Arsenal ta yi galaba kan Manchester City a Community Shield

Arsenal ta samu karsashin shiga Firimiyar Ingila ta bana da za a soma a mako mai kamawa.

Arsenal ta yi galaba kan Manchester City a Community Shield

Arsenal ta samu nasarar doke Manchester City a wasan Community Shield da suka fafata a wannan Lahadin.

Hakan dai ya kara wa Arsenal karsashin shiga Firimiyar Ingila ta bana da za a soma a mako mai kamawa.

An tashi wasan 1-1 ba tare da buga karin zagaye biyu na karin lokaci ba, inda da aka je bugun fenariti kungiyar da Mikel Arteta ta yi nasara 4-1 a kan kungiyar da Pep Guardiola ke jagoranta.

Matashin dan wasan Manchester City Cole Palmer ne ya fara jefa kwallo a ragar Arsenal a minti na 70, kafin Leandro Trossard ya farke ta a minti na 101 bayan kara minti 8.

A haka wasan ya kai zuwa bugun Fenariti, inda Kevin de Bruyne da Rodri suka zubar wa City, sannan Fabio Vieira ya jefa wa Arsenal bugun karshe da ya tabbatar da nasararta.

Shi dai wannan wasa na Community Shield ana fafatawa ne tsakanin kungiyar da ta lashe Gasar Firimiyar Ingila da wadda ta lashe Kofin FA.

Idan kuma ya kasance kungiya daya ce ta yi wa wannan gasanni biyu rubdugu, a kan bai wa kungiyar da ta zo ta biyu a gasar Firimiyar Ingila ta fatata wasan da wadda ta zamo zakara.

A kakar da ta gabata dai, Manchester City ce ta lashe Gasar Firimiyar Ingila sannan kuma ta lashe Kofin FA, inda Arsenal ta zo ta biyu a Firimiyar.

Yanzu kungoyin biyu za su saurari fara gasar Firimiyar ta bana a mako mai zuwa, inda Man City za ta kara da Burnley ranar Juma’a, ita kuma Arsenal ta karbi bakuncin Nottingham Forest ranar Asabar.

Tinubu ya yi naɗin sabbin muƙamai huɗu

Majalisar Zartarwa ta amince da kusan Naira tiriliyan 50 Kasafin Kuɗin 2025

Tinubu ya jagoranci zaman Majalisar Zartarwa

HOTUNA: Ana shirye-shiryen jana’izar marigayi Lagbaja