Arewa na buƙatar haɗa kai da Kudu Maso Kudu don ceto Najeriya — El-Rufai
A baya-bayan nan dai El-Rufai ya sa zarw da jam’iyyarsa ta APC.

Tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya buƙaci manyan ‘yan siyasa daga yankin Arewa da Kudu Maso Kudu su haɗa kai gabanin zaɓen 2027.
El-Rufai, ya yi wannan kira ne yayin da ya kai ziyarar ta’aziyya ga iyalan marigayi dattijo kuma jagoran yankin Neja Delta, Edwin Clark.
- Babu ɗan Arewa mai hankali da zai yi tallan APC a 2027 – Jigo a PDP
- Fasinjoji 4 sun rasu yayin da bas ta kama da wuta a Jigawa
A cewarsa, Najeriya tana cikin matsala mai tsanani kuma tana buƙatar ɗauki cikin gaggawa.
“A shekarun baya, Arewa da Kudu Maso Kudu sun kasance abokan siyasa,” in ji El-Rufai.
“Kada mu manta da hakan. Mu koma kam wannan haɗin kai. Mu ceci wannan ƙasa domin tana buƙatar ceton gaggawa. Dole ne mu ɗauki matakin ceton ƙasar nan.”
Maganganunsa sun zo ne yayin da ake raɗe-raɗin cewa yana shirin sauya sheƙa daga jam’iyyar APC.
A makonnin da suka gabata, ya gana da ’yan siyasa daga jam’iyyun adawa bayan wani saɓani tsakaninsa da jam’iyyar APC mai mulki da kuma gwamnatin Shugaba Bola Tinubu.
El-Rufai, wanda ya je ziyarar ta’aziyyar tare da tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, ya yaba da rawar da Atiku ya taka wajen kawo sauye-sauyen tattalin arziƙi a lokacin mulkin Shugaba Olusegun Obasanjo.
Segun Showunmi, tsohon mai magana da yawun yaƙin neman zaɓen Atiku, ya tabbatar da cewa wannan ganawar tana cikin shirye-shiryen siyasa gabanin zaɓen 2027.
A watan Janairu, El-Rufai ya gana da Hamza Al-Mustapha, tsohon hadimin marigayi Janar Sani Abacha, da Shehu Gabam, shugaban jam’iyyar SDP, da wasu ’yan siyasa a Abuja.