Ashe Turawa mutane ne? (9)
Haka nan na biya fam uku (wato Naira 780), na koma daki domin na kwashi gara. Koda na zauna na dandana abincin sai na ce da kaina ‘lallai Iro ka kawo kanka inda za a kashe ka,’ domin kuwa shinkafar ba ta dahu ba, dankalin kuma sanyi karara, romon da na zuba kuwa ba gishiri […]
Haka nan na biya fam uku (wato Naira 780), na koma daki domin na kwashi gara. Koda na zauna na dandana abincin sai na ce da kaina ‘lallai Iro ka kawo kanka inda za a kashe ka,’ domin kuwa shinkafar ba ta dahu ba, dankalin kuma sanyi karara, romon da na zuba kuwa ba gishiri ciki, dole na ture kwanon abincin, na shiga tunanin da me zan yi buda-baki da me kuma zan yi sahur da asuba, ko kuwa ta-mike zan yi baki daya?
A wannan rana sai na ji ina ma a ce ban kawo kaina kasar ba, ga dai sanyi ya rufe ni cikin daki, ga kuma yunwa za ta kashe ni, ban ji ba, ban gani ba! Na rasa abin yi dole ta sa na kwanta ina tunanin mafita.
Bayan wani lokaci can sai na ji ana kwankwasa kofa, na ce ko wane ne kuma ya zo ya dame ni, domin kuwa tashi zuwa bude kofar gidan ke da matsala gare ni. Amma da yake ba wani da ya san na zo Ingila, dole ta sa na fito daga daki na bude kofar zauren sai na ga Dokta Moses (abokin tafiyata) tsaye yana mani murmushi. Ya ce ya zo ne ya ga yaya na karasa da batun buda-baki, nan sai na ji tamkar na fashe da kukan dadi, domin kuwa na baro shi a ofis ne, shi zai wuce gidan matarsa, duk da cewa an ba shi masauki nan inda aka sauke ni, amma ba nan yake kwana ba, can yake zuwa kusa da filin kwallon Arsenal da ke unguwar Highbury, na kwashe duk yadda aka yi da masu abinci na rattaba masa, sai na ji ya fashe da dariya, ya ce ai na san za a aika. Ya ce in taso mu tafi. Na kama wata jibgegiyar rigar da na sayo a Saudiyya lokacin aikin Hajji na sanya, na jawo takalma na bi shi haka nan cikin sanyin.
Muka fito daga masaukin, muka shiga wani shagon Indiyawa, ya ce ga shagon kaya nan, na shiga sayayyar duk abin da na ga zai iya ciyuwa gare ni. Na kwashi gwangwanayen kifi irin su Gesha da Sadin da madara da jus-jus da burodi iri-iri da kiret na kwai da ruwan sha da sukarin masu ciwon suga, da ayaba da lemu da inabi. Ni dai kwasa kawai nake, har Ba’indiyen na kallona kamar ya ga fatalwa. Na kwashi kaya tamkar dai idan na shiga gida ba zan fito ba. Na kwashi kayana na kai cikin gida, na zuba wasu a suto, wasu a firij, wasu kuma a bisa dirowar falo, sa’annan na koma na kwanta, na yi ajiyar zuciya, na ce an kada wannan magen, saura wata.
Da yake na kimtsa abinci, abin da kurum ya zo mani a rai shi ne yadda zan yi maganin sanyi. Saboda haka koda safiya ta yi ban leka ko’ina ba, domin kuwa na gani a cikin talabijin cewa sanyin bala’i za a yi wannan ranar, ni kuwa ban ga dalilin da zai sa in kai kaina makasa ba. Saboda haka na buga waya na shaida wa Dokta Moses ni dai ina gida ba zan fito ba, sai sanyi ya tsagaita, sai na ji ya sake fashewa da dariya, ya ce da ni ai ba a ma fara sanyin ba tukuna, ka bari dai karshen mako sai na zo na kai ka ka sawo kayan sanyi, na ce sai ya zo. Ya ce da gaske ba za ka fito ba ke nan, na ce ko alama a gaida madam, na ajiye waya.
Ina cikin gida har aka sha ruwa na dafa shayi na sha, na koma kan gado ina kallon tasoshin talabijin, in na kalli labarai in koma wadda ke yin fim, ko kuma kallon kwallo ko kuma tashar yara, har dare ya soma, can sai na ji waya ta kada, na ce wane ne kuma? Ina daga hannun wayar sai na ji muryar Farfesa Graham Furniss, cikin Hausar shi da za ka dauka Bahaushe ne tangaram, ya ce ‘Ibrahim ni ne Graham, gani nan kasa wajen tarbar baki.’ Ban yi wata-wata ba na ja takalmi na sauka kasa, na same shi muka gaisa, yana dariya ya ce da ni, Dokta Moses ne ya ce ka ce ba za ka fito ba saboda sanyi, kuma wai sai karshen mako za ku sayen kayan sanyi, shi ne na zo maka da wadannan kayan ko za ka gwada ka ga in za su yi ma, sai ka yi amfani da su kafin ka sai naka.’ Ka ji karimcin Bature, amma mai ruwan Hausawa. Da duba gabansa na gan shi da jakunkuna guda biyu masu kama da Ghana- must- go, sai na yi murmushi, na ce a raina can a gida an ce da ni kafin in zo Nahiyar Turai, Turawa ba su da zumunci da karimci, to ashe ba haka ba ne. Na yi masa godiya, na ce ko dai kila ruwan Kanawa da ya sha ne na shekara da shekaru a lokacin yana Najeriya, ya sa ya zama daban da saura. Ni dai ban tambaye shi a zahiri ba, ya kama min na hau injin kai mutum sama da kayan. Zai tafi na kwaso tsarabar da na zo masa da ita, ba komai ba ne irin littattafai da bai samu damar saye ba, lokacin da yake Najeriya ya yi murna, na raka shi kasa ya shiga mota ya koma gida.
Ina komowa na dubi abin da ya zo man da su, na ga cewa duk abin da ake bukata na kayan sanyi ya zo da su. Ga dai manyan rigunan sanyi guda biyu, da kwat-kwat manya-manyan guda uku da wandunan maganin sanyi guda biyu da safuna na kafa da hannaye da huluna da maratayai na wuya. Sai kurum na rumgume su na kwanta bisa a kan gado, murna ai ba sai na fada ba.