Arewa ta hakura da shugabanci a 2015 – Bafarawa
Tsohon Gwamnan Jihar Sakkawato Alhaji Attahiru dalhatu Bafarawa ya yi gargadi game da masu neman a zakuda da mulkin kasar nan zuwa wani sashi a shekarar 2015 da sunan karba-karba.Bafarwa wanda ya gana da shugaban Jam’iyyar PDP na kasa Alhaji Ahmadu Adamu Mu’azu a Sakatariyar Jam’iyyar a Abuja ya ce kuskure ne a rika fafutikar […]

Tsohon Gwamnan Jihar Sakkawato Alhaji Attahiru dalhatu Bafarawa ya yi gargadi game da masu neman a zakuda da mulkin kasar nan zuwa wani sashi a shekarar 2015 da sunan karba-karba.
Bafarwa wanda ya gana da shugaban Jam’iyyar PDP na kasa Alhaji Ahmadu Adamu Mu’azu a Sakatariyar Jam’iyyar a Abuja ya ce kuskure ne a rika fafutikar neman mulki bisa dogaro da batun shiyya domin Najeriya ta kowa da kowa ce.
Ya ce gwagwarmayar neman mulki ya dawo Arewa a shekarar 2015 ba za ta samu nasara ba, kuma wajibi ne a ba kowa ’yancin zaben wanda yake so. “Najeriya ta kowa da kowa ce, lokacin da ka yi maganar Arewa ko Kudu a siyasa kana kashe dimokuradiyya ce, abu mai muhimmanci shi ne a samu dimokuradyya a cikin gida, domin haka batun shi ne a ba kowa ’yancin zabi,” inji shi.
Tsohon Gwamnan ya ce ya fice daga Jam’iyyar APC ne saboda ta gaza yin rajistar mambobinta bayan watanni da kafuwarta. Bafarawa wanda ya koma PDP a makon jiya ya ce galibin masu cewa su wakilan APC ne ba su da katin rajista. “Ban shiga PDP saboda ita ce jam’iyya mai mulki ba, ko domin saboda ina neman mukami. Na shige ta ne saboda in taimaka wa kasata. Kuma hanya mafi sauki ta gina PDP ita ce a tsaya kan manufofinta da tsarin mulkinta. Idan muka bi manufofi da tsarin mulkin jam’iyyar za mu magance matsalolin jam’iyyar.”
Ya ce su da suke cikin APC sun yi imanin za ta iya kawo canjin da ake bukata, amma a wata shida da suka gabata jam’iyyar ta gaza ba da kati ga kowa, amma tana ta nada shugabanni tare da kiran ’ya’yan PDP su hade da su.Ya ba shugaban PDP na kasa tabbacin mutane da dama a Sakkwato za su shigo PDP kuma su lashe zabe mai zuwa.
Ya ce ba wata matsala da za ta hana shi aiki da Mataimakin Gwamnan Jihar Alhaji Mukhtar Shagari inda ya ce ’ya’yan PDP a jihar ciki har da mataimakin gwamnan sun kai masa ziyarar girmamawa.