Arsenal ta yi sukuwar salla a kan Man City da ci 5

Arsenal ta ƙara jefa Manchester City cikin tsaka mai wuya.

Arsenal ta yi sukuwar salla a kan Man City da ci 5

Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Arsenal ta yi sukuwar salla a kan Manchester City ta ci 5 da 1 a Gasar Firimiyar Ingila.

Ƙungiyoyin biyu sun ɓarje gumi da yammacin ranar Lahadi a filin wasa na Emirates, a mako na 24 na gasar.

Ɗan wasan tsakiyar Arsenal, Martin Ordeegard ne ya fara jefa ƙwallo a minti na biyu da fara wasa.

Bayan dawowa daga hutun rabin lokaci, Erling Haaland, ya warware ƙwallon da Arsenal ta jefa wa Manchester City, a minti na 55.

A minti ma 56 Thomas Partey ya ƙara jefa wa Arsenal ƙwallo ta biyu.

A minti ma 62 Lewis Skelly ya jefa ƙwallo ta uku, sai Kai Havertz ya jefa ƙwallo ta huɗu a minti na 76.

A minti na 93, ɗan wasan gaban Arsenal, Nwaneri ya ƙarƙare da ƙwallo ta biyar a raga.

Yanzu haka dai Liverpool ce ke jan ragamar teburin gasar da maki 56 daga wasanni 23, yayin da Arsenal ke biye mata da maki 50 daga wasanni 24.

Nottingham Forest tana mataki na uku, da maki 47 daga wasanni 24 s teburin gasar.

Ita kuwa Manchester City na mataki na huɗu a teburin gasar da maki 41 daga wasanni 24 da ta buga.

Manchester City na ci gaba da fuskantar matsaloli tun bayan da wasu manyan ’yan wasanta suka samu rauni, kuma a baya-bayan nan kyaftin ɗinta Kyle Walker ya bar ƙungiyar zuwa AC Milan da ke ƙasar Italiya.

Hajjin 2023: An dawo wa mahajjata 3,000 kuɗaɗensu a Kaduna

’Yan sanda sun ceto mutum 23 da aka sace a Kaduna

Arsenal ta yi sukuwar salla a kan Man City da ci 5

Fasinjoji 30 sun ƙone ƙurmus a hatsarin mota a Ondo