Arsenal ta karya lagon Everton a Goodison Park

Da wannan sakamakon Arsenal ta haɗa maki 13 tana mataki na huɗu.

Arsenal ta karya lagon Everton a Goodison Park

Arsenal ta karya lagon doke Everton har gida bayan ta lallasa kungiyar da ci daya mai ban haushi a Goodison Park.

Everton dai ta yi rashin nasara da ci 1-0 a hannun Arsenal a wasan mako na biyar a Firimiyar Ingila ranar Lahadi.

Sai da aka kai ruwa rana a wasan, inda har ka tafi hutun rabin lokaci babu kungiyar da jefawa abokiyar karawarta kwallo a raga.

Bayan da suka koma zagaye na biyu ne Leandro Trossard ya ci wa Gunners kwallo.

Gunners, wadda ta maye gurbin golan tawagar Ingila, Aaron Ramsdale a wasan da David Raya – ta yi rashin nasara a wasa huɗu baya daga biyar da ta ziyarci Everton.

Arsenal ta yi wasa 12 a waje kenan ba tare da an zura mata kwallo a raga ba a Firimiyar Ingila tun daga fara kakar bara.

Fulham da Manchester City su ne ke biye da Gunners a irin wannan bajintar da kowacce ke da bakwai-bakwai.

Da wannan sakamakon Arsenal ta haɗa maki 13 tana mataki na huɗu, iri ɗaya da wanda Tottenham ta biyu da kuma Liverpool ta uku.

Ranar 24 ga watan Satumba Arsenal za ta karɓi bakuncin Tottenham a karawar mako na shida a Premier League.

Kafin nan Gunners za ta buga Champions League ranar 20 ga watan Satumba, inda PSV Eindhoven za ta ziyarci Emirates.

Bama-baman Lakurawa ne suka kashe mutane a Sakkwato – Sojoji

Gobara ta ƙone shaguna da kayan miliyoyi a kasuwar Nasarawa

Abubuwan farin ciki da suka faru a 2024

Gyaran TCN ya janyo ɗaukewar wutar lantarki a Abuja