Arsenal ta kawo karshen ci-yau-ci-gobe da Manchester City ke yi mata

Guardiola ya ce dama haka wasa ya gada, yau nasara gareka gobe ga waninka.

Arsenal ta kawo karshen ci-yau-ci-gobe da Manchester City ke yi mata

Arsenal ta kawo karshen ci-yau-ci-gobe da Manchester City ke yi mata duk haduwa a Firimiyar Ingila tsawon shekaru takwas.

Arsenal dai ta yi nasara a kan Manchester City da ci 1-0 a wasan mako na takwas a gasar Firimiyar Ingila da suka kara a Emirates ranar Lahadi.

Karon farko ke nan da Arsenal ta doke Manchester City a gasar Firimiyar tun shekarar 2015.

Tun farko sun je hutu ba ci kuma karon farko da hakan ta faru tsakanin ƙungiyoyin tun bayan Afrilun 2012, kuma a lokacin Gunners ce ta ci wasan ta hannun Mikel Arteta a lokacin yana buga mata tamaula.

Daf da za su tashi wasan ne Arsenal ta ci kwallo ta hannun Gabriel Martinelli, saura minti huɗu lokaci ya cika.

Arsenal ta yi fafatawar ba tare da Bukayo Saka ba, karon farko da bai buga mata wasam Firimiyar ba, wanda ya yi karawa 87 a jere a babbar gasar tamaula ta Ingila.

Shi ne kan gaba a irin wannan yawan buga Firimiyar Ingila a jere a tarihin wasannin.

Da wannan sakamakon Arrsenal tana mataki na biyu a kan teburin Premier League da maki 20, iri ɗaya da na Tottenham, wadda take ta ɗaya.

Mai horas da kungiyar Manchester City, Pep Guardiola bayan tashi daga wasan, ya ce dama haka wasa ya gada, sun samu ta su damar amma basu jefa kwallo ba, yayin da Arsenal ta yi amfani da ta ta damar wajen samun nasara.

Aminiya ta ruwaito cewa, a wasan karshe da suka fafata a kofin Community Shield, Arsenal ce ta yi nasara kan City a bugun daga kai sai mai tsaron gida bayan tashi wasan daya da daya.

Arsenal ta kara samun kwarin gwiwa a kokarinta na ganin ta lashe gasar a wannan kaka, ganin yadda a kakar da ta gabata ita ce ta kare a mataki na biyu.

Ranar Asabar Tottenham ta ci Luton 1-0 a wasan mako na takwas a babbar gasar tamaula ta Ingila.

Kawo yanzu ba a doke Tottenham da Arsenal ba daga wasa takwas da aka fara a Firimiyar bana.

Hotunan zanga-zangar tsofaffin sojoji Abuja

Girgizar ƙasa ta kashe mutum 95 a ƙasar Tibet

Boko Haram ta mamaye sansanin sojoji ta sace makamai a Borno

Ɗan ta’adda ya sa wa Zamfarawa harajin N100m