Arsenal ta yi canjaras da Southampton

Wannan shi ne karon farko da Gunners ta yi canjaras a Firimiyar a kakar bana a karawa 11.

Arsenal ta yi canjaras da Southampton

Arsenal ta yi canjaras da Southampton a wasan mako na 13 na gasar Firimiyar Ingila da suka fafata a ranar Lahadi.

Kungiyoyin biyu sun tashi 1-1 a karon battar da suka yi a filin wasa na St Mary.

Arsenal wadda ke jan ragamar teburin Firimiyar ta fara cin kwallo ta hannun Granit Xhaka a minti na 11 da fara wasa.

Sai dai Southampton ta farke ta hannun Stuart Armstrong bayan da aka koma zagaye na biyu.

Wannan shi ne karon farko da Gunners ta buga 1-1 a Firimiyar a kakar bana a karawa 11, bayan da ta yi nasara a tara, Manchester United ta doke ta 3-2.

Ɗan Aljeriya ya shiga hannu kan safarar makamai a Zamfara

’Yan bindiga sun kashe ’yan banga sun sace mai unguwa a Kaduna

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50

Jami’an Sibil Difens sun kashe mayaƙan Boko Haram 50