Aro: Sterling ya tafi Arsenal, Chelsea ta ɗauko Sancho
Chelsea ta ɗauko aron Jadon Sancho daga Manchester United domin maye gurbin da Sterling ya bari.
Ƙungiyar Kwallon Ƙafa ta Arsenal ta ɗauki aron ɗan wasan gaban Chelsea, Raheem Sterling a rana ta ƙarshe ta rufe musayar kasuwar ’yan wasa.
Haka ita ma kuma Chelsea, ta ɗauko aron Jadon Sancho daga Manchester United domin maye gurbin da Sterling ya bari.
- Abubuwan da ya kamata ku sani game da cutar ƙyandar biri
- Bruno Labbadia ya yi watsi da aikin horas da Super Eagles
Tun da farko sabon kocin Chelsea, Enzo Maresca ya shaida wa ɗan wasan Ingilan cewa ba ya cikin ’yan wasan da zai yi amfani da su.
A yayin da yake rattaba hannu kan sabuwar yarjejeniyar, Sterling ya ce “abu ne da bai min daɗi ba, amma zuwana Arsenal ya faranta mini rai.”
Ya ƙara da cewa “ƙungiya ce da na jima ina fatan taka wa leda, ita ce ƙungiyar da ta dace da ni a yanzu, na yi farin ciki ƙwarai da gaske.”
Sterling ya taka leda manyan ƙungiyoyin gasar Premier da suka haɗa da Liverpool da Manchester City da Chelsea sai kuma Arsenal yanzu da ya koma.
Ɗauko aron Sancho da Chelsea ta yi daga Manchester United na zuwa ne a daidai lokacin ya riƙa samun saɓani da kocin ƙungiyar, Erik ten Hag lamarin da ya sa dangantaka ta yi tsami tsakani.
Daga cikin yarjejeniyar, Chelsea za ta sayi ɗan wasan na Ingila mai shekara 24 kan kuɗi tsakanin fam miliyan 20 zuwa 25 a kakar wasa mai zuwa.