Arewa mu dogara da kanmu
Tun kafin mamayar Turawan mulkin mallaka, yankin Arewa yana bisa kyakkyawar turbar tsarin mulki da zamantakewa mai kunshe da girmama juna, mutunta juna. Tare da nuna kauna ga juna da tausayawa juna tsakanin al’ummun yankin, duk da kasancewar akwai bambanci addini da kuma yare.Tsakanin jagororin dake mulki da kuma mabiyansu, akwai kyakkyawar alaka da fahimtar […]
Tun kafin mamayar Turawan mulkin mallaka, yankin Arewa yana bisa kyakkyawar turbar tsarin mulki da zamantakewa mai kunshe da girmama juna, mutunta juna. Tare da nuna kauna ga juna da tausayawa juna tsakanin al’ummun yankin, duk da kasancewar akwai bambanci addini da kuma yare.
Tsakanin jagororin dake mulki da kuma mabiyansu, akwai kyakkyawar alaka da fahimtar juna, talakawa sun gamsu da adalcin shugabanninsu yayin da shugabanni suka aminta da biyayyar talakawansu. Ba cuta ko cutarawa, kowa na rayuwa cikin jin dadi da walwala.
A wancan zamanin yankin yana kan tsarin tattalin arziki bisa ga dogaro da kai, domin samun kudaden harkokin rayuwa na yau da kullum. Akwai dauwamamman zaman lafiya tsakanin kabilun dake zaune a yankin. Domin kowa na kansa yake nema, duk inda yakasance akwai yalwar arziki a cikin al’umma to rikice – rikice da tashe -tashen hankula kan yi sauki.
A lokacin yankin ya dogarane kacokam akan harkar noma da kiwo, a matsayin babbar hanyar samun kudade na shiga. Sai kuma haraji. Domin yankin Allah ya huwace masa kasar noma mai albarka da kuma tarin ma’adinai iri- iri kunshe cikin karkashin kasa.
Koda turawan mulkin mallaka suka zo sun tarar da yankin arewa cikin tarin arziki mai albarka, na noma da kiwo da kuma dumbin jama’a masu yawa dake da bambancin addinai da kabilu. Sai dai suna zaune bisa kyakkyawan shugabanci da zamantakewa.
Bayan hade yankin Kudanci da kuma Arewaci da Turawan mulkin mallaka suka yi. Da sunan Najeriya a alif 1914. Yankin shike samar da kudaden tafiyar da kasa ta hanyar sayar da amfanin gona da ake nomawa. Yankin yakan samar da kudaden ne fa bayan samarwa da kasar isasshen abincin da za’a ci.
Da zamani ya zo aka fara gano man Fetur a kasashen duniya. Yankin ne ya dauki nauyin aikin gano albarkatun man Fetur dake kudancin kasarnan. Wanda bayan shafe shekaru masu yawa haka ya cima ruwa aka samu man Fetur na farko a kauyen “Oloibiri” dake cikin jihar Bayelsa a alif 1956.
Yankin dai shi ne ya dauki gaban gabarin nauyin hako man Fetur, da sunan gwamnatin Najeriya a alif 1958. Inda ake hako ganga 4,928 a duk kullum. Ba tare da yin wata yarjejeniya ba akan ba yankin wani kaso na musamman a matsayin fansa bisa sadaukantar da dukiyarsa don ganin samun nasarar aikin.
A yau an wayi gari dan kudancin kasarnan nawa dan Arewa kallon raini, tare da hura masa hanci. Akan cewa shi cima zauna ne, man Fetur nasu ne alfarmace ake mana. Sun mance da halin dattako da sanin yakamata da yankin arewa ya nuna akan ganin an fara hako man Fetur a wannan kasa tamu.
A jiya Arewa ta kasance wani tauraro dake da tsananin haske, da haskensa ya game dukkan wannan kasa tamu. To amma a yau wannan haske na arewa ya dusashe. Sabo da haka lokaci ya yi da zamu zauna muwa kanmu fada. Mu hade kawunan mu wuri guda, kowa ya bada gudumuwarsa don ganin mun mai do da martaba tare da kimar wannan yanki namu da aka sammu da shi.
Allah dai ya shimfida mana kasar noma marar iyaka mai albarka, dake kunshe da tarun ma’adinai iri – iri. Ga mashahuran attajirai da masana fannonin ilimi iri -iri da ake jin amon su a duniya. Ga dubunnan matasa nan mararsa ayyukan yi. Ya kamata mu yi wani hobbasa don ganin wannan yanki namu ya dawo cikin hayyacinsa.
Ayi wani hadin gwiwa tsakanin gwamnatocin yankin da kuma masu arziki, don gayyato kamfanonin kasashen waje domin zuba jari a harkar noma na zamani. Musamman noman shinkafa, alkama, gyada, ridi, rogo, auduga da sauransu. Da kuma mayar da hankali akan hako ma’adinai tare da sarrafa su. Ko da ta hanyar kafa kananan masana’antu ne. Yankin zai samu alfanu mai yawan gaske idan hakan ya tabbata.
Hakan zai samarwa da yankin kudade masu yawan gaske ta hanyar dogaro da kai, baya ga dimbin matasan da za su samu ayyukan yi, wanda hakan zai takaita yawaitar aikata ayyukan ashsha da ake yawan samu a cikin al’umma.
Man Fetur da ake da hamuki akansa, a yanzu an wayi gari ba wani kasuwa gareshi ba mai tabbas. A kullum fuskantar barazana yake a kasuwannin duniya, musamman bisa ga yadda manyan kasashen dake sayansa ke alakanta amfani da shi yakan kawo gurbatar muhalli. Idan kunne ya ji, jiki ya tsira. Arewa dai ta mu ce kuma mune zamu gyara kayammu. Allah taimake mu.
Injiniya Jibril Abdul Daura 08038997861, 08022997340