Ashe Turawa mutane ne? (7)
Ko da na shiga cikin ginin wannan katafariyar Jami’a, mai hawa biyar, na ga wurin cindum da mutane, dalibai kala-kala, da yake yawancinsu fararen fata ne, ko dai Turawa ko Larabawa ko Asiyawa ko kuma irina bakar fata sai ka ji kamar ka shiga wata sabuwar duniya ne, sai cakwai-cakwai kawai kake ji ko’ina, harsuna […]
Ko da na shiga cikin ginin wannan katafariyar Jami’a, mai hawa biyar, na ga wurin cindum da mutane, dalibai kala-kala, da yake yawancinsu fararen fata ne, ko dai Turawa ko Larabawa ko Asiyawa ko kuma irina bakar fata sai ka ji kamar ka shiga wata sabuwar duniya ne, sai cakwai-cakwai kawai kake ji ko’ina, harsuna na tashi kamar ana matsar kalangu!
Ina shiga sai na na matsa kusa da wadansu ’yan mata da ke karbar baki na yi musu bayanin ko ni wanene, da inda za ni. Nan take suka sa na yi wani dan littafi, aka ba ni wani dan kati na lika wa rigata, suka ce in haye hawa na hudu, ofis na 472, nan ne Cibiyar Nazarin Al’amurran Afirka, wato masu masaukina. Na haye na’urar yin sama da mutane, na sauko a inda aka ce, na bi layi ina dubar lambobi har na isa na 472. Ina sa kai cikin ofishin sai muka yi ido hudu da Angelica Baschiera, Sakatariyar Cibiyar. Tana gani na sai ta ce da ni ‘hala dai Dokta IbrahimMalumfashi ne!’ Ba wai tambaya ta yi ba, don ta tabbatar ko shi ne, na ce da ita ‘shi ne’. Ta ba ni wuri na zauna, muka shiga tadi, domin ni kadai take jira, ganin cewa abokin aikina Dokta Moses Mamman, daga Jami’ar Ahmadu Bello Zaria tuni shi ya dade da isowa London, domin shi ba kamar ni ba, bai samu matsalar bizar shiga Ingila ba.
Ba mu dade ba ta mike ta ce ai sai mu shiga fama. Da yake gogan ya san irin gonar da ya zo, bai bata lokaci ba, sai ya zauna da kyau gaban ta. Ta jawo wata wasika daga cikin teburin da take zaune, ta saba katuwar rigar sanyi da ke rataye a kusa da ita, ta ce mu tafi. Na dauka zama za mu yi, da na ga ta yi gaba, ni kuma sai na bi. Muka sauko hawa na kasa, muka shiga dakin karatun jami’ar, ta mika wa wata mace da ke kan komfuta takardar, ita kuma ta yi ’yan buge-bugenta a komfuta, ta mika wa wani takardar, shi kuma ya ce na zauna kusa da teburinsa ya yi nasa buge-bugen a komfuta, ya dauke ni hoto, nan take ya mika mini, adentiti kad, na duba na ga hotona da mukamina da watannin da zan yi, sai kurum na yi murmushi, na ce mu je zuwa, mahaukaci ya hau kura.
Muna fita daga nan sai Angelica ta ja ni ta kai ni cikin dakin karatun jami’ar, inda ofis dinmu da ni da Dokta Moses Mamman yake, na samu Dokta Moses, ya takarkare yana ta bugun komfutar Ta-Fi- Da- Gidanka da ya zo da ita, muka gaisa, na nemi wuri na ajiye tawa komfutar, da ta ga mun shiga yin Hausa, sai ta ce sai an jima, ta bar mu nan, ni kuma sai na ji wani dadi ya rufe ni, domin ko rabon da in yi Hausa tun da na bar Najeriya, sai yanzu!
Dokta Moses Mamman shi ne takwarana na wannan ziyarar bincike da ake bai wa Malaman Jami’o’in Najeriya da suka cancanta, suka kuma haye dukkan matakan da Jami’ar London da Lebentis Foundation suka gindaya. Shi dan kabilar Ikulu ne daga Jihar Kaduna, yana kuma koyarwa ne a Jami’ar Ahmadu Bello Zariya, a fannin nazarin ilmin Jogurafiyya.
Duk da cewa ba mu taba ganin juna ba, amma tamkar mun dade da sanin juna ne, domin tun muna Najeriya mun yi ta aika wa juna sakonni ta Imel da yin waya domin sada zumunta da sanin irin halin da kowa yake ciki na zuwa Ingila. Shi da yake matarsa na nan Ingila tana aiki, ya kuma sha zuwa Ingilar bai sami matsalar biza ta shiga Ingila ba. Hasalima ya shekara biyu yana ziyartarta a Ingila shi ya sa shi ya riga ni tasowa zuwa Ingila.
Ya baro Nijeriya tun ranar 15 ga watan Satumba, ni kuwa sai ranar 25 ga watan na Satumba na baro. Amma duk da haka tare za mu komo gida Najeriya, idan Allah Ya kai mu ranar 15 ga watan Disamba 2007.
Ba abin da muka shiga tattaunawa ni da shi, irin yadda rayuwa za ta kasance, me ake so mu yi a Ingila? Ina za mu je? Wanene zai duba aikin binciken da za mu yi? Yaushe za mu gabatar da makalu? Yaya abincin kasar yake? Sanyi fa yaushe zai tsananta? Tambayoyi dai ga su nan ina ta yi masa, yana ba ni amsa gwargwadon sanin sa.
Babban abin da ya jawo hankalina kai shi ne amsar kudin guzurin zama Ingila wanda shi tuni ya amsa, sa’annan sayen kayan sanyi, domin ya gan ni cikin fararen kaya na shadda, kamar yadda na saba a Najeriya, ya ce da ni, wadannan kayan ba za su kai ni ko’ina ba, ni ma na fahimci haka, domin kuwa ko da na fito daga masauki, ji na yi kamar an kwara mini ruwan kankara a jiki, na ji kamar na koma, amma ba yadda zan yi, dole na tafi, to in koma in ce da su me, ba ni na kawo kaina ba!
Na shiga zagaya dakin karatun da muke ciki domin in fahimci yanayinsa, domin kuwa nan ne zan yi wata uku ina faman karatu da bincike da nazari da kuma gabatar da makalu.
Tun da farko na dai fahimci cewa wannan wuri ba karamin wuri ne ba. Hawa biyar ne jibge da littattafai da jaridu da mujallu da duk wani abin karatu da ka sani a doron kasa. Ko’ina ka shiga kuma ga komfuta nan, ga teburan zama na musamman , ga mashin na photocopy nan kyauta, domin sun yi dabarar da duk wanda aka ba adentiti kad na jami’ar to cikin katin akwai kudi jibge na kwafar duk abin da kake so. Malamai nasu daban, da yake mu an dauke mu a matsayin malamai, garabasar da yawa take. Don haka duk inda za mu shiga domin kwafe abu lambarmu ta malamai masu bincike za mu sa wa injin din mu yi ta kwafar abin da muke so, ba mai ce da kai uffan.