Ashe ana soyayya a kurkuku?

Rayuwa dai babu yadda ba ta kasancewa kuma babu inda ba a tafiyar da harkokin rayuwa. Kowa dai ya san rayuwar kurkuku, rayuwa ce ta kunci da wahala da zullumi. Amma duk da haka ashe ana gudanar da soyayya da zumunci a cikinta. Za mu iya fahimtar haka, idan muka nazarci wannan labarin na kasa, […]

Ashe ana soyayya a kurkuku?
Ashe ana soyayya a kurkuku?

Rayuwa dai babu yadda ba ta kasancewa kuma babu inda ba a tafiyar da harkokin rayuwa. Kowa dai ya san rayuwar kurkuku, rayuwa ce ta kunci da wahala da zullumi. Amma duk da haka ashe ana gudanar da soyayya da zumunci a cikinta. Za mu iya fahimtar haka, idan muka nazarci wannan labarin na kasa, wanda wani ya aiko mana amma babu suna:

Wata budurwa ce aka yi wa sharri, aka dora mata laifin kisan kai, aka je kotu kuma alkali ya yanke mata hukuncin daurin rai-da-rai a kurkuku.
Da aka kai ta kurkuku, bayan ta shiga ba ta da wani aiki sai kuka. Ana nan sai wani mutum da yake aiki a kurkuku, wanda aikinsa kawai shi ne, idan mutum ya rasu ya zo ya yi dawainiyar sanya mamacin a akwati, a rufe shi, sannan a je a binne gawar.
Kullum sai ya ganta tana kuka har wata rana ya je ya tambaye ta abin da ya sa take kuka. Ta kwashe labarinta kaf ta gaya masa. Ta ce kuma abin da ya sa take kuka koyaushe shi ne, don tana budurwa ne, amma ga shi za ta kare rayuwarta a gidan yari.
Tausayinta ya kama shi, kodayaushe idan ya shigo sai ya zo wajenta sun gaisa. Yana dai dan debe mata kewa, har soyayya ta shiga tsakaninsu sosai har suna cewa ba wanda ya isa ya raba su. Sai dai kuma ta yaya za su yi auren?
Wata rana suna hira sai ta ce: “Ya kamata mu san yadda za mu yi na kubuta, mu je mu yi aure.” Sai ya ce mata: “To ya za a yi?”
 Sai ta ba da shawarar cewa: “Idan an yi mutuwa a gidan nan, zan je in shiga cikin akwatin da gawar take. Idan ka zo da yaranka sai ka rufe kawai. Idan aka binne, sai ka je daga baya ka tone ni, mu gudu.”
Ya amsa, ya ce: “To haka za a yi, kawai idan an yi rasuwa ki je ki shiga.”
Bayan kwana biyu da magariba aka yi rasuwa a gidan yarin, kawai sai ta tashi ta gano inda gawar take, ba tare da ta nemi inda yake ba, tun da dama da alkawarin. Kawai sai ta dauki wata ’yar karamar fitilar hannu ta tafi dakin da gawar take, ba tare da duba gawar mace ko namiji ba, kawai ta kwanta kusa da ita a cikin akwatin.
Yaransa na zuwa sai suka binne gawar, suka yi dawowarsu kurkukun.
Budurwar nan ta dan jira kadan ba ta ji ya zo ya tone ta ba, sai ta fara yi wa zuciyarta tambayar cewa: “A ce dai ya ki zuwa ya tone ni, tab!” Sai ta ce bari dai ta duba gawar nan, namiji ne ko mace? Sai ta zaro fitilar nan, ta yi ’yan dabaru ta haska fuskar gawar. Kwatsam, sai ta ga ashe saurayinta ne ya rasu ba wani mutum na daban ba.
Wanda ya aiko da labarin nan ya ce, shin in amafita ga wannan budurwa?
***

Abdul Abuja, 08133844064:
FDk, ban san laifin da na yi muku ba, saboda na sha rubuto wasika zuwa wannan fili amma ba a taba bugawa ba. In kudi ake bayarwa to a gaya mini nawa ne ake bayarwa kafin a buga?
***

Mudassir Ibrahim Ningi, 08169139393:
FDk, a gaskiya a matsayina na wanda ya san halin da ake fadawa in an yaudari masoyi, ga shawara ga masu bibiyar wannan shafin, musamman mata: Kun ga maza iyayenku ne, ya kamata ku daina yaudararsu, don gudun bacin ransu. Da fatan za ku gyara.
***
Malam Mudassir, ni ban taba jin ana ce wa maza iyayen mata ba, amma nakan ji ana cewa mata iyayen al’umma saboda su ne suke haihuwa, suke raino da koya tarbiyya da sauransu. Ko kuwa sabuwar ma’ana ka samo, oho! – FDk.
***

Daga Gado Marafan Sifawa, 08065717934:
Uhum! Malama kin buda baki amma kin kasa magana. FDk, barka da wannan lokaci amma Malama Sha’awa Mungadi, ai kowace riga, wuya kan saye da ita. In ana soyayayarku sai madadi amma da zarar kun debe amarci sai ku rika dogon haske, tilas namiji ya yi shi ma, ya canja. Mu kam har gobe tamkar yau aka kawo amarya. Har idan kin ga namiji ya yi maki jifar matattar mage, tabbas ba laifin gulob ba ne, laifin batur ne. Na yi imanin cewa duk matar da ta ci gaba da tarairayar mijinta da kalamai fiye da yadda take kullum, za ta samu nasarar mallakarsa kuma su zauna lafiya cikin soyayya.
***

’Yar uwarku kuma kanwarku, 07068607589
Wallahi a lokacin nan kamar ciwon zuciya ya same ni, da ta buga na fadi na mutu ga baki daya, na ji duniya ta yi mini zafi, ya sa ni na tsani maza, ya sa ni na tsani rayuwata, ya cuce ni, na shiga damuwa saboda ya yaudare ni. ’Yan uwana, ina son ku taya ni addu’a, Allah Ya bi mini hakkina a kansa kuma ku taya ni addu’a Allah Ya cire mini tunaninsa a raina. Kuma na fada masa ba zan taba yafe masa ba sannan kuma ga shi na fada wa duniya ba zan taba yafe masa ba kuma in sha Allahu sai an yi masa mafiyin abin da ya yi min. Yanzu haka maganar da nake muku har an kai kudin gaisuwar aurensa da kuma sadakinsa da wata.
***

Muhammad Yusuf Goje, 08149027674:
Zuwa ga filin Dausayin kauna, amincin Allah ya tabbata a gare ka, ya kai jagoran masoya FDk, tare da sauran ’yan uwa ma’abota dandalin soyayya. A gaskiya ina so in fara soyayya kuma ga shi ban san mene ne so ba, ballantana na san farillansa da sunnoninsa. Don haka nake neman shawarar yadda za a yi in san su kafin na fara.
***

Babbar magana, wai dan sanda ya ga gawar soja! Ai kuwa ilimin soyayya fadi gare shi, da wahala a tatike shi a shafukan jarida. Kawai ka tafi makaranta, ka shako ilimi. – FDk.  
***

Abubakar Hassan Abubakar Ningi:
Addu’a ga FDk, fatan alheri ga dukkannin ma’abota wannan shafi. FDk, ina yi maka addu’ar Allah Ya kara maka nisan kwana mai amfani, juriya, hakuri da kwazo; Allah Ya ci gaba da gyara mana kasarmu Najeriya.
***

Amin, amin Ya Allah. Malam Abubakar, muna godiya, Allah Ya saka da alheri. FDk