Arewa da MTN za su karrama ‘yan fim
kungiyar ‘yan fim ta Arewa Film Makers Association of Nigeria tare da hadin gwiwar Kamfanin sadarwa na MTN za su karrama fittatu da jarumai da kuma sauran masu ruwa da tsaki a harkar kasuwanci da kuma shirin fina-finan Hausa.Za a gudanar da wannan taron ne a ranar Asabar 23 ga wannan watan a dakin taro […]
????????????????????????????????????

kungiyar ‘yan fim ta Arewa Film Makers Association of Nigeria tare da hadin gwiwar Kamfanin sadarwa na MTN za su karrama fittatu da jarumai da kuma sauran masu ruwa da tsaki a harkar kasuwanci da kuma shirin fina-finan Hausa.
Za a gudanar da wannan taron ne a ranar Asabar 23 ga wannan watan a dakin taro na Afficient da ke Unguwar Nasarawa GRA a cikin Birnin Kano da misalin karfe 8:00 na dare.
Shugaban Arewa na Jihar Kano Isma’il Na’abba Afakallahu ya ce wannan biki shi ne farko, zai kuma zama sharar fage ne na jerin irin wadannan bukukuwa na karramawa da kungiyar za ta rika gudanarwa duk shekara a babban birnin tarayya Abuja tare da tallafin kamfanin sadarwa na MTN.
Ya ce: “Burinmu a wannan biki shi ne cike gibin da ake da shi a wannan masana’anta na rashin irin wadannan bukukuwa da tarurruka da aka saba yi a ko’ina a duniya a bangaren shirin fim.”
Idan ba a manta ba a baya an yi irin wadannan tarurruka daga baya aka daina amma yanzu kungiyar take son farfado da su don a zaburar da masana’antar da kuma yaba wa wadanda suka yi abin kirki.