Arsenal za ta lashe kofi a bana – Santi Cazorla
dan kwallon tsakiya a kulob din Arsenal Santi Carzola ya ce da alama kulob din zai lashe kofi a kakar wasa ta bana.dan kwallon ya bayyana haka ne jim kadan bayan kulob din ya bayyana shi a matsayin dan kwallon da ya fi kwazo a kakar wasan da ta wuce (Player of the Year).Carzola ya […]
dan kwallon tsakiya a kulob din Arsenal Santi Carzola ya ce da alama kulob din zai lashe kofi a kakar wasa ta bana.
dan kwallon ya bayyana haka ne jim kadan bayan kulob din ya bayyana shi a matsayin dan kwallon da ya fi kwazo a kakar wasan da ta wuce (Player of the Year).
Carzola ya ce a gaskiya ya ji dadin wannan karramawa da kulob din ya yi masa kuma hakan zai kara masa kwarin gwiwar cigaba da nuna kwazo a kakar wasa ta bana.
“Zan yi duk mai yiwuwa na taimaki kulob din Arsenal lashe kofi a bana”, inji shi.
Rabon da kulob din Arsenal ya dauki wani kofi tun a shekarar 2005 bayan da ya lashe kofin kalubale na Ingila (FA).
Rahotannin da ke fitowa sun tabbatar kulob din ya ware zunzurutun Fam miliyan 70 don cefano zaratan ’yan kwallo kafin a fara kakar wasa ta bana.