Asian Cup: Mata za su yi alkalanci a Gasar Kofin Maza a Qatar

A karon farko, mata za su yi alkalanci a gasar maza ta Cin Kofin Nahiyar Asiya da za a gudanar a kasar Qatar a 2024

Asian Cup: Mata za su yi alkalanci a Gasar Kofin Maza a Qatar

Yoshimi Yamashita

A karon farko mata za su yi alkalanci a gasar maza ta Cin Kofin Nahiyar Asiya (Asian Cup) da za a gudanar a kasar Qatar a shekarar 2024.

Hukumar Kwallon Kafa ta Nahiyar Asiya (AFC) ta sanar a ranar Alhamis cewa fitacciyar alkalin wasa ’yar kasar Japan, Yoshimi Yamashita, na daga cikin matan da za su yi alkalanci a gasar mazan.

Yamashita, wadda ta yi alkalanci a Gasar Kofin Duniya ta Maza ta 2022 a Qatar, za ta yi alkalancin a wannan karon ne tare da wasu mata hudu a gasar nahiyar Asiya da zai gudana daga watan Janairu zuwa Fabrairun 2024.”A karon farko a tarihi alkalan wasa mata za su su yi alkalanci a gasar kwallon kafar maza zalla ta nahiyar,” a cewar Hukumar AFC.A Agusta hukumar ta sanar da cewa za ta kaddamar da gasar cin kofin mata ta nahiyar Asiya daga shekara mai zuwa.

Hukumar ta ce a gasar mazan da ke tafe, za a yi amfani da na’urar VAR 100 bisa dari a karon farko.

Karon farko ke na da kasashe 24 za su kece raini a gasar, wadda a bana kasar Qatar mai masaukin baki ce ke rike da kofin.

Daga cikin kasashen da ake sa ran za su kayatar da masu kallo akwai Japan da Korea ta Kudu bayan da suka kai matakin ’Yan-16 a Gasar Kofin Duniya na Qatar 2022.