Ashe Turawa mutane ne? (6)
Kila yanzu wasu na iya tambayar me ya kawa ni London? Amsar ba wuya gare ta ba. Haduwa ce a birnin Kano ta tayar da zuwan nawa Ingila. Taro ne na masana harkar adabin Hausa daga jami’i’oi daban-daban a birnin na Kanon. Nan ne na gabatar da wata kasida, wadda ta dan burge masu saurare. […]
Kila yanzu wasu na iya tambayar me ya kawa ni London? Amsar ba wuya gare ta ba. Haduwa ce a birnin Kano ta tayar da zuwan nawa Ingila. Taro ne na masana harkar adabin Hausa daga jami’i’oi daban-daban a birnin na Kanon. Nan ne na gabatar da wata kasida, wadda ta dan burge masu saurare. A cikin masanan akwai wani Farfesa daga Jami’ar London da ya zo wajen taron, ya ji dadin abin da na gabatar, mun tattauna da shi, ya nuna mani cewa akwai wasu ayyuka makamantan wannan da na tattauna a Ingila, da zan karanta su, zan kara samun haske kan wannan fage da nake bincike a kai. Nan take muka kulla zumunta, ya kuma ba ni adireshin da ya ce zan aika da batuna, za su iya daukar nauyina zuwa Ingila, sai dai ya nuna mani cewa gasa ce ake yi duk shekara, don haka ba garanti, mai rabo ke samu.
Ni dai na amshi adireshin amma ban ma tuna da batun ba sai can bayan an dade da watanni a cikin watan Afrilu na 2007, lokacin saura wata daya a rufe amsar batutuwan gasar. Kamar dai in fasa ganin kila na yi latti, haka nan na aika masu da batuna da kuma ko ni wanene da irin yadda nake so na amfana da wannan dama. Kafin a rufe wannan karbar batutuwan gasar ranar 1 ga watan Mayu 2007, na sami labarin cewa sun ga sakona, sai na koma na ci gaba da rayuwata. Duk abubuwan da ake yi ta Imel ne, wato Intanet, saboda haka ba wata matsala ta rashin sanin abin da ake ciki, sai dai in ba komfuta, ba kuma Intanet.
A ranar 6 ga watan Yuni 2007 na sami sako daga Sakatariyar Cibiyar da ke gudanar da gasar cewa ‘bayan an bi duk takardun da aka aiko domin shiga wannan gasa daga Nijeriya, an kuma tattauna duk batutuwan da kowa ya aiko, an kuma dubi ayyukan da kowa ya yi a rayuwa, kwamitin tacewa da daukar masu zuwa binciken wata uku na Lebentis da Jami’ar London, karkashin jagorancin Farfesa Murry Last, na farin cikin bayyana maka cewa ka samu gurbi daya daga cikin biyu da aka ware wannan shekarar, muna tsimayarka a watan Satumba na 2007. Suka kuma kara da cewa za mu aiko maka da tikiti da sauran bayanai nan gaba kadan. A cikin wasikar sun kara da cewa, zan zauna tare da su daga ranar 15 ga Satumba zuwa 15 ga Disamban 2007.’
Bari na yi abin gwari-gwari domin a gane dukkan irin wannan kai-kawo da nake ta yi. Shi wannan zama da take bayani, na bincike ne da karatu da ziyarce-ziyarce (ko kuma na karatu da yawon bude ido) da gabatar da kasidu da halartar tarurrukan kara wa juna sani da leka wuraren sayar da littattafai da ajiye su da dai makamantan wuraren karuwar ilmi. Kana iya cewa wannan balaguro wata ‘yan makaranta ce mai tarin muhimmanci, kuma dama ce da duk wani malami zai so ya samu domin zuba wa tukunyar ilminsa ruwa masu albarka.
Sauran batutuwa da ma can na yi muku bayani, saboda haka a wannan safiya da na wayi gari a London ba abin da na yi sai faman neman gano inda mazaunin jami’ar yake. Tun a masauki na tambayi budurwar da ke gaban teburin amsar baki ko ya zan gano inda School of Oriental and African Studies, Unibersity of London, take, nan take ta yi man kwatance, ta ce da na fita, in yi dama zuwa bakin titi, in dubi Yamma sai in mike in yi ta yi, ta ce har cikin jmi’ar ba zan bace hanya ba. Ina fita kuwa na doshi Yamma kamar yadda ta ce da ni, ina yin kamar tafiyar minti biyar sai ga ni a Russell Skuare, unguwar da Jami’ar take. Na dade da sanin unguwar ko dai ta wasiku ko kuma ta Intanet shekaru da suka wuce. A daidai wannan wuri ne dubban mutane suka sha da kyar a lokacin da aka sanya bama-bamai a tasoshin karkashin kasa a shekarar 2005, inda bom uku suka fashe da misalin karfe takwas na safe, tsakanin tashar Liberpool da Edgware da kuma tsakanin King Cross zuwa Russell Skuare. Daga baya kuma wani bom din ya fashe a bisa wata bas mai hawa biyu a tashar Tabistock, kusa da King Cross ita ma. ‘Yan kunar bakin wake ne su hudu aka ce suka saki wadannan bama-bamai a ranar 7 ga watan Yulin 2005, inda mutane 52 suka mutu, sama da 770 suka jikkata.
Saboda haka ko da na iso wurin, idanuna na kai da kawo ko zan sake ganin an yo waje da gudu, wai ko wani bom ya sake tashi saboda tun a gida ake yi man bayanin na fashewar bama-bamai a unguwar. Haka kuma duk wata doguwar bas da na gani mai hawa biyu sai na yi nesa da ita, ina tunanin ko akwai bam a ciki. Kafin dai na kai cikin jami’ar, wadda ba ta nesa da tashar Russell sai da na ga bas-bas irin waccan da bom ya fashe kai sun kai goma, kowa na ta kai da kawo cikin su, daga nan ne na fahimci cewa su ma ‘yan kasar sun fara mantawa da abin da ya faru, balle ni da zuwana ke nan! Wai abin da Hausawa ke cewa fin mai kora shafawa!
Ginin jami’ar London da na makarantar SOAS, kamar yadda aka fi kiran ta, ke ciki ba wani abin tokabo ba ne, amma kuma ya tsaru, idan mutum ya taba shiga Senate Building na Jami’ar Ahmadu bello Zaria, zai ga cewa tamkar haka wurin yake, sai dai kowa da komi na cikin ginin ne, cikin tsari da tsaro da kuma inganci.
Na yi kamar minti biyar ina kallon ginin kafin na shiga, domin kuwa gini ne na tarihi. An samar da shi tun a shekarar 1836, shekara daya da rasuwar Sultan Muhammadu Bello na Daular Usmaniyya a Nijeriya. Sai dai ita wannan makaranta ta SOAS daga baya ta samu, an kafa ta ne a shekarar 1916, shekara biyu da samuwar kasarmu Nijeria. An kudurta ne ta kasance cibiyar nazarin al’amurran da suka shafi nahiyar Asiya da Afirka da kuma Gabas ta Tsakiya, bisa wannan fage ne ta yi suna duk duniya!
Za Mu Ci Gaba