Arewa ta tantance wadanda za a horas kan aikin fim
kungiyar ‘yan fim ta Arewa Film Makers ta kammala tantance ‘yan fim din da za su samu horo kan aikin fim a kasashen waje. Wannan ya biyo bayan shirin gwamnatin tarayya na tallafa wa masana’antar fina-finai a Najeriya ne inda har ta ware Naira billiyan 3 domin habaka sana’ar shirya fina-finan a karkashin shiri na […]
kungiyar ‘yan fim ta Arewa Film Makers ta kammala tantance ‘yan fim din da za su samu horo kan aikin fim a kasashen waje.
Wannan ya biyo bayan shirin gwamnatin tarayya na tallafa wa masana’antar fina-finai a Najeriya ne inda har ta ware Naira billiyan 3 domin habaka sana’ar shirya fina-finan a karkashin shiri na musamman mai suna Project Act Nollywood.
Wannan shirin ya kunshi manyan rukunai guda uku watau samar da horo da kwarewa da rubuta labari da shiryawa da kuma kasuwanci.
Wata majiya da ke kusa da Arewa ta ce wannan shirin da ke karkashin kulawar ma’aikatar kudi ta tarayya, kungiyar Arewa ce ke wakiltar ‘yan fim din Hausa kuma sun yi taruka da yawa da ministar kudi a Abuja kuma tuni shirye-shirye suka yi nisa don fara gaba ta farko na wannan shirin watau bayar da horo wanda za a fara cikin watan gobe.
“Arewa ta gama shirinta tsaf don tura ‘ya‘yanta wasu makarantu masu zaman kansu na shirin fina-finai a karkashin shirin inda za su samu horo. Za kuma ta tura wadansu a cikinsu zuwa kasashen waje don halartar gajerun kwasa-kwasai don karo ilimi wanda gwammnatin tarayya za ta dauki nauyi duk a karkashin shirin.” Inji majiyar.