Asalin rubutun boko da bunkasar harshen Hausa (2)

Bunkasar rubutun boko Amma dai idan muka dawo maganar asalin soma rubuta Hausa da boko irin wanda har yau muke amfani da shi, to zaifi kyau mu koma kan maganar mu ta sama cewa Turawan mulkin mallaka ne suka assasa tare da tabbatar mana da ita. Farfesa Mahdi Adamu ya tabbatar mana da hakan a […]

Asalin rubutun boko da bunkasar harshen Hausa (2)

Bunkasar rubutun boko Amma dai idan muka dawo maganar asalin soma rubuta Hausa da boko irin wanda har yau muke amfani da shi, to zaifi kyau mu koma kan maganar mu ta sama cewa Turawan mulkin mallaka ne suka assasa tare da tabbatar mana da ita. Farfesa Mahdi Adamu ya tabbatar mana da hakan a shafi na 55 na littafinsa mai suna ‘The Hausa factor In West African History’. Kuma ga kadan daga abin da ya ce: Karatu da rubutu ta hanyar boko ya samu ga Hausawa ne a farkon karni na 20. Saboda a shekarar 1900AD ne gwamnatin Ingila ta karbe ragamar mulki daga hannun sarakunan Hausawa, amma sai a 1903 sojojin Gwamna Lugga suka cinye Kano da Sakkwato a yaki, sannan suka bude makaranta ta farko a Sakkwato tare da malamai biyu, watau Mr. Kurdan da mataimakinsa Malam Ibrahim, amma makarantar ba ta dade ba saboda iyaye sun ki sanya ‘ya’yansu don gudun kada a cusa musu akidar Kiristanci.

Farfesa ya nuna cawa rashin gamsuwar Hausawa ga ilimin da Turawa suke shirin ba su dadadden abu ne, kuma tun a wancan zamanin kalmar ‘Boko’ ta samo asali, wadda a cewarsa ma’anarta da Hausa shi ne kamar a ce ‘rufe kura da fatar akuya’ (Watau a yi basaja wajen rufe wani abu da wani abu).

Tun kafin wannan ma, shi kansa Lugga sai da ya kalli Hausawa da yadda suka yi riko da addini tun a lokacin, sannan ya yi amannar cewa bai yiwuwa a ce za a koyar da su boko kamar yadda ake koyar da shi a kasarsu Ingila.

A wani zancen kuma, cewa aka yi tun sa’ar da Lugga yake yaki a kasar nan ya fara sanyawa ana rubuta Hausa ta hanyar amfani da rubutun Romawa (boko). Saboda kamar yadda muka fada tun a baya, Lugga ya fahimci tasiri da bunkasar yaren Hausa a wannan yanki na Arewa, amma kuma a wurinsa bai yiwuwa ya rubuta Hausa da ajami kamar yadda ya samu Hausawan lokacin suna yi. Dalilan yin hakan suna da yawa, daga ciki akwai fadin cewa idan zaa rubuta Hausa da ajami, sai an koyi yare biyu maimakon daya, watau sai an koyi Hausa, sannan kuma an koyi Larabci. Amma watakila babban dalilin ya fi ga kiyayyarsu ga Larabawa ko kuma a ce kiyayyarsu ga Musulunci (kamar yadda babban dalilin kin jinin boko daga Hausawa shi ne kiyayyarsu ga Kiristanci, tun da watakila da a ce Musulmi ne suka kawo ilimin zamani kasar Hausa da ba a yi artabu da iyaye wajen su sanya ‘ya’yansu ba).

 Akwai wani abu ma da ba sai an boye ba. Lugga ya fada cewa ba ya ganin rashin sanya Musulmi a cikin sojojinsa a matsayin siyasa, amma a zahiri siyasar ne.  Tun da dai kusan daukacin sojojin nasa ba Musulmi ba ne, mutane ne gwarawa da sauran kabilu marasa addini wadanda suke adawa da Musulunci, wadanda kuma yawa-yawansu suna da matsala da Musulmi tun a lokacin jihadi, don haka suna zucci-zuccin karya daulolin da Musulmi suka kafa domin daukar fansa. A daya bangaren kuma, akwai kwatankwacin wannan kiyayyar a zukatan Hausawa, kuma tana daga manyan dalilan da ya sa Hausawa suka kyamaci ilimin boko. Tun da ilimin ya zo ne daga wadanda suke gani a matsayin makiyansu. Shi ya sa sai da aka sha artabu aka soma sanya yara a makarantun zamani a wancan lokacin, kodayake har zuwa yanzu (kusan shekara 114 ke nan) wasu daga cikinmu Hhausawa na kallon ilimin boko a matsayin haramtaccen abu kuma gurbatacce.

Ai a zahirin yakin da Turawa suka yi a zamanin mulkin mallaka da ’yan kasa aka yi, domin mafi yawan dakarunsu ’yan kasa ne bakaken fata, tun da Turawa ba yawa gare su ba a rundunonin, hasali ma wannan yanki namu kamar makabarta ya zame wa Turawa saboda yawaitar cututtuka da ke musu lahani a yankin.

Shi kuwa rubutun Ajami, Turawa da wadanda ba Musulmi ba na daukarsa a matsayin rubutu ne na Larabci kuma na Musulunci, dama kuwa da tun da dadewa Turawa da Larabawa ba wata dasawa suke ta a zo a gani ba, musamman ma saboda bambancin addini. Idan kuma ba haka ba, to za mu iya cewa baya daga cikin manufar Turawa a zuwansu wannan yanki su inganta addinin Islama, tun da a nasu ganin rubutun ajami na Musulunci ne. Dalili ke nan da ba za su yadda su yi aiki da rubutun Ajami ba ballantana har su inganta shi. 

 Don haka aka ce babbar sadarwar da sojojin Lugga suka fi fahimta daga gare shi ita ce rashin kaunarsa ga Musulunci. A zahiri, ban jin an taba ruwaito wata kalma ta batanci da Lugga ya yi wa Islama, amma a badini, ayyukansa na son ganin ya habaka addininsa ne tare da cika umarnin kasarsa. Shi ya sa kuma sojojinsa suka fi kaunar kome za a rubuta musu, a rubuta musu shi da harshen Hausa, yaren da suka fi sha’awar yarawa sama da nasu, amma kuma cikin haruffan sabuwar wayewa da Turawa kuma Kiristocin mulkin mallaka suka kawo, watau Romanci.

Za mu ci gaba