Arewa ta shirya taron magance matsalolin fina-finan Hausa

A kwanakin baya ne kungiyar shirya fina-finan Hausa da aka fi sani da Arewa Film Makers ta shirya taron magance matsalolin da suka yi cacukwi da masana’antar fina-finan Hausa. An shirya taron ne a dakin taro na  marigayi Janar Murtala Mohammed da ke Birnin Kano.Taron na yini guda ya samu halartar jarumai da furodusoshi da […]

Arewa ta shirya taron magance matsalolin fina-finan Hausa

wasu daga cikin mahalarta taron mataA kwanakin baya ne kungiyar shirya fina-finan Hausa da aka fi sani da Arewa Film Makers ta shirya taron magance matsalolin da suka yi cacukwi da masana’antar fina-finan Hausa.
An shirya taron ne a dakin taro na  marigayi Janar Murtala Mohammed da ke Birnin Kano.
Taron na yini guda ya samu halartar jarumai da furodusoshi da daraktoci da masu tsara labarin fim da masu daukar hoto da sauran masu ruwa da tsaki a harkar fim; tsofaffi da kuma sababbi da kuma ‘yan kasuwa da masu dillancin fina-finai daga jihohin Kano da Kaduna da kuma Katsina.
A yayin taron ‘yan fim sun amince ba za su ci gaba da rayuwa irin ta tumasanci ba. Na farko idan har mutum ya yarda zai yi fim dole ne ya mallaki kamfani da ofis, kuma kamfani ya samu rajista kamar yadda dokar kasa ta tanada, zai kuma samu akalla sakatariya a matsayin ma’aikaciya. Zai kuma mallaki duk sauran abubuwan da ya kamata kamfanin shirya fim ya mallaka. Ba wai kawai ka ga mutum a kan hanya ba daga shi sai ‘yar wayar hannu sai ya ce wai yana da kamfani, kuma kamfanin ko takardar tsire babu.
A bangaren ’yan wasa an yi  iyaka daga yanzu babu wanda zai sake rayuwa a masana’antar shirin fim a matsayin jarumi ne ko jaruma ba tare da bin wasu ka’idoji ba. Sau da dama wasu jaruman musamman ma mata sukan yi karya inda suke hada baki da wasu maza a zuwan su iyayensu ne ko kuma masu rikonsu.
Matakan da aka dauka yayin taron sun hada da: a yanzu an ruguza duk wani jarumi. Za a sabunta rijista. Jarumi zai sayi sabon fom  na neman shiga kungiya, a fom din akwai ka’idoji da suka kunshi wurin sa hannun jarumi da sa hannun mahaifi ko shakikinsa, sai rantsuwar kotu (affidabit). Daga nan sai kungiya ta kira jarumi ko jaruma ganawa, a nan zan a tantance shi ko ita.
A bangaren kamfani kuma,  dole sai akwai ofis mai rijista ta kasa ta limited liability. Idan ya cika dukkan ka’idoji sai kungiya ta ba shi lasisin shirya fim. Ko an ba kamfani lasisi idan ya kauce ka’ida sai a kwace lasisin. A bisa korafin da ake samu daga mutanen gari kan mu’amalarsu ‘yan fim mata inda wadansu ke yin mummunan shiga to nan ma an taka birki, domin Arewa ta kafa kwamitin na mutane uku kuma har sun zauna da Hukumar Hisba, za kuma su zauna da Hukumar tace fina-finai ta jihar Kano da ta tarayya domin samun goyon baya.
Shugaban kungiyar Arewa Film Makers ta kasa, Alhaji Abdullahi Sani Abdullahi wanda aka fi sani da Baba karami ya ce suna aiki ba dare ba rana don ganin an magance matsalolin da suka dabaibaye masana’antar fina-finan Hausa.