani amfani a ilimi idan bai kai ga samun aikin yi ba.

Wannan ya haifar da habakar yaran da ba sa zuwa makaranta, wanda daga nan ne suka zama babban abin da ake nufi shi ya sa ake samunsu cikin ayyukan da ba su dace ba.

Abin da muke fuskanta a yanzu ya kamata a yi tsammaninsa tun a baya, kuma a hana shi.

Abin takaici, yanzu muna fama da matsalolin da ba mu da albarkatun da za mu magance su.

Samar da ayyukan yi ga dimbin al’umma babban kalubale ne, amma koda muna da ayyukan yi, da yawa ba su da kwarewa da ilimin da za su yi ayyukan.

Arewa ta zama abin da ake cewa ta yi wa kanta, kuma yayin da yake da sauki a zargi wasu, a karshe, alhakin ya hau kanmu, ba gwamnati ba.

Kuma mun koma ba mu da tattalin arzikin da zai samar mana da ayyukan yi kuma ya magance mana matsalolinmu.

Lokacin da aka yi zanga-zanga, yara kanana masu karancin shekaru ne suka mamaye ta, galibi ana alakanta su da cewa almajirai ne. Wannan al’amari ya dade da a Arewa. Ta yaya za mu magance shi?

Batun almajiranci na da nasaba sosai da yadda muke rainon yara da kuma haihuwa. Wadanda kuka gani a lokacin zanga-zangar ne kawai aka gani.

Idan ka ziyarci unguwanninmu, kauyukanmu da garuruwanmu, za ka ga yara da yawa wadanda suke ba da gudunmawa ga rashin zaman lafiya a cikin birane.

Matsalar ba kawai ga wadanda suke bayyane ba ne; akwai wasu da yawa wadanda ba su fito sarari ba suna nan da yawa.

Idan ka kawar da na yanzu, wasu za su maye gurbinsu saboda mun ci gaba da samar da karin irin wadannan yara da ba mu shirya musu wata makoma a gaba ba.

Lokacin da ake tattaunawa kan mafita, an gano yawancinsu al’adu ne da zamantakewa.

Da alama muna fassara wasu ayoyi na littattafai masu tsarki, muna ganin ya kamata mu yi aure mu haifi ’ya’ya.

Duk da haka, na yi imani manufar ita ce yin aure da samar da al’umma tagari da samar da kyawawan halaye, ko akalla nagartattun mutane – mutanen da za ku iya kula da su.

A cikin al’ummomin da suka ci gaba, yawan mutanen da ke yin aikin farko na raguwa, amma yawan aiki na karuwa.

Wadanda a yanzu ba a bukatarsu a kananan ayyuka saboda sun yi karatu sun samu ilimi kuma yana kara musu kima.

Idan ka kara darajar mutum, zai iya samun aikin yi da kansa ko ya kirkira da kansa.

Idan ba zai iya samun aiki a gida ba, zai iya tafiya inda ake bukatarsa kuma ya zama masu amfani koda kasashen waje ne.

Wannan shi ya sa da yawa daga cikin ’yan uwanmu masu ilimi suke kaura zuwa kasashen waje — ba don babu ’yan gida a can ba, amma don wadancan kasashe suna bukatarsu.

Da zarar an kai su, ana nuna su ga kwararrun ma’aikata masu kwarewa, kuma wajen akwai ingantattun kayan aiki, fasaha da ilimi, wadanda ke sa su zama masu fa’ida.

Abin bakin ciki, kowa da kowa yana da damar yin rayuwa shiryayyiya, kuma ya kai makura a kwarewa.

Wasu mutane suna cewa lalacewar dabi’a na karuwa tare da koyi da kasashen Yamma, kafofin watsa labarai da sauran tasirin zamani.

Wane tasiri kake ganin da’a za ta taka wajen magance a matsalolin Arewa?

Bari mu fara da rukunin iyali, tushen al’umma. A da uba da uwa za su jagoranci ’ya’yansu a kan abin da za su yi.

A lokacinmu, an samu iyakataccen fallasa ga tasirin waje.

Akwai gidajen sinima, amma suna cikin kebabbun wurare, kuma dole ne ku je wurin don ganin komai.

Bayan lokaci duk da haka, fasaha ta fara kusantar duniya komai ya zo kusa.

Na tuna lokacin da nake Birtaniya, idan muna son yin waya a gida, sai mun je British Telecom, mu kama lokaci, sannan mu jira lokacin da za su hada da Nijeriya, sai Kaduna, Kano daga karshe Katsina, tsari ne mai tsayi.

Idan muna son mu aika da kudi, na yi aiki a matsayin ma’aikacin banki tun farkon aikina, kuma dole ne kun bi irin wannan tsari – zuwa banki, ku samu takarda, kuna jira a sarrafa su, amma yanzu duk wannan ya canza.

Tare da waya kawai, za ku iya magana da kowa ko aika kudi nan take.

’Ya’yanmu babu makawa sun gamu da fasahar zamani, wacce ke da bangarori masu kyau da marasa kyau.

A wurare irin su Birtaniya kimiyya ta samu ci gaba saboda wasu dalilai, musamman saboda ilimi da nishadi.

Ga misali, yara suna zuwa kwanciya ne da misalin karfe 8 zuwa 9 na dare. Amma mu a nan ba haka abin yake ba.

A shekarun baya kana barci a lokacin da ya kamata ka yi barci saboda za a rufe kofar gidanku dole ka kasance a cikin gida.

A yanzu abin ya canza domin kuwa yaranmu idonsu ya bude da wasu al’adu da ba irin namu ba a yayin tasowarsu.

Haka a yanzu ya yi daidai ne da mutumin da ke jin yunwa sai aka ba shi abinci isassshe wanda hakan na iya sa shi ya cika cikinsa har ya kai ya cutar da kansa.

Al’umma ta zuba ido ba tare da haramta ko hana abin da bai dace ba.

A shekarun baya, yara iyayensu na kare su daga wasu irin ilimomi ko al’adun da ba su dace ba, misali ba ka sanin lokacin da iyayenka ke mu’amalar aure sannan ba ka tambayar yadda ake samun ’ya’ya domin ko an fada maka cewa ta baki suke fitowa za ka yarda.

Amma a yanzu saboda wayewa zuwa ga wasu irin dabi’u duka abubuwa sun lalace.

Akwai mutane da ke samun kudi saboda irin wadannan sababbin dabi’u kuma abin na shafar al’ummarmu.

Ta bangaren amfani kuwa, kimiyya ta taimaka wajen sa karatu ya yi sauki ga kowa.

Sannan ana karatu da koyarwa da koyo a cikin sauki. Amma fa idan ba a sanya idanu ba, al’adu da dabi’unmu duka za su lalace.

Ga misali, yaro a yanzu zai iya boyewa yana kallon abin da bai kamata ya kalla ba cikin dare ba tare da kowa ya sani ba.

A wasu kasashe akwai hanyoyin kula da kuma takaita abin da ake kallo a cikin wayar hannu, domin kuwa ana karbe wayoyi kafin a kwanta, amma mu a nan mun rasa wannan tarbiyya da kwarewa ta daukar irin wannan mataki.

Shi ya sa muke ganin karancin tarbiyya a tsakanin matasanmu.

Wannan ne ya kai ga tambaya ta gaba, a shekarun baya kamar yadda ka ba da shawara akwai mutane a Arewa wadanda kalamansu ke da muhinmanci a cikin al’umma.

Amma a yanzu da aka samu yanayi abin ya canza.

Me ya faru da irin wannan shugabanci?

A Afirka ba ki dayanta, ana girmama shekaru, wanda hakan ke da muhinmanci ga iyali.

A baya, al’adu na da muhimmanci, malaminka kamar mahaifinka yake, kuma dole ka yi masa biyayya kamar yadda kake girmama iyayenka.

Saboda abin da iyayenka suka ba ka ta tabbatar da cewa ka samu abinci da wajen kwana.

Amma yanzu saboda canjin rayuwa da tattalin arziki hakan ya canza.

A yanzu iyaye dogara suke a kan yaransu, maimakon yara su dogara ga iyayensu yin haka ne ya shafi tsarin iyali.

A baya akwai karancin masu ilimi, akasari shugabannin addini ne ke fadia-ji, amma a yanzu matasa sun samu damar karanta Kur’ani da Baibul kuma suna fassarawa da kansu.

Idan wani ya nemi yi masu bayani sai su rika tambaya kamar me yake fadi ne? Ga abin da kuma na gani me zai ce?

Irin wasu bayanai na ra’ayi suka sa aka daina girmama wasu al’adu ko dabi’u sannan ga matsin tattalin arziki da kuma ra’ayoyi mabambanta a cikin al’umma.

Sannan a baya, mutanen da ake darajawa suna jawabi ne ga mutane kadan.

Amma a yanzu idan har muna son maido da darajar dabi’u dole a mayar da hankali wajen daidaita dabi’un matasa tun daga farko.

Dole a koyar da su halaye masu kyau tun suna kanana saboda su girma cikin aminci.

Kalubalen a yau shi ne, tazara a tsakanin tsofaffi da matasa na dada takurewa domin wadanda ke rike da mukaman addini ko wasu mukamai a cikin al’umma kusan shekarunsu daya ne da na wadanda suke kokarin gyara wa dabi’u ko shugabanci.

A baya akwai tazarar shekaru sosai, malaminka ya fi ka shekaru da kwarewa.

A lokutan rikici kamar wadanda muka ga an yi, akasari matasa ne a kan gaba, wannan ba abin mamaki ba ne musamman saboda zuciyar matasa babu wuya a juya ta, musamman wadanda ba su samu tarbiyya mai kyau ba.

Idan za a magance hakan, dole mu fara daga asali ta hanyar inganta karatun boko ta yadda zai karantar da dabi’u nagari ba kawai ba da bayanai ba.

Idan muka yi haka za a samu canji a yayin da suke girma.

Me kake ganin ya janyo matsalar shugabanci kuma yaya za a maido da martabar Arewa?

Dole ne a fahimci cewa shugabanci na tafiya ne da halayyar wadanda ake shugabanta.

Idan muka yi zancen shugabanni a yau su wane ne? Su ne ’yan siyasa da gwamnoni da ’yan majalisa sai kuma ’yan adawa.

Kamar yadda shugaba ne jagora gangar jiki idan kai na da isassshen ilimi da hangen nesa sauran gangan jiki zai bi shi ta hanyar kiyaye lafiya da tsabta.

Amma idan kai ba ya da bambanci da sauran gangan jiki, shugabanni sai su zama ba su da banbanci da mabiya.

Akasarin shugabanninmu ba su shirya zama shugabanni ba tun suna kanana.

Ba za ka iya canza su ba a lokacin daya, idan mutum ya girma yana da halaye marasa kyau kuma sai aka ba shi shugabanci halayensa na asali za su kasance a tare da shi.

Duk da cewa muna bukatar shugaba na kwarai amma hanyoyin zabar shugabannin akwai matsal, muna cikin rudani.

Don kawai mutum ya cancanta ba shi ke nufin zai iya shugabanci ba.

Akwai bukatar a duba tarihin mutum da kwarewarsa tare da yin kwakwaran bincike a kansa.

Abin damuwa shi ne yadda muke zaben shugabanni bai dace ba, ta yadda kowa na iya samun mulki, idan hakan ya faru abin da wadanda suka samu mulkin za su fara yi shi ne biyan bukatar kansu.

Dan Adam na da burika a zuciyarsu na biyan bukatun kansa musamman a abin da ya rasa.

Idan muna son ci gaba, dole ne shugabanni su shirya sadaukarwa, dole su fahimci akwai bukatar su kare mutuncinsu komai wahalarsa.

Idan shugaba na da dauriya da tsantseni mabiyansa ma za su bi shi.

Dole ne mu dawo da dabi’u na kwarai mu kuma fahimci cewa babu wanda ke raya mutum Allah ne Ya ba mu hankali domin mu kare kanmu.

A Arewa akwai alamun mutane su rika dogaro ga ’yan uwansu ta yadda har suke ganin kamar babu bukatar su yi aiki, dole ne a canza irin wannan tunani.

Dole mu fahimci cewa mu ne za mu gyara gobenmu. Duk wanda ya tsinci kansa a kan mukami dole ya fahimci da cewa ana kallonsa, don haka akwai bukatar su yi abin da ya dace.

Ya kamata a samar da wasu hukumomin kula da yadda ake tafiyar da mulki baya ga haka su kasance a shirye suke su sadaukar da nufin ciyar da Arewa da Nijeriya gaba.

Batun almajiranci da kuma miliyoyin yara da ba sa zuwa makaranta duk wannan halayyarmu ce ta janyo haka.

Wadannan matsaloli gwamnati ba za ta iya magance su ba ita kadai.

Gwamnati na iya samar da yanayi mai kyau amma dole mu magance matsalar daga tushe.

Janye yaran nan daga kan titi ba zai magance matsalar ba, domin kuwa da yawa za su maye gurbinsu.

Maimakon haka sai mu hada hannu da garuruwa ko unguwannin da yaran suke fitowa daga can.

A ilimantar da iyalansu da sama masu hanyoyin dogaro da kai.

Akwai kasashen da ba su da ma’adanai a kasa amma suna ciyar da al’ummarsu gaba.

Sai mun fahimci cewa al’ummarmu arziki ne tare da kula da su yadda ya kamata, idan ba haka ba kuwa za mu ci gaba da fuskantar matsaloli.

Idan har ba mu canza tsarinmu ba, karni mai zuwa zai fi wanda ake ciki a yanzu muni.

Dole mu dauki matakan da suka dace domin kare gobenmu.

Davido zai bai wa marayu tallafin N300m a Najeriya

Ba mu yanke hukunci kan ƙudirin harajin Tinubu ba — Abbas

Masu garkuwa da mutane na neman N10m kan manoma 6 a Taraba

Hotunan Gobarar Kasuwar Laranto da ke Jos