Arsenal ta kusa kammala cinikin Khedira

Rahoton da jaridar Marca da ake wallafawa a Sifen ta fitar ya nuna kulob din Arsenal da ke Ingila ya amince ya ajiye wa kulob din Real Madrid da ke Sifen zunzurutun Fam miliyan 19.7 kwatankwacin Yuro miliuyan 25 don ganin ya dauke dan kwallo Sami Khedira kafin a fara kakar wasa ta bana a […]

Arsenal ta kusa kammala cinikin Khedira
Arsenal ta kusa kammala cinikin Khedira

Rahoton da jaridar Marca da ake wallafawa a Sifen ta fitar ya nuna kulob din Arsenal da ke Ingila ya amince ya ajiye wa kulob din Real Madrid da ke Sifen zunzurutun Fam miliyan 19.7 kwatankwacin Yuro miliuyan 25 don ganin ya dauke dan kwallo Sami Khedira kafin a fara kakar wasa ta bana a watan gobe.
Sai dai kulob din ya cigaba da tattaunawa da dan kwallon a kan yawan albashin da yake son kulob din ya rika biyansa kafin ya amince ya sanya musu hannu.
dan kimanin shekara 27, Khedira ya ce yana bukatar  kulob din Arsenal ya rika biyansa albashin Fam miliyan 5 da rabi kwatankwacin Yuro miliyan 7 ne a duk shekara.  Ko kuma Fam dubu 200 kwatankacin Naira miliyan 53 a duk mako.