Arsenal ta sayi matashin dan kwallo daga kulob din Ajad

A ranar Talatar da ta wuce ne kulob din Arsenal da ke Ingila ya sayi wani matashin dan kwallon gaba mai kimanin shekara 16 mai suna Donyell Malen daga kulob din Ajad na Holland. Tuni kulob din biyu suka cimma yarjejeniyar cinikin dan kwallon. Sai dai daya daga cikin jami’an da ke kula da matasan […]

Arsenal ta sayi matashin dan kwallo daga kulob din Ajad
Arsenal ta sayi matashin dan kwallo daga kulob din Ajad

A ranar Talatar da ta wuce ne kulob din Arsenal da ke Ingila ya sayi wani matashin dan kwallon gaba mai kimanin shekara 16 mai suna Donyell Malen daga kulob din Ajad na Holland. Tuni kulob din biyu suka cimma yarjejeniyar cinikin dan kwallon. Sai dai daya daga cikin jami’an da ke kula da matasan ’yan kwallon a kulob din na Ajad mai suna Win Jonk ya bayyana bacin ransa a kan yadda aka sayar da shi ga Arsenal.

dan kwallon yana buga wa kulob din matasa na Ajad da ke Holland ne, amma ya gwammace ya canza sheka zuwa kulob din Arsenal don a raine shi a can.
“A gaskiya za mu yi rashin Donyell Malen daga kulob din Ajad, don matashin dan kwallo ne mai hazaka”, a wata sanarwa da Wim Jonk ya fitar a yanar sadarwar kulob din.
Amma ga dukkan alamu dan kwallon ba zai fara yi wa kulob din kwallo a matakin manya ba sai nan gaba saboda karancin shekarunsa.

 

’Yan sanda sun kashe ’yan fashi 3 a Binuwai

Mahara sun sace bsarake, sun harbi matarsa a ƙauyen Ondo

Sarkin Musulmi ya umarci a fara neman jinjirin watan Muharram

An tsinci gawar wata mata babu kai a Abuja