Ashe Turawa mutane ne? (11)
Haka kuwa aka yi, safiyar Lahadi da misalin karfe goma sha daya na safe, sai ga wayarta, na sauka kasa na tarar da ita, muka shiga mota sai cikin gari. Ni dai ban san inda muke shiga ba, amma da yake na yi wasan Monopoly tun ina makarantar sakandare, sai na ga kamar na koma […]
Haka kuwa aka yi, safiyar Lahadi da misalin karfe goma sha daya na safe, sai ga wayarta, na sauka kasa na tarar da ita, muka shiga mota sai cikin gari. Ni dai ban san inda muke shiga ba, amma da yake na yi wasan Monopoly tun ina makarantar sakandare, sai na ga kamar na koma gonar wasan ne. Duk wani titi da na dade da haddacewa na wasan Monopoly, sai in fahimci ashe da ma akwai shi a zahiri. Mu ne kan Titin Euston, muka ratsa titin Odford, shiga can, fita nan, ta titin Merylebone ne, zuwa yankin Westmister, har dai muka kare a unguwar Hampstead, domin na gaya wa Angelica cewa wurin farko da nake so in ziyarta shi ne kabarin Karl Mard, Shugaban ’Yan Gurguzun Duniya.
Mun iso makeken filin da kabarin yake, wuri ne mai yawan dausayi da ciyayi da itace, ga kananan koramu nan ko’ina. Mutane na ta sha’aninsu, yara da manya, tsofaffi da mata sai kai da kawo suke yi. Wadansu na wasan kwallo, wadansu na yawo da karnunkansu, wadansu na zaune suna shakatawa. Sai da muka biya fam shida, ni da ita, sa’annan aka bar mu muka shiga. Kaburbuka ne ga su nan bilahaddin, wasu sun dade da mutuwa, wasu kuma kwanan nan. Duk kuwa da an ce kada a matsa kusa da kabarin Karl Mard a dauki hoto, sai da muka fakaici idon masu tsaron wurin, na yi tsaye kyam kusa da shingimemen butuntumin Karl Mard, aka dauke ni hoto da shi, na kuma dauko shi ta fuskoki daban-daban, domin ajiyar tarihi.
A nan wurin ne na ga kaburburan yawancin ’yan gurguzu na duniya, wasu ma ba nan Landan suka mutu ba, amma aka dauko gawarwakinsu aka binne kusa da Karl Mard. Na ce a raina ka ga wadanda suka fi ni iya batun, su ba ziyara suka kawo masa ba, makwabtaka suke da shi har a matabbata.
Kila wani ya tambaye ni me kuma ya hada ni da Karl Mard, da har na kai masa ziyara? Wallahi ba dangin Inna bare na Baba, sai dai abin da zan ce bai wuce karambanin rayuwata ba. Ni dai ina da wata dabi’a, duk lokacin da na ziyarci wani wurin da ban taba zuwa ba, nakan yi kokarin ziyartar inda na san wadansu ba su damu da shi ba, domin a nawa tunanin, irin wannan wuri, nan kallon yake. Kila shi ya sa ban leka fadar Sarauniyar Ingila ba, ko Trafalgar Skuare, ko kuma maginar Big Ben, ko kuma gidan BBC ba sai daga baya. Haka na yi ko da na je Saudiyya aikin Hajji, duk da yana daga cikin tsarin aikin Hajji a ziyarci wasu wurare na musamman a Madina da Makka, musamman dutsen Uhud, inda aka kashe su Sayyidina Hamza da sauran shahidai suka yi shahada, ni bayan an kare ziyarar da addu’o’i, na mayar da hankali ne wajen gano inda maharban da Annabin Rahama (SAW) ya zaba domin kare Musulmi suka yi daga da kuma inda Khalid bin Walid ya bi ya ci dunun Musulmi a wajen yakin. Har yau ina tunawa da wannan wuri da na hango, kamar ina nan aka yi yakin na Uhud.
Wannan ke nan. Bayan mun kammala yawo a makabartar, sai muka isa gidan Angelica, nan ne na hadu da danta Marco, dan shekara 3 da haihuwa, yaro ne mai hazakar gaske, da gani na sai ya sha jinin jikinsa, ban yi mamaki ba, ya ki kula ni, sai ya kalle ni, ya sadda kai kasa, ya sake kallona, sai na ga ya kalli hular da ke bisa kaina, ya ce da Angelica, ina na samo helmet irin wannan. Muka fashe da dariya mu duka, domin shi a wurinsa kube ba ta da wani suna idan ba hular kwano ba, da yake sa wa in ya hau kekensa.
Duk da cewa bai saki jiki da ni ba, zuwa magariba bayan na sha ruwa, sai ga ni da shi mun baje a baranda, muna ta wasa da kayan wasansa, ta yadda ko da muka shiga mota za su mayar da ni gida, ya dage cewar yaushe zan dawo mu sake yin wasa, wai na fi mahaifiyarsa iya wasa da yara, muka yi dariya, na ce da shi da zarar na samu sukuni, zan zo.
Litinin na yi na kama hanyar jami’a, da ma na ce muku rabon da in shiga jami’ar tunda muka halarci walimar barka da zuwa da na leka a gurguje na dawo gida saboda sanyi. Ita ma walimar abin bayani ce ga wanda bai san tadojin Turawa ba.
Muna shiga cikin jami’ar aka ce za a yi mana marabar cin abincin rana ne, saboda haka ko da na fito daga ofishinmu ni da Moses wajen karfe 12 da rabi, sai muka tasar wa dakin shakatawar manyan malaman jami’a, can muka samu Angelica da wadansu manyan farfesoshi guda shida, biyu dai na san su, domin kuwa ina iya kiransu ’yan Arewacin Najeriya. Akwai Farfesa Murry Last, wanda nake wa lakabin ‘Barayar Sarkin Musulmi’ saboda aikin da ya yi wa Daular Usmaniyya da Arewacin Najeriya ta fuskar bincike, shi ne kuma shugaban kwamitin tace masu son zuwa Ingila ta hanyar Lebentis. Akwai kuma Farfesa Graham Furniss, wanda mun dade da sanin juna, saboda turbar binciken adabi ta hada mu a wurare da dama, in ban da Ingila da ban taba zuwa ba, shi kuwa Arewacin Najeriya tamkar gida ne a wurinsa. Sauran sai da aka yi mini bayani na gane ko su wane ne. Akwai Farfesa Kramer, shi ne shugaban cibiyar da ta kawo mu Ingila da Farfesa Richard Fardon, Darakatan SOAS, jami’ar da cibiyar take zaune da kuma Farfesa Marten, na Sashen Nazarin Harsunan Kudancin Afirka.
Nan dai aka sha abin sha, aka tattauna, aka yi mana maraba, aka watse. Muna komawa ofis sai Angelica ta ce yanzu kuma kowa tasa ta fisshe shi. Ta ce su sun gama da mu, idan akwai abin da muke bukata, muna iya nemanta ko ta waya ko ta Imel, wato Intanet, da yake a gida da ofis, kwana muke kan Intanet. Ta bayyana mana cewa muna da damar mu kai ziyarar bincike ko gabatar da kasida wurare uku, wajen birnin Landan, sa’annan duk inda muke son zuwa bincike ko karatu ko gabatar da kasida a cikin birnin Landan ba shamaki, mu je, ko mu bidi a tura mu, domin za a biya mu kudin mota da na makwanci.
Za mu ci gaba