Ashe garkuwar ‘Iron Dome’ ta Isra’ila holoƙo ne?

A lokaci guda Iran ta nuna wa duniya cewar garkuwar sararin samaniyar Isara’ila da ake tsoro fanko ne

Ashe garkuwar ‘Iron Dome’ ta Isra’ila holoƙo ne?

Shugaban kasar Iran ya fitar da wata sanarwa bayan hare-haren da ƙasar ta kai kan Isra’ila da yammacin ranar Talata, inda ya bayyana hare-haren a matsayin “martanin da ya dace” ga irin “cin zarafi” na Isra’ila, sai dai ya jaddada cewa Iran ba ta son yaki.

Shugaba Masar Masoud Pezeshkian ya ce: “Wannan mataki ne domin kare muradu da ’yan kasar Iran,” kamar yadda ya wallafa a shafinsa na X.

Ya kara da cewa, “Ya kamata Netanyahu ya fahimci cewa, Iran fa ba ta so kuma ba ta takalar yaki, amma a shirye take tsaf domin cewa cas ga duk wata barazana…kada ka soma fada da Iran; zancen ke nan,” in ji shi.

Me ya sa Iran ta kai hareharen?

Cikin wata sanarwa, rundunar kare juyin juya halin Musulunci na Iran din ta bayyana cewa, an kai hareharen ne a matsayin mayar da martani ga kisan da Isra’ilar take yi wa al’umnar Gaza da Lebanon, da kuma kisan gillar da ta yi wa shugaban kungiyar Hizbullah Hassan Nasrallah da kwamandanta Abbas Nilforoushan a makon jiya a Beirut da kuma shugaban Hamas, Ismail Haniyeh a farkon shekarar nan a birnin Tehran.

Hare-hare sun sauka kan sansanonin Isra’ila – Jami’in Hizbullah

Wani babban jami’in kungiyar Hezbollah – mai gwagwarmaya da makamai – ya shaida wa kafar yada labaran Al Jazeera cewa hareharen da Iran ta kai na rokokin sun yi nasarar sauka inda aka nufa su kai sannan sun yi barna a sansanonin sojin Isra’ila da dama kamar yadda aka tsara.

Jami’in, wanda bai so a bayyana sunansa ba, ya kara da cewa matakan garkuwar makamai masu linzami da Isra’ilar ta girke sun yi “rauni”, yana mai jaddada cewa an samu hasarar rayukan sojojin Isra’ila.

Dama dai rundunar sojin Isra’ila ta yi kaurin suna wajen dakile bayanan barnar da ake yi wa kafofi da cibiyoyinta.

To sai dai rundunar sojin Isra’ila ta yi ikirarin kakkabo da “yawa daga makaman” masu linzami guda 180 da Iran ta harba, sai dai ta ce da akwai wasu “kebabbun” wuraren da hare-haren suka yi tasiri a tsakiya da kudancin Isra’ilar. Amma a nata bangaren, rundunar askarawan Jamhuriyar Musulunci ta Iran (IRGC) ta ce kashi 90 cikin 100 na makaman da aka harba sun cimma wuraren da aka tsara su sauka.

Shin garkuwar Isra’ila ta tashi aiki ne?

A cikin shekarun da suka gabata, Isra’ila ta kafa wasu mashahuran tsare-tsare na zamani wadanda za su iya sunsuno ko gano in wani makami ya kunno kai zuwa inda jama’a take ko inda aka adana kayan yaki.

Bari mu leka nau’o’in tsarin tsaron samaniyyar Isra’ila:

The Arrow (Kibiya)

Wata garkuwa ce da aka kera tare da taimakon Amurka, da aka samar da ita domin kakkabo makamai masu linzami masu cin dogon zango, ciki har da nau’in makaman roka da Iran ta harba a ranar Talata.

Garkuwar Arrow da ke aiki a wajen sararin samaniya, Isra’ila ta kuma yi amfani da ita wajen dakile makamai masu linzami masu cin dogon zango da ’yan tawayen Houthi suke harba mata daga Yaman.

David Sling (Majaujawar Dauda)

Har ila yau, ita ma wannan garkuwar tare da taimakon Amurka aka gina ta, an tsara ta ne da zimmar kakkabo makamai masu linzami masu cin matsakaicin zango irin na Hezbullah a Lebanon.

An girka shi tura a lokuta da dama a yayin wannan yakin.

Iron Dome (Tulluwar ƙarfe)

Ita ma dai wannan garkuwar tare da sa hannun Amurka aka samar da ita, ta yi kaurin suna wajen kakkabo rokoki masu cin gajeren zango.

Ta kakkabo dubban rokoki tun lokacin da aka girke ta shekara 10 da suka gabata.

A cewar Isra’ila, garkuwar Iron Dome takan iya samun nasara da kusan kashi 90 cikin 100 wajen kakkabo rokokin da aka harba.

Iron Beam (Ginshikin karfe)

Ita wannan garkuwar Isra’ilar ce da kanta ta sana’anta shi domin katse hanzarin duk wata barazanar da ta tunkaro Isra’ilar.

An yi amfani da fasahar Laser (wato haske mai ratsa shamaki) wajen gina ta.

Isra’ila ta ce wannan sabuwar fasaha ce abar a yi na’am da ita lura da arhar alkinta ta fiye da sauran matakan garkuwar da take amfani da su a halin yanzu.

A cewar rahotannin kafofin watsa labarai na Isra’ila, kudin alkinta kowace garkuwar Iron Dome guda ya kai kusan dala dubu 50, yayin da sauran matakan garkuwar suke iya cin sama da dala miliyan biyu wajen kakkabo makami mai linzami guda daya tak.

To amma ita garkuwar Iron Beam, ana kashe wasu ’yan daloli kalilan wajen kakkabo makami mai linzami guda, sai dai har yanzu ba a fara tsarin aiki da garkuwar ba tukuna.

Iran ta karya lagon Isra’ila

Shi ma a cewarsa, Aliyu Dahiru Aliyu, wanda dan jarida ne kuma mai sharhi kan al’amuran siyasar duniya, hare-haren da Iran ta kai wa Isra’ila sun zama tamkar barazana ce ga shekaru da aka yi ana nuna tamkar ba wanda zai iya nuna wa Isra’ilar yatsa wajen kai mata harehare ta sama saboda tsaron sararin samaniyarta da abin da matakan garkuwa irin su “Iron Dome”.

Ya ce Iran ta karya wannan siddabarun a ranar Talata, “… bayan harba rokokin da ita wannan fasaha ta kasa tare su kuma a cewar Iran kaso 80 cikin 100 na makaman sun dira a inda aka tsara su dira na sansanin sojoji da kuma filin jiragen yaki.

“Fasahar da Isra’ila take amfani da ita kala biyu ce. Akwai ta “Iron Dome” da take harbo kananan rokoki da kuma ta ‘DaYid Sling’ da aka tsara ta harbo manyan makamai.

“Sai dai a sabon harin na Iran duka biyun ba su nuna bajintar bayar da kariya ba.

“Bidiyoyi sun bayyana yadda rokokin Iran suka dira a gurare daban-daban inda suka yi mummunar barna.”

Ya kara da cewa babban sakon da hare-haren suke nunawa shi ne: “Iran a shirye take da yakin da zai iya ballewa,” in ji shi.

“A yanzu dai Firaministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu, ya bayyana cewa za su mayar da martani.

“Su kuma sojojin Iran sun ce a shirye suke su kai yakin wani mataki matukar aka taba su.

“Idan har yakin ya fadada to zai mamayi kasashe kamar su Iraki da suka dauki aniyar bai wa Iran kariya.

“Ballewar yaki a Gabas ta Tsakiya abu ne mai yiwuwa amma da ake dari-darinsa.

An dade da sanin cewa Iran ba ta son shiga yaki da kanta amma tunda a wannan karon aka ga ta shiga to tabbas a shirye take

“Kuma da yake Isra’ila ba ta saba ko kwarewa da yakin kasa da kasa ba, ta fi himma wajen afkawa kungiyoyi, tabbas ba za ta iya yaki da Iran ta yi nasarar da take zato ba.”

Sai dai a cewar Aliyun, shigar Amurka yakin zai tsawaita yakin ne kawai amma ba lallai ya bayar da nasarar da Isra’ila take tunani ba, “ganin cewa har yanzu Amurka ta kasa gamawa da yakin Yaman ma balle kuma Iran.”’

Mun fara binciken turmutsutsin tallafin abinci — Shugaban ’Yan Sanda

Tinubu ya soke ayyukansa saboda rasuwar mutane a Abuja da Anambra

NNPC ya rage farashin fetur zuwa N899

Mutum 10 sun mutu a wajen rabon tallafin abinci a Abuja