Asarar da muka yi a ambaliyar Borno —’Yan kasuwa
“Duk shagunan da ke Monday Market da Post Office ruwa ya shanye su,” in ji wani dan kasuwa
’Yan Kasuwar Monday Market da sauransu a Maiduguri sun tafka mummunar asara sakamakon ambaliya bayan fashewar Madatsar Ruwa ta Alau mai nisan kilomita 10 daga garin.
Ranar Litinin da tsakar dare ambaliyar ta yunkuro, inda ta raba dubban mazauna unguwannin Post Office, Gwange, Moromoro, Gadar Customs, Gidan Zoo, Bulabullin, Maidoki Roundabout, Jami’ar Maiduguri, Cocin Saint Patrick da sauaransu da muhallansu.
Wani dan kasuwa ya ce, “Duk shagunan da ke Monday Market da Post Office ruwa ya shanye su.”
- Gaskiyar batun garkuwa da Sheikh Bello Yabo
- Ambaliya ta raba dubban mutane da gidajensu a Maiduguri
- NAJERIYA A YAU: Dabarun Magance Matsalolin Najeriya
Wakilinmu a garin Maidurugi ya zagaya garin, inda ya iske ’yan kasuwar Monday Market suna lissafin irin asarar da suka yi sakamkon ibtila’in.
Wasu daga cikinsu sun nuna matukar kaduwarsu da kuma tunanin yiyuwar maye gurbin abin da suka rasa a ambaliyar.
Wani mai sayar da sukari da fulawa a kasuwar, Muhammad Bulama, ya ce ambaliyar ta shanye kasuwar gaba daya.
“Duk shagunanmu da ke kallon gidan Marigayi Alhaji Mai Sugar sun yi ambaliya, sukari da fulawa da shinkafa da kayan girki na miliyoyin Naira sun lalace.
“A sa mu a add’ua! Buhunan kayan abinci irin su sukari da shinkafa da gishiri da taliya da sauransu duk sun jike sun narke,” in ji shi.
Wakilinmu ya lura yawan ruwan da ke ambaliyar yana kara kaurwa inda yake kara shiga wasu unugwanni.
Hakazalika ambaliya ta mamaye Gidan Zoo na Kyarimi ta wuce da namun dajin da ke ciki, inda a halin da ake ciki namun dajin suke neman mafaka.
Wani mazaunin yankin ya ce, “yanzu haka mun fice daga unugwar saboda gudun hari daga namun daji da kwarin da ke gidan zoo.
Rundunar ’yan sanda a Jihar Borno ta bukaci jama’a da su kaurace wa yankunan da aka samu ambabaliya zuwa wasu wurare masu aminci.