Arsenal ta doke United a Old Trafford
Arsenal, wadda wasa daya ya rage mata za ta buga da Everton a ranar ta 19 ga watan Mayu.
Arsenal ta doke Manchester United da ci daya mai ban haushi a wasan mako na 37 a Firimiyar Ingila da suka kara ranar Lahadi a Old Trafford.
Gunners ta ci kwallon ne a minti na 20 da fara wasan ta hannun Leandro Trossard, kuma maki ukun da ya ba ta damar komawa ta ɗaya a kan teburin kakar bana.
Kai Havert ne ya bayar da kwallon da Trossard ya zura a ragar United, ya zama kan gaba mai hannu a zura 14 a raga, ya ci takwas ya bayar da shida.
Wanda ke kan gaba a wannan kwazon a bana shi ne Cole Palmer na Chelsea.
Wannan ce kakar farko da Havertz ya ci kwallo ya kuma bayar aka zura a raga da yawa a Premier League tun bayan 13 a 2022.
Da wannan sakamakon Arsenal ta koma ta daya a kan teburin Firimiyar Ingila da maki 86, yayin da Manchester City, wadda ta je ta ci Fulham ranar Asabar ta koma ta biyu da maki 85.
Ranar Laraba Manchester United za ta karbi bakuncin Newcastle United a kwantan wasan mako na 34.
Daga nan kungiyar Old Trafford za ta je gidan Brighton ranar Lahadi 19 ga watan Mayu, domin buga wasan karshe a kakar bana a Premier League.
Haka kuma ranar Talata 14 ga watan Mayu, Manchester City za ta je gidan Tottenham, domin buga kwantan mako na 34 a Premier League.
Daga nan Manchester City za ta karbi bakuncin West Ham a wasan karshe a kakar bana ranar 19 ga watan Mayu a Etihad.
Arsenal, wadda wasa daya ya rage mata za ta buga da Everton a Emirates a dai ranar ta 19 ga watan Mayu.