Asalin rubutun boko da bunkasar harshen Hausa (3)
Bayan an ci Kano da Sakkwato da yaki, sai Gwamna Lugga ya sa aka yi masa hasashen daliban da ke makarantun allo a wannan yanki, inda kintace ya nuna cewa akwai misalin makarantun Allo da ake karantar da addinin Musulunci cikin rubutun Larabci (Arabiyya) da ajami kusan dubu 25, sannan daliban da ke cikin makarantun […]
Bayan an ci Kano da Sakkwato da yaki, sai Gwamna Lugga ya sa aka yi masa hasashen daliban da ke makarantun allo a wannan yanki, inda kintace ya nuna cewa akwai misalin makarantun Allo da ake karantar da addinin Musulunci cikin rubutun Larabci (Arabiyya) da ajami kusan dubu 25, sannan daliban da ke cikin makarantun sun KUSA dubu 250. Wannan ta sa Lugga fahimtar cewa akwai aiki ja a gabansa, amma dai an ce da taimakonsa aka kafa makarantar mishan a Bidda a cikin shekara ta 1904, inda aka fara koya wa wasu mutane, ciki har da tsirarun Musulmi rubutun Hausar boko, gami da harshen Ingilishi. An ce ana koyar da daliban ne cikin harsunanmu na gida, watau Hausa da Nufanci.
Gwamna Lugga ya sanar da Ingila yunkurin da ya fara na juya rubutun ajami zuwa haruffan Rumawa (Boko), kamar yadda aka samu a kundin takardun da ya shafi Turawa zuwa Ingila (Annual Report, Northern Nigeria no. 476, 1903, 332-3).
Nasarar Rubutun Boko Kan Ajami:
Daga lokacin da aka fara samun gagarumar nasara a fannin rubutun boko a kasar Hausa kuwa shi ne, wajajen shekara ta 1908, lokacin da Lugga ya tura Dokta Hans bischer, wanda aka fi sani da danhausa zuwa kasashen Sudan, Misira (Egypt) da Gwalkwas (Ghana) domin yin nazari a kan yadda kasashen ke bayar da ilimi ga mutanensu, wadanda akasari Musulmi ne saboda kasancewar Hausawa Musulmi sun ki tura ’ya’yansu a harkar boko. Bayan danhausa ya dawo gida ne aka ce ya bude makarantar Elemantare da ake kira Makarantar danhausa a Nasarawa-Kano, wadda aka ce da dalibai 30 ta soma, wadanda suka zo daga mabambantan yankuna da kuma kabila.
Amma dai daga wannan lokacin ne aka samu cewar an fara fassara littattafai na ilimi, wadanda aka rubuta su a wasu yarukan duniya zuwa Hausa, aka yi rubutun nasu kuma da rubutun boko, a sannan ne kuma gwamnati ta mayar da Hausa a yankin Arewa a matsayin yaren sadarwa (abin da kusan ya jaza wa kowacce kabila da ke yankin fara koyon harshen Hausa ke nan), sannan kuma a hankali har hukumar fassara ta Jihar Arewa da aka fi sani da ‘NORLA’ ta zo, wadda ita ma ta ba da gagarumar gudunmuwa wajen fassara manyan littattafan ilimi masu amfani zuwa Hausa.
Daga littattafan farko da aka soma fassarawa zuwa Hausa da rubutun boko a wancan lokaci akwai misalin ‘Koyon Lissafi’ da ‘Dare Dubu Da daya’ da ‘Tarihin Garuruwan Borno’ da sauransu da dama.
Daga wannan nake ganin ta haka rubutun Hausar boko ya ci galaba a kan rubutun ajami da gagarumar nasara, domin rubuce-rubucen da aka yi na ilimi kusan sun zarta wadanda aka rubuta da Hausar ajami zuryan. Don haka sai bukatuwar ilimi ga jama’a ta tursasa su koyon haruffan boko don ganewa sama da koyon haruffan Hausar ajami. A yanzu mun kai munzalin da dalibi zai kammala digirin digirgir ba tare da ya karanta wani littafi a ajami ba.
Bunkasar Harshen Hausa:
A bisa fahimta irin tamu, yaren Hausa gamayya ce ta haifar da shi. Littafin Baibul mai tsarki ya fadi cewa shekaru da dama da suka gabata, mutanen duniya da harshe daya kurum suke amfani, sai daga baya yaruka suka rika samuwa ta yadda zuwa yanzu akwai kimanin yaruka dubu bakwai a fadin duniyar nan. Ina tsammanin Littafin Alkur’ani mai girma bai yi magana irin wannan ba, amma duk da haka maganar da ta fito daga Baibul na iya tabbata a kimiyance, tun da dai mun san cewa Allah Ubangiji ne ya saukar da littattafan duka guda biyu.
Samuwar harshen Hausa na iya zamowa daga hadakar kalmomi na wadansu yaruka mabambanta. Ma’ana, tana iya kasancewa karo-karon kalmomi daga yaruka daban-daban ne ya hadu ya samar da yaren Hausa kacokan dinsa. Hakan kuwa na iya faruwa ne idan muka kalli Hausawan su kansu, za mu ga cewa kabilu ne da dama suka cakudu suka rikide tare da zamowa Hausawa, lokaci mai tsawo da ya shude.
Misali, bari mu dauki manyan garuruwan Hausa mu dan yi karamin nazari a kansu. A tarihin kafuwar Kano, an ce wani mai suna Dala ne ya fara zama a kan wani dutse wanda daga bisani aka sanya masa suna Dala. A hasashe, hakan ta faru tun a wajajen karni na bakwai. Littafin tarihin Kano da ake kira ‘Kano Chronicle’ (Tarih baladil Laziy Musamma Kano) ya ruwaito kwatankwacin haka, har kuma ya rubuta a shafin farko “La na’alamu kabilatihi.” Ma’ana, ba mu san kabilar shi wannan Dala din ba, wanda hakan ke nuna cewar sam-sam Dala ba Bahaushe ba ne. Hakan kuma na nuna cewa asalin kalmar Dala ita ma ba ta Hausa ba ce.
Daga lokacin Dala da lokacin rayuwar zuriyarsa, kalmomi mabambanta sun shigo cikin harshen Hausa. Kamar misalin Girgije (sunan kakan Barbushe, kalmar kuma da Hausawa ke nufin hadari), Magaji daga Magajin Dala, da makamantansu.
Daga bisani aka ce Bagauda ya zo Madatai ta Kano ya kama noma. A bisa mafi rinjayen magana, Bagauda Bamaguje ne. Shi ma watakila sunan kabilarsa Maguzawa, ko kuma sunan kabilar tasa ya zama yana da wani lakabi na zahiri na daban, amma an sakaya shi ne da sunan Maguzanci, kalmar da a Hausa ke nufin mutanen da ba su da addini. Daga wajensu kalmomi irinsu noma, guguwa, hadari, shekara da shekarau suka fito. Wadannan jinsi na Maguzawa kuma su ne suka kafa kusan kafatanin tsoffin biranen da ke kasar Kano a yau. Misali kamar Rano da Gaya da Gwarzo da kiru da wasunsu, kodayake, duk da muna da karancin fahimta a kan jinsin Maguzawa, amma da alama suna iya zamowa kabilu mararraba tamkar yadda jinsin Fulani suke a yau.
Sannan dai, a littafin ‘Kano Ta Dabo,’ marubucinsa marigayi Alhaji Abubakar Dokaji, ya fadi cewa a tsohuwar Kano akwai kabilun Gazargawa da ke zaune a Jakara, Zadawa da ke tsakanin Jakara zuwa Sontolo, kangon da ke tsakanin Sontolo da Burkum, Zaura da ke tsakanin Bompai da Wasai, Dundunzuru da ke tsakanin Watari zuwa dandutsen karya, Shiriya dake tsakanin Sontolo zuwa Shinke, Sheme dake tsakanin Damargu zuwa Kazaure, Tokarawa dake tsakanin karmami zuwa Ringim da wasunsu. Dukkan mafi rinjayen wadannan kabilu sun hade guri daya lokaci mai tsawo da ya gabata, har ta kai ga harshen Hausa kurum ake yi a Kano kuma a duk duniya idan ka ce Kano, za a ce maka birnin Hausawa ne.
Mu kalli Katsina, su ma an ce Durbawa ne suka kafa garin tun a karni na 13. Wamban Katsina Alhaji Abba Kali ya taba fada a wata hirarsa da gidan Rediyon Faransa cewa wadanda suka kafa garin Katsina sun zo ne daga wani gari mai suna Mani. Garin Mani yana nan har yanzu a Jihar Katsina to amma ana tsammanin mutanen garin Mani na farko ba Hausawa ba ne, wata kabila ce wadda ta taso daga yankin Mali.
Haka abin yake a Zariya. Littafin ‘History of Zaria (1350-1902)’ na Yakub Hassan ya nuna cewa asalin Birnin Zazzau mutane ne daga Kufena, Kuchichchiri, Turunku, Madarkachi, Kargi da Tukur-Tukur suka yi hadaka wajen kafa birnin. Domin kuwa, dukkan wadancan garuruwa tsoffin wurare ne da binciken fannin nazarin al’amura masu dadadden tarihi ya tabbatar da wanzuwar mutane da dadewa kafin kafuwar Zazzau a karni na 13 kuma akasari wadancan mutanen kabilu ne mabambanta misalin Kadarawa da wasunsu, har dai daga bisani aka samu cewa kabilar Torankawa suka zo suka kwace ikon wurin.
A yanzu kuma garin ya rikide zuwa kasar Hausa, masarautarsu da al’adunsu duk na Hausa ne. Su ma dai watakila jikokin wadancan kabilun ne kusan za mu iya cewa suka ajiye yarukansu da al’adunsu tare da zamowa Hausawa zalla.
Za mu kammala