Arewa ta fi karfin a rika yi mata gorin arziki – Dokta Habibu Gwarzo

Dokta Habibu Muhammed Gwarzo shi ne jagoran yakin neman Jihar Ghari daga Jihar Kano. A hirarsu da Aminiya, ya ce yankin Arewa yana da muhimmanci ga Tarayyar Najeriya idan aka waiwayi tarihin kafuwar kasar nan: Aminiya: Ka kasance jagoran gwagwarmayar neman Jihar Ghari daga Jihar Kano lokaci mai tsawo, wadanne dalilai kuke da su na […]

Arewa ta fi karfin a rika yi mata gorin arziki – Dokta Habibu Gwarzo
Arewa ta fi karfin a rika yi mata gorin arziki – Dokta Habibu Gwarzo

Dokta Habibu Muhammed Gwarzo shi ne jagoran yakin neman Jihar Ghari daga Jihar Kano. A hirarsu da Aminiya, ya ce yankin Arewa yana da muhimmanci ga Tarayyar Najeriya idan aka waiwayi tarihin kafuwar kasar nan:

Aminiya: Ka kasance jagoran gwagwarmayar neman Jihar Ghari daga Jihar Kano lokaci mai tsawo, wadanne dalilai kuke da su na bukatar karin jihohi a kasar nan?
Habibu Gwarzo: To da farko dai muna yin wannan gwagwarmaya ce domin mu kara kawo ci gaba a wannan kasa tamu mai albarka, ta yadda zamantakewa za ta inganta a kowane fanni na rayuwa. Idan ka dubi ita Jihar Kano za ka ga ta yi girman da ya kamata a ce an kara mata jihohi ta yadda za a kara samun ci gaba mai amfani kamar dai yadda muke gani a jihohin da aka kirkiro a baya-bayan nan. Wannan yana daga cikin dalilan da suka sanya muke wannan fafutika yau kimanin shekara arba’in da uku.
Aminiya: Wasu suna ganin cewa jihohin da ake da su ba su da isassun kudin gudanarwa, amma kuna neman a kara wasu, yaya kuke kallon wannan al’amari?
Habibu Gwarzo: Masu wadannan kalamai na rashin kudi a hannun jihohi ba su da hujjar yin kokwanto kan kokarinmu na neman karin jihohi a kasar nan domin akwai jihohin da suke karbar kudi daga Asusun Tarayya mafi karanci, amma idan ka je cikinsu za ka yi mamakin irin ci gaban da suke samu da dan abin da suke karba, kamar Jihar Jigawa wadda aka cire daga Jihar Kano. Ai karancin kudi ba ya hana gudanar da aiki, muddin dai aka samu shugabanni masu kishin ci gaban al’umma. Sannan idan Allah Ya tabbatar mana da Jihar Ghari, za mu tsaya sosai mu dora wadanda Allah Ya bai wa jagorancinta kan sahihiyar hanya da jihar za ta inganta cikin kankanen lokaci, kuma koda ba ma wannan duniya, ai muna da sahihan mutane a yankin Jihar Ghari wadanda za su dora daga inda za mu tsaya cikin yardar Ubangiji. Idan har Allah Ya tabbatar mana da mafarkinmu na samun jJihar Ghari, to muna da dukkan abubuwan da ake bukta na gudanar da ayyuka domin idan ka duba, a kananan hukumomin da suke cikin jadawalin jihar ta Ghari, akwai abubuwa da suka shafi ma’adinai da fadamu da filayen noma da sauran muhimman abubuwa da za su taimaka mana wajen bunkasa jihar cikin lokaci kankane. Don haka batun karancin kudi kawai magana ce ta mutane wadanda watakila ba su san luggogi na tafiyar da gwamnati ba, koda kuwa tana da karancin kudi a hannunta. Ai idan aka waiwayi tarihi yankin Arewa shi ne yankin da yake rike da kansa ta fannin noma da fatu da kiraga tun ma kafin a samu man fetur da ake yi wa Arewa gori a kansa, har ana cewa wai ’yan Arewa su ne cima-zaune saboda rashin sanin tarihi. Wajibi ne duk jihohin da aka kirkiro a wannan karni su tashi tsaye wajen kara bullo da hanyoyin samun kudin gudanar da ayyukan raya kasa kafin a ce suna jiran kaso daga Gwamnatin Tarayya.
Aminiya: Amma masana tattalin arziki suna ganin cewa karin jihohi zai kara yawaita matsaloli a kasa, yaya kuke ganin wannan batu?
Habibu Gwarzo: Wannan magana ba haka ba ne, domin tattalin arziki yana hannun masu mulki na kowane mataki. Amma idan muka tsaya muka alkinta noma da kiwo da sarrafa ma’adinan da Allah Ya shimfida a kasarmu da mutanen da muke da su masu matukar basira ai za mu yi kafada-da kafada da kowace jiha ta kasar nan saboda yadda za mu sanya kishin kasa. Haka kuma shi kansa man fetur din da ake mana gori a kansa, ai akwai shi a yankinmu na Arewa kamar Bauchi da Borno amma makirci ya hana a hako shi, don haka lokaci ya yi da ’yan Arewa za mu farka mu yi kokarin ganin yankinmu ya zarce tsara ta yadda kowa zai ji dadin albarkar da yankin ke da ita.
Aminiya: Taron kasa ya baza zabin karin jihohi a kasar nan, yaya kake ganin yiwuwar karin jihohin a matsayinka na mai neman a kara jihohi a Najeriya a wannan lokaci?
Habibu Gwarzo: Wannan tambaya tana da muhimmanci kwarai da gaske, kuma ina yaba wa wakilan taron kasa da suka zartar da cewa a kara kirkiro jihohi a kasar nan kuma dama muna cikin wannan gwagwarmaya ne suka same mu. Sai dai a yi hattara kan maganar gyaran kundin tsarin mulki kada a sanya son zuciya ko nuna fiffiko ga wani bangare. A bai wa al’ummar Najeriya dama su bayyana nasu ra’ayin kan wannan batu kada a yi abin da zai jawo rashin tabbas ga kasa. Ina so a fahimci cewa yadda ake kallon Arewa ko kadan ba haka take ba, domin yankin na da matukar muhimmanci ga kasancewar Nkjeriya a dunkule, sannan wajibi ne dukkan al’ummar Arewa su kara zage damtse wajen ganin martabar yankin tana nan daram. Kuma duk wani jigo na yankin ya sani cewa gudunmawarsa tana da muhimmanci wajen kare martaba da mutuncin yankin sabanin yadda aka ji Shugaban Taron kasa Mai shari’a Idris Kutugi yana cewa wai ’yan Arewa su ne tsiraru.
Aminiya: Wadanne matsaloli kuke fuskanta tun da kuka fara fafutikar neman Jihar Ghari?
Habibu Gwarzo: Babu shakka mun fuskanci matsaloli da kalubale iri-iri tunda muka fara gwagwarmaya har zuwa wannan lokaci da muke fatan samun nasara. Mun samu matsaloli da shugabanni da masu mulki wadanda suke ganin ko muna yi ne domin mu tozarta su ko mu rage musu iko. Amma mu manufofinmu su ne a kara kusantar da gwamnati ga jama’a, kamar yadda muke gani a jihohi irin su Jigawa wadda aka kirkiro shekara 23 kacal, yau ga ta ta zamo abar misali musamman a lokacin Gwamna Sule Lamido wato shekara bakwai da suka gabata.
Aminiya: Mene ne sakonka ga al’umma bisa wannan aiki da kuke yi?
Habibu Gwarzo: Ina so al’umma da mahukunta su fahimci cewa muna neman karin jihohi ne domin a kara samun ci gaba mai kyau a wannan kasa tamu Najeriya. Sannan ina fata wannan kokari da muke yi zai zamo hanyar ciyar da kasar nan gaba ta kowane fanni na rayuwar al’umma. Daga karshe, ina so al’ummar kasar nan su gane cewa Allah Shi ne ya yi ikonSa a kanmu na mu zauna a matsayin kasa daya kuma gwamnati daya, don haka a daina bata wani bangare saboda kawai ana ganin ba ya da amfani, kowa ya tsaya ya kare mutunci da martabar Najeriya a matsayin kasa daya.