Arteta ya yi watsi da neman afuwar da Firimiyar Ingila ta yi wa Arsenal
Hakuri ba zai dawo mana da maki biyun da aka haramta mana ba.
Kociyan Arsenal, Mikel Arteta ya yi watsi da neman afuwar da Firimiyar Ingila ta yi dangane da kuskuren alkalanci da aka yi wa kungiyarsa.
Arteta ya ce bayar da hakuri bai wadatar ba, abin da kadai zai sanya su gamsuwa shi ne dawo wa Arsenal da makinta biyu bayan takaddamar da ta biyo wasansu da Brentford a Firimiyar Ingila.
- Buhari ya gana da Tinubu a Aso Rock
- Mutumin da aka yi kuskuren daurewa shekara 28 ya shaki iskar ’yanci
Hukumar da ke kula da alkalan wasan Firimiya ce ta aike da sakon neman yafiya ga Arsenal sakamakon abin da ta kira kuskure wanda ya kai ga bayar da kwallon da Ivan Toney ya zura duk da cewa tun a lokacin Arsenal ta yi tirjiyar cewa an ci kwallon ce bayan satar gida.
Sai dai Lee Mason da ke kula da na’urar taimaka wa alkalin wasa ta VAR bai bayar da damar bibiya don tantance sahihancin kwallon da aka bayyana da ta satar fage ba.
Hukumar ta PGMOL ta bayyana lamarin da kuskuren dan Adam wanda a kan iya yafewa, sai dai Arteta ya ce abin da ya farun ba kuskure ba ne kawai rashin sanin aiki ne.
A cewar Arteta, sam Arsenal ba ta karbi bayar da hakurin ba, yana mai cewa kuskuren ya haddasa wa Arsenal asarar maki 2 wanda ba dawo da su za a yi ba.