Artabun sojoji da ’yan Boko Haram ya ci mutum 10 a Okene
Mutum 10 sun mutu a fafatawar da aka yi da sojoji da wasu mutane da ake zargin ’yan kungiyar Boko Haram ne a garin Okene da ke Jihar Kogi.Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya rawaito cewa sojojin sun yi asubanci tare da dirar mikiya ga wani masallaci da ke unguwar Inike a garin Okene […]
Mutum 10 sun mutu a fafatawar da aka yi da sojoji da wasu mutane da ake zargin ’yan kungiyar Boko Haram ne a garin Okene da ke Jihar Kogi.
Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya rawaito cewa sojojin sun yi asubanci tare da dirar mikiya ga wani masallaci da ke unguwar Inike a garin Okene domin kama mutanen da ake zargin, bayan da suka samu rahoton cewa ana boye bindigogi da sauran makamai a masallacin.
Amma a cewar sojojin suna zuwa masallacin sai aka bude musu wuta inda suka mayar da martani. Rahotanni sun ce wasu daga cikin sojojin sun samu raunika a yayin artabun, inda aka garzaya da su babban asibitin Lokoja domin yi musu jinya, yayin da wata majiyar ta shaida wa Aminiya cewa an kashe wani karamin hafsan soja a yayin fafatawar.
Kamfanin NAN ya ce sojojin sun kai harin ne baya da suka samu rahoton cewa ana boye bindigogi da sauran makamai a masallacin, sakamakon bayanan da aka samu daga wasu mutum biyu da suka kama a yayin wani artabun da suka yi a ofishin Hukumar SSS da ke garin Lakwaja a ranar 25 ga Satumban da ya gabata, wadanda suka ce a wannan masallaci suke boye makamansu.
Mutanen Unguwar Inike inda lamarin ya auku sun guje daga unguwar zuwa lokacin hada wannan rahoto, yayin da masu karfin hali suka ci gaba da kasancewa a kulle a cikin gidajensu saboda tsoro.
Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Kogi Mista William Aya, ya ki cewa komai a kan lamarin, inda ya ce abu ne da ya shafi sojoji.