Asamaoh Gyang yi wa wata budurwa ciki a Ghana1
A ranar Talata da ta wuce ne aka samu labarin Kyaftin din Black Stars da ke Ghana Asamaoh Gyang ya dade yana lalata da wata yarinya mai suna Sarah Kwabla al’amarin da ya sa ake zargin ta dauki cikinsa ba tare da sun yi aure ba. Budurwar ce ta fito karara ta shaida wa duniya […]

A ranar Talata da ta wuce ne aka samu labarin Kyaftin din Black Stars da ke Ghana Asamaoh Gyang ya dade yana lalata da wata yarinya mai suna Sarah Kwabla al’amarin da ya sa ake zargin ta dauki cikinsa ba tare da sun yi aure ba.
Budurwar ce ta fito karara ta shaida wa duniya halin da take ciki bayan wani gidan rediyon FM da ke kasar ya yi hira da ita. Sannan ta yi barazanar sakin hoton bidiyon da ta rika dauka a lokacin da suke lalata a lokuta da dama ba tare da sanin dan kwallon ba, muddin ya ki amincewa da cikin da take dauke da shi.
Budurwar ta ce, tana da shaidar da ta nuna yadda dan kwallon ya sha ziyartarta a gidanta da ke Ghana kuma ya rika yin lalata da ita. Ta ce a duk lokacin da suke lalatar, dan kwallon ba shi da masaniyar tana nadar lalatar da suke yi a na’urar bidiyo don haka ne take neman fasa kwai muddin ya ki amincewa da daukar nauyin cikin.
A nasa bangaren, Asamaoh Gyang ya karyata batun da take masa na cewa shi ya yi mata cikin, sai dai bai musanta ziyarar da yake kai mata a lokuta da dama ba. Hasalima ya ce idan ya ziyarce ta sukan yi tadi ne irin na masoya kafin ya koma gidansa.
Ita ma Lauyar budurwa Sarah mai suna Maurice Ampaw ta ce tana da shaidar da ta nuna Asamaoh Gyang tare da manajansa sun sha kai wa budurwa Sarah ziyara a gidanta da ke Ghana a lokuta da dama, inda dan kwallon ya rika lalata da ita kuma daga nan ta dauki cikinsa, amma abin mamaki bayan ta sanar da shi tana dauke da cikinsa sai ya nemi ya noke da hakan ce ta sa suke tunanin shigar da maganar gaban kotu don a bi musu kadi. Ta ce suna da kwakkwarar shdiar da ta nuna dan kwallon ya yi lalata da Sarah a lokuta daban-daban.
Yanzu dai al’amarin ya bazu a Ghana inda wasu ke Allah-wadai yayin da wasu kuma suke shakkun batun budurwar inda suke ganin tana neman shafa masa kashin kaji ne don ta ga yana da kudi.