Artabun sojoji da ’yan Shi’a a Zariya
Daga shafi na 2 Da Aminiya ta ziyarci gidan mahaifinsa da ke Malali, Kaduna domin jin ta bakin danginsa, ta tarar da ’yan uwansa na tattaunawa a kan lamarin.“Gaskiya ba za mu ce komai game da wannan zance ba, saboda kusan duk labarin da muke ji kan abin da ya faru da shi a jaridu […]
Daga shafi na 2
Da Aminiya ta ziyarci gidan mahaifinsa da ke Malali, Kaduna domin jin ta bakin danginsa, ta tarar da ’yan uwansa na tattaunawa a kan lamarin.
“Gaskiya ba za mu ce komai game da wannan zance ba, saboda kusan duk labarin da muke ji kan abin da ya faru da shi a jaridu muke ji. Ina ganin ma kun fi mu samun labarai a kan abin da ke faruwa a yanzu. Me za mu ce tunda har yanzu ba mu samu gawarsa ba. Sai dai nan gaba dila mu ce wani abu amma a yanzu babu abin da za mu ce,” inji wani dan uwansa da bai ambaci sunansa ba.
A ranar Talatar da ta wuce ma an yi arangama a tsakanin ’yan sanda da mabiya Shi’a a Tudun Nufawa, Kaduna inda ’yan Shi’a uku suka rasu sakamakon harbinsu da aka yi. Wannan rikici ya faru ne kwana daya bayan sojoji sun ba da sanarwar cewa Sheikh Zakkzaki da matarsa na tsare a hannunsu.
Rahotanni sun ce wasu mabiya Shi’ar sun samu raunuka sakamakon harbinsu da ’yan sandan kwantar da tarzoma suka yi kuma ’yan sanda biyu sun samu rauni.
Zakzaky da matarsa na hannunmu – Sojoji
Bayan da aka rida yada jita-jita cewa an kashe Malama Zeenatu matar Sheikh Zakzaky kuma ba a san inda Sheikh Zakzaky yake ba, Rudunar Sojojin Najeriya a wata ganawa da manema labarai a Kaduna ta ce Sheikh Zakkzaky da maidakinsa suna hannunta cikin kulawa mai kyau.
Kwamandan Ruduna ta daya da ke Kaduna, Manjo Janar Adeniyi Oyebade ya bayyana haka, inda ya musanta zargin da ’yan Shi’ar suka yi cewa wai an yi musu kisan dare-dangi a Zariya.
“Babu wanda ya je Zariya har ya ga yawan mutanen da suka hallaka. Duk shaci-fadi kawai ake yi cewa wai an kashe mutane da yawa. darfin da soji suka yi amfani da shi wajen murdushe tarzomar bai wuce da’ida ba. dwarai mutane sun mutu amma ba yadda ake yadawa ba,” inji shi.
Ya yi kira ga mabiya Shi’ar su kwantar da hankalinsu tare da bin doka domin kuwa shugabansu na nan cikin kulawa a tsare a hannun sojoji kuma nan ba da dadewa ba za a ba shi damar yin jawabi gare su.
“Yana nan a wajenmu tare da mai dakinsa. Na yi magana da su kuma nan ba da dadewa ba zai yi jawabi ga mabiyansa, saboda haka su kwantar da hankalinsu tare da bin doka domin ba mu da wani mugun nufi a kansa a matsayinsa na dan kasa,” inji Janar din.
’Yan Shi’a sun nemi Sarkin Kano ya shiga tsakani
Mabiya Shi’a a Jihar Kano sun nemi Sarkin Kano Malam Muhamamdu Sanusi II ya shiga tsakaninsu da sojoji game da halin da ake ciki bayan fito-na-fiton da aka samu tsakaninsu da sojoji a Zariya.
A jawabin shugaban tawagar Malam Aliyu Babba ya bayyana wa Sarki Sanusi cewa sun zo fadar ne don neman Sarkin Kano a matsayinsa na uban al’umma ya shiga tsakaninsu da sojoji game da irin matakin da suke dauka a kansu na dodarin hana su gudanar da harkokinsu.
A cewar Aliyu Babba su mutane ne masu son zaman lafiya, don haka suna da tabbacin ba ’ya’yan dungiyarsu ne suka tsokani sojojin ba, kamar yadda suke idirari ba. “Duk abin da ake fadi game da abin da ya faru ranar Asabar a Zariya cewa mutanenmu ne suka tsokani sojoji babu gaskiya a ciki. Mu mutane ne masu son zaman lafiya. Don haka muke rodon Sarki ya taimaka ya yi mana tsakani da sojojin da suke dodari hana mu gudanar da ayyukanmu,” inji shi.
Da yake mayar da martani Sarkin Muhamamdu Sanusi ya ce zai yi iya dodarinsa wajen ganin an sulhunta batun tare da kawo darshen rigimar.
Sarkin ya yi kira ga ’yan dungiyar su rida bin matakin sulhu a duk lokacin da wani abu makamncin haka ya taso maimakon daukar doka a hannu, kuma ya yi kira ga dungiyoyin addini su guji shiga duk wasu abubuwa da za su janyo musu fadawa cikin rigingimu.
‘A sako mana Sheikh Zakzaky’
Jagoran ’yan Shi’a a Katsina Malam Yakubu Yahaya, ya ce an dulla shirin auka wa magoya bayansu ne ta karkatar da tafiyar Babban Hafsan Sojojin Najeriya zuwa hanyar da suke muzahara da gangan, bayan sun san akwai hanyar da za su iya amfani da ita.
Malamin ya shaida wa taron manema labarai haka a gidansa a Katsina a ranar Talata, inda ya zargi gwamnati da shirya madardashiyar hallaka jama’arsu, kuma ya kira Shugaban dasa Buhari da Saddam Huseini. Ya ce, dama wannan na daga cikin irin kwangilar da wadanda suka aza shi bisa mulkin dasar ke son aiwatarwa. “Gwamnati ita ce Boko Haram ba wani ba, domin da haka suka dirdiro ta domin amfani da su don biyan wata budata tasu, daga baya kuma suka zo suna kashe su,” inji Malamin.
Malam Yakubu ya tabbatar da cewa, jagoransu Malam Ibrahim Zakzaky na hannun sojoji kuma ya samu raunuka, inda yayi kira a sako jagoransu domin yi masa magani don ba su yarda da wanda ake yi masa ba.
Shugaban dasa Muhammadu Buhari dai ya aika da tawagar manyan jami’an gwamnati da na tsaro zuwa Kaduna da Zariya domin ganin halin da ake ciki, tare da gabatar masa da rahoto kan abin da ya auku.
Sai dai mabiya Shi’a sun yi watsi da kwamitin da Sufeto Janar ya kafa don bincikar lamarin, inda suka ce wanda aka ba shugabancin kwamitin daramin jami’i ne da ba zai iya dora laifi a kan na sama da shi ba.
dungiyar Dattawa Arewa da Majalisar doli ta Addinin Musulunci da dungiyoyi da dama da dasashen waje da suka hada da Iran da Amurka da Ingila sun budaci a gudanar da bincike domin gano wadanda ke da laifi a kashe ’yan Shi’ar sakamakon rikicinsu da sojoji.
Sojoji sun gano ’yan Shi’a 220 a ginin dardashin dasa a Husainiyya
A shekaranjiya Laraba sojoji sun gano mutum 220 a ginin dardashin dasa da ke Husainiyya inda Sheikh Ibrahim Zakzaky ke gabatar da lacca.
Akasarin wadanda aka gano dananan yara ne da mata, wadanda suka shafe tsawon kwana hudu ba ci ba sha kuma yawancinsu sun galabaita. Tuni sojojin suka mida su ga ’yan sanda .
Kakakin ’yan Shi’a, Ibrahim Musa ya tabbatar da faruwar haka kuma ya ce ’yan sandan sun mida musu wadannan mutum 220. Aminiya ta yi dodari jin ta bakin Shugaban Kwamitin Binciken da Shugaban ’Yan sandan Najeriya ya kafa AC Shehu Usman amma ya di magana a kai.