Arsenal ta yi cefanen Trossard daga Brighton
Yanzu haka Arsenal ke jan ragamar teburin Firimiyar Ingila da maki 47.
Kungiyar Kwallon Kafar Arsenal ta cimma yarjejeniyar sayen dan wasan gaba na Brighton kuma tauraron Belgium, Leandro Trossard.
Gunners dai ta shiga wannan ciniki ne bayan rasa damar daukar Mykhailo Mudryk dan kasar Ukraine wanda tuni kungiyar Chelsea ta sha gabanta wajen daukarsa.
- Mun sha kama fitattun ’yan siyasa masu ta’ammali da miyagun kwayoyi —Marwa
- Wa’adin Tsofaffin Kudi: Mun zuba ido mu ga yadda CBN zai kare da mutanen karkara —Sarkin Musulmi
Rahotanni sun ce, Trossard ya samu matsala da mai horar da kungiyar Brighton Roberto de Zerbi, abin da ya sa shi neman sauya sheka domin ci gaba da murza leda.
Trossard ya raba gari da Brighton bayan shafe shekaru uku da rabi a kan farashin fam miliyan 26 kamar yadda Goal ta tabbatar.
A wannan kakar wasa, Trossard ya jefa wa Brighton kwallaye 7 da kuma taimaka wa wajen jefa wasu guda 3 daga wasanni 16 da ya buga.
Daga cikin kwallayen da ya ci har da guda 3 da ya zira a karawar da Brighton ta kara da Liverpool wanda aka tashi 3-3.
Yanzu haka Arsenal ce ke jan ragamar teburin Firimiyar Ingila da maki 47 daga wasanni 18, yayin da Manchester City mai kare kambu ke matsayi na 2 da maki 39, sai kuma Manchester United wadda ita ma ke da maki 39.