Asali, dalili da sakamakon kashe-kashen ta’addanci a kasarmu

A wannan makon, mun zakulo wannan muhimmin tsokaci ne daga ma’adanar hazikin malami, mai sharhi kan al’amuran yau da kullum, DOKTA ALIYU U. TILDE. Malamin ya haska mana asali da dalili da kuma abin da kashe-kashen ta’addanci ke haifarwa ga al’ummarmu, sannan kuma ya ba mu shawarwari managarta, yadda za mu yi wa kawunanmu kiyamul […]

Asali, dalili da sakamakon kashe-kashen ta’addanci a kasarmu
Asali, dalili da sakamakon kashe-kashen ta’addanci a kasarmu

A wannan makon, mun zakulo wannan muhimmin tsokaci ne daga ma’adanar hazikin malami, mai sharhi kan al’amuran yau da kullum, DOKTA ALIYU U. TILDE. Malamin ya haska mana asali da dalili da kuma abin da kashe-kashen ta’addanci ke haifarwa ga al’ummarmu, sannan kuma ya ba mu shawarwari managarta, yadda za mu yi wa kawunanmu kiyamul laili, ta yadda za mu taka wa wannan mummunar ta’ada burki. A karanta a tsanake, domin a amfana:

Ina mika ta’aziyyata ga iyalan dukkan wadanda suka rasa rayukansu tun lokacin da saka bama-bamai da hare-hare suka dawo Arewacin Najeriya. Nan kusa a Jos, kwanaki can wannan ta’addanci ya riski ’yan uwa da yawa a wajen ibada da wajen cin abinci, haka ma a kwananan nan, an rasa rayuka a Yola da Kano. Allah Ya jikan wadanda suka riga mu gidan gaskiya.
Lokaci ya yi da al’ummar Musulmi ya kamata mu fada wa kanmu gaskiya. A dogon nazarina kan lamarin, gaskiya guda ce wacce ba za a kauce mata ba. Asalin wannan abun guda ne. In ba shi aka jefar ba kuma aka tashi haikan wajen hana yaduwarsa, babu ranar karewar kashe-kashe da sunan addini.
Ba wani abu ba ne banda akidar kafirta Musulmi da take hakkin abokan zama wadanda ba Musulmi ba da sunan raya addini. Duk wanda Shedan ya jarrabe shi da wannan, ko ma mece ce akidarsa, ya san cewa tsakaninsa da ta’addanci kadan ne.
Gaskiyar magana ke nan. Da zarar ka kafirta mutum, to fa tsakaninka da kashe shi dama ce kawai da ba ka samu ba. Daman nan tana samuwa kashe shi ba komai ba ne, balle wawushe dukiyarsa da bautar da iyalinsa. Ka kafirta mutum ka ce ba ka taimaka wajen kashe shi ba, kamar ka ka bulbula masa fetur ne wani ya kyasta ashana, kana in ya kone ka ce ba ka ciki? Kana ciki.
Wannan ya faru a baya da sunan tajdidi. In wasu sun aikata shi a wannan zamani ba abin mamaki ba ne. Tsattsauran ra’ayi bai tsaya a kungiya guda ba. Hasali ma ana samunsa a cikin kowace irin akida hatta a cikin addinai da akidojin da ba na Musulunci ba. Ah, misali, in ka dauki wanda ya ce zai taka wuyan Annabi (wal iyazubillah) ai abin da ya fi bam ma sai ya sa wa mutane.
Kwanaki nake tattaunawa da iyalina irin musibar da Musulmi suka samu kansu a ciki lokacin da muka ga askar a cikin masallacin Annabi suna gadin masallata sahu-sahu. Haka yake a Makka da manyan masallatai da yawa a duniya. Na ce mata wannan bala’i ya kai iyaka. Askar din nan don wa suke gadin nan? Don gudun bama-baman Amurka ko Rasha? A’a, don gudun sharrin Musulmi ’yan uwansu da za su zo, in an bar su, har gaban kabarin Annabi (SAW) su ta da bam. Subhanallah! Subhanallah!
Masu ja da wannan nasiha tawa sai su yi ta yi don rayuwarsu, da shahararsu, da mukaminsu a cikin al’umma ko na malamansu sun ta’allaka ne da yaduwar wadannan akidu, har suna alfahari da yaduwar tasu. Yaduwar abu kuwa ba hujja ba ce ta dacewarsa da halin yau ko ingancinsa. Idan da haka ne, to da Shedan ya fi kowa daidai, tunda ya fi kowa mabiya. Amma gaskiya daya ce. A juri zuwa rafi…
karshe abun zai koma takarar mulki tsakanin masu wadannan ayyuka da kansu. Yau ga ISIS suna kashe Taliban duk da gwagwarmayar da Taliban ta ke yi ita ma ba don komai ba sai don Taliban ba ta yi mubaya’a ba ga shugaban ISIS, Al-Baghdadi.
karshe, addu’armu ita ce Allah Ka shagaltar da mu da laifukanmu da kokarin gyara su har sai mun gagara kai wa matsayin da za mu rika ganin wasu masu Kalma ba Musulmi ba ne su. Haka nan kuma ka hana mu cin zalin abokan zamanmu don kawai addininmu ba daya ne da su ba. Ka kare mu daga dukkan bala’i da bata wacce shedan zai nuna mana cewa shiriya ce.
To mene ne abin yi yanzu? Ba abin yi fiye da kyamatar wadannan zafafan akidu da kuma guje masu. Da zarar wani ya ce maka su wane kafirai ne ko ya nemi zuga ka ka ci hakkin abokin zamanka wanda ba addininku daya ba, to ka yi maza ka cika wa rigarka iska, ka bar wurinsa, komai hujjarsa. Ingancin hujja shi ne makomar da za ta haifar ga ’yan Adam. In a karshe za ta kai ga cin mutuncin wasu, ko kashe su ko lalata dukiyarsu, to ka sani ba akida mai kyau ba ce; abar kyama ce. Ka kuma yi matukar kokarinka ka kare duk wanda za ka iya karewa daga wannan musibar, kama daga iyalinka da danginka da wadanda za su ji maganarka. Wannan kuma ita ce babbar gudunmawa da za ka ba kasarka wajen wanzuwar zaman lafiya. Inda hali, ka fara daga nan.
Kamar yadda na yi tsammani, ma’abota wadannan akidu za su yi kokarin halatta kafirta mutane da hujjojin da muka saba ji. To, ba maganar ke nan ba; domin daga kafirta shi sai kuma me zai biyo baya? Sai kashe shi in an samu hali, ba batun gardama ba ne. Kuma shi muke gani yanzu yana faruwa. Idan ba haka ba, me ya kai ’yan Boko Haram kashe Musulmi? Duk yadda mutum ya juya fa ba zai kauce wa wannan gaskiyar ba. In ko ya yarda sai kashe shi to ya daina ganin laifin Boko Haram da ISIS. Domin kuwa bambancinsu makami ne kawai da amfani da shi.
Allah Ka jikan wadanda suka mutu, Ka gaggauta sauki ga masu rauni, Ka ci gaba da kare duk dan Najeriya da mahlukanka gaba daya. Amin Ya Rabbal alamin!
***