Ashe Turawa mutane ne? (8)
Domin in tabbatar da gaskiyar lamarin, sai na nemi littafin Ruwan Bagaja, bugun farko, wanda ban taba gani ba, na shiga kwafewa, sai da na nade shi kaf, ba wanda ya dube ni, balle ya ce da ni ci kanka, na dubi kudin da suka rage na kwafe wasu littattafai da makamantan su da dama, […]
Domin in tabbatar da gaskiyar lamarin, sai na nemi littafin Ruwan Bagaja, bugun farko, wanda ban taba gani ba, na shiga kwafewa, sai da na nade shi kaf, ba wanda ya dube ni, balle ya ce da ni ci kanka, na dubi kudin da suka rage na kwafe wasu littattafai da makamantan su da dama, duk da haka sai na ga ina da sauran fam 249 da kwabbai masu yawa; ka san ko nawa ke nan a kudin Nijeriya? Dubu 64,740!
Wani abin karin dadi ba kuma shi ke nan ba, idan ka lamushe wadannan kudade akwai wasu fam 250 an ajiye na ko ta kwana.
Ni dai a wannan ranar azumi ne kurum ya hana ni yin katabus wajen kwafe abubuwa, duk da haka sai da na cinye kwalin takarda uku, shafi 1,500, kafin na je gida, na sha ruwa! Ganin wannan garabasa ta sa nan take sai na ji wani karin dadi ya rufe ni, domin kuwa ga inda Allah ya kai damo ga harawa, zai ci, kuma ya yi birgima!
Shi dai wannan wuri da muke ciki na ajiyar littattafai da kayayyakin karantawa, yana dauke da littattafai da ire-iren su sama da milyan biyu da dubu 200. bangaren al’amuran Afirka kadai hawa guda aka ajiye masa inda ake da littattafai masu tarin yawa, wasu ma da ban taba sanin akwai su ba. Yaya aka yi na san da haka? Abin da na fara yi shi ne laluben abin da ke cikin wannan hawa domin sanin me ke a cikin dakin dangane da Afirka, domin a lokacin na san yadda zan bullo musu! Na shiga cikin komfuta ne ina ta lellekawa da duddubawa, sai kuwa da na yi kusan kwana bakwai ban kai karshen su ba.
Da yake ban san yadda kan dawan garin yake ba, ga kuma azumi a bakina, ina gama kwafe abin da zan iya da kuma leke-leke a komfuta sai na kama hanyar gida don in shirya abin buda baki da sahur. Ina bisa hanya ne na san cewa lallai na jawo wa kaina da na sa kananan kaya, domin kafin na isa gida, ji nake kamar wanda ke tafiya cikin ruwan sama, sanyi ya yi mani kamun da ban taba jin irin saba. Na kosa in shiga gida, amma kuma da na tuna cewa cikin gidan ma sanyin ne sai na ji raina ya kara baci, an dai riga an rubuta a jikin kofar kowane gida cewa ba za a kunna iyakondishin ta zafi ba sai ranar 1 ga Oktoba, lokacin kuwa duk muna 26 ga Satumba ne! Na ce da kai na Ibrahim za ka ga tasku na tsawon mako guda kenan.
Haka na daddaga na isa gida, na ja kofar gida na tamke. Na shiga daki, na samu bargo na toshe bakin kofar dakin, na bi duk inda wata wagegiyar taga take na sa bargo na kara toshe inda sanyi yake iya shigowa, na ci sa’a a cikin suton gidan akwai barguna da zannuwan gado sama da biyar, saboda haka ban sami matsalar abin rufa ba. Ni dai ban san lokacin da aka kira sallar magariba, idan ma an kira to ban ji ba, in ma akwai masallaci a kusa ke nan, domin kuwa ban ga alamar sa ba.
Na kintaci lokacin sallar magariba, na bude baki da shan shayi, sa’annan na dubi takardar da ke like a jikin bango, na ga an ce akwai abincin sayarwa a kasan ginin ga mai bukata. Ba don ina so ba, dole ta sa na rarrafa kasa in ga abin da suke da shi. Na shiga cikin wurin sayar da abincin, katon wuri ne, ga ’yan uwana masu bincike da nazari da ke zaune a wurin kowa yana dauke da tire, ya bi layi, zai sayi abin da yake so. Ni ma kamar dan birnin Rum, na yi yadda kowa ya yi. Sai dai da alama duk wanda ke wurin ya san abin da zai ci, kila in ban da ni.
Ba wani abu ya sa ni cewa haka ba, sai ganin cewa wasu za ka ga suna diba da kan su ne, wasu su ce a zuba wancan, a hada da wancan, a yamutsa da wancan. Ka ga mutum dauke da abinci, shi ba na ciyar da tunkiya ba, shi kuma ba na ba kurege ba, domin kuwa kayan zaki ne, kimshe da ganyaye kala-kala, a cikin kwano guda!
Na dai bi layi gabana na faduwa domin kuwa ban san yadda za a kare ba idan na na rasa abincin da zan ci daga abubuwan da ke barbaje a ko’ina. Da aka zo kai na na dubi abin da ke rubuce a takardar kuku, sai na rasa abin yi, duk abin da ke wurin ba wanda zan iya lasawa, ko dai ka ga an ce wannan abincin na wanda bai cin nama ne, ko kuma a ce da kai, wannnan naman an yi masa wanka da giya ko kuma wannan miyar da alade a cikinta. Na yi tsaye na rasa yadda zan yi, ga shi kuma na tsare wa na baya hanya, dole na gusa, rike da tire na rasa yadda zan yi. Can wata daga cikin kukun da ke wurin da alama ko ‘yar Pakistan ko kuma Bangaladashi ce, ta yo inda nake tsaye rike da tire, ta ce da ni, ‘Halal, halal?’. Nan take na ji wani dadi ya rufe ni, ina kada kai ina ce da ita, ‘shinkafa, shinkafa,’ cikin Ingilishi. Da alama ta fahimce ni, nan take ta nuna mani wani tebur, na yi can, ga dai shinkafar, amma ba miyar ci, sai na hangi soyayyen dankalin turawa, na ce ta hada mani su, ta hada, na ce miya fa? Ta ce sai waccan da na baro, ita kuma ba halal ba ce! Na ce to da me zan ci shinkafar da dankalin? Ta nuna mani wani tangaran, na leka na ga wata miya tamkar an so a yi farfesu, an kasa, sai wani yauki take yi. Na zuba cikin shinkafar na ga ba abin da ya fito a fili irin na miya, na sake ambulawa wai ko na ga hasken miya, ina! Yadda ka san na zuba romo ne a miyar.