Aruna Irani: Waiwayen rayuwar tauraruwar Indiya

Kamar yadda bincike ya tabbatar, tauraruwar fina-finan Indiya, Aruna Irani, tana zaune ne a gida mai lamba 603, B. Gazdar Apts, daura da otel din Juhu, a birnin Mumbai na kasar indiya. Ita kanwa ce ga daraktan fina-finai, Indra Kumar, tana auren Kuku Kohli, wanda shi ma daraktan fina-finai ne.  Ta fara yin fice ne […]

Aruna Irani: Waiwayen rayuwar tauraruwar Indiya
Aruna Irani: Waiwayen rayuwar tauraruwar Indiya

Kamar yadda bincike ya tabbatar, tauraruwar fina-finan Indiya, Aruna Irani, tana zaune ne a gida mai lamba 603, B. Gazdar Apts, daura da otel din Juhu, a birnin Mumbai na kasar indiya. Ita kanwa ce ga daraktan fina-finai, Indra Kumar, tana auren Kuku Kohli, wanda shi ma daraktan fina-finai ne. 

Ta fara yin fice ne a fina-finai da wani mashahurin fim mai suna Gunga Jumna, amma kafin shi, ta fito a wasu kananan matsayi a fina-finai kamar Jahanara, Farz da kuma Aaya Sawan Jhoomke. Haka kuma, ta rika fitowa cikin fina-finai tare da dan barkwanci Mehmood, a cikin fina-finai kamar Aulad, Humjoli da kuma fim din Naya Zamana. Inda ta kara cirar tuta, shi ne inda ta taka kyakkyawar rawa a fim din da ya shahara sosai kuma ya kayatar, watau Caraban. Tun daga lokacin ta fito cikin fina-finai sama da guda 300.
Babu shakka ta samu yabo sosai a harkar fina-finai, domin kuwa shaida ta tabbatar da haka, inda ta samu kyautar fitattar kawar jaruma da fim din Pet Pyaar Aur Paap a shekarar 1984, aka kuma sake ba ta irin wannan kyauta da fim din Beta, a shekarar 1992. Mafi yawan fina-finan da ta rika fitowa, ta rika taka rawa ne a matsayin bahaguwa, wacce mafi yawan lokaci take zama ’yar rawa.
Wasu daga cikin fina-finan da ta fito a cikinsu, sun hada da: Hain Sanam, Ladmi, Yeh Dil Aashikanaa, Censor, Beti No. 1, Bulandi Aarzoo, Anari No.1, Haseena Maan Jaayegi, Hote Hote Pyar Hogaya, Phool Aur Aag, Rajaji, Silsila Hai Pyar Ka, Zulmi, Barood, Iski Topi Uske Sarr, Kudra, Maharaja, Dil To Pagal Hai, Do Ankhen Barah Haath, Ghulam-E-Musthafa, Hamesha, Itihaas, Saat Rang Ke Sapne, Saaz, Aurat, Chhote Sarkar, Ek Tha Raja, Indian Jaan, Rajkumar Rakshak, Ahankar, Kalyug Ke Abtaar, Kartabya, Prem, Raghubeer, Anokha Premyudh Bhagyawan, Brahma, Gopi Kishan, Insaniyat Laadla, Raja Babu, Suhaag, Aansoo Bane Angaray, Chor Aur Chaand, Dhanwaan, Kayda Kanoon, Mukabla, Professor Ki Padosan da kuma fim din Wakt Hamara Hai. Haka kuma, ta fito cikin dogon fim din da aka rika nunawa a cikin talabijin mai suna Maayka. Irin abin da ta yi a fim din, ya yi kama da abin da ta yi a cikin fim din Beta.