Arewa ta hakura da mulki sai shekarar 2019 – Matasan Ijaw
Shugaban Majalisar Matasan Ijaw ta Duniya, Kwamared Udengs Eradiri ya bukaci ’yan Arewa su yi hakuri su goya wa Shugaba Jonathan baya ya sake zarcewa a kan mulki har zuwa shekara 2019 su ma za su mara wa dan Arewa baya. Shugaban ya kuma musanta zargin da ake masu cewa suna yi wa ’yan Arewa […]
Shugaban Majalisar Matasan Ijaw ta Duniya, Kwamared Udengs Eradiri ya bukaci ’yan Arewa su yi hakuri su goya wa Shugaba Jonathan baya ya sake zarcewa a kan mulki har zuwa shekara 2019 su ma za su mara wa dan Arewa baya.
Shugaban ya kuma musanta zargin da ake masu cewa suna yi wa ’yan Arewa barazanar tashin hankali idan shugaba Jonathan bai ci zabe ba.
Kwamared Eradiri ya bayyana haka ne a lokacin da ya je Kaduna domin ganawa da matasan Arewa inda suka sanya hannu a kan wata yarjejeniyar zaman lafiya a tsakaninsu a ranar Lahadi.
Eradiri ya bayyana rashin jin dadinsa kan yadda wasu matasa suka rika jifar tawagar Shugaba Jonathan a lokacin yakein neman zabensa a kwanakin baya. Ya ce yin haka bai dace ba kuma wannan ne ya sa wasu matasa daga yankinsu suka rika yin wasu kalamai marasa dadi ga ’yan Arewa.
“Hakika babu yadda za a yi Shugaba Jonathan ya zarce ba tare da goyon bayan ’yan Arewa ba, wannan ne ya sa muka zo nan domin hada kai da ku mu samu nasara idan ya kammala mulkinsa a shekarar 2019 sai mu goyawa dan Arewa baya. Mun san akwai shugabanin kirki masu hazaka a Arewa. Saboda haka idan kuka mara wa Shugaba Jonathan baya a shirye muke mu mara muku baya a shekarar 2019,” inji shi.
Kwamared Eradiri ya ce wannan sanya hannu da suka yi da takwarorinsu na Arewa alama ce da ke nuna cewa zaben da za a yi nan da ’yan kwanaki zai gudana cikin zaman lafiya da kwanciyar hankali.
A jawabin Shugaban Majalisar Matasan Arewa, Kwamared Isah Abubakar ya ce sun dakiu lokaci mai tsawo suna tattauna yadda za a yi su sanya hannu a yarjejeniyar zaman lafiya tsakaninsu da matasan Kudu. Ya ce a shirye suke su tabbatar da zaben da za a yi a cikin wannan wata an gudanar da shi cikin kwanciyar hankali da nasara.