Asibiti na neman gudunmuwar kashi a kasar Sin
Wani asibitin yara da ke birn in Shangai na kasr Sin ya bayar da sanarwar neman gudunmuwar kashin mutane. Wannan sanarwa dai an baza ta ne a shafukan sadarwar zumunta na WeChat, al’amarin da ya samu dimbin goyon baya a tsakanin masu mu’mala da kafofin sada zumunta na intanet a kasar Sin.A sanarwar da aka […]
Wani asibitin yara da ke birn in Shangai na kasr Sin ya bayar da sanarwar neman gudunmuwar kashin mutane. Wannan sanarwa dai an baza ta ne a shafukan sadarwar zumunta na WeChat, al’amarin da ya samu dimbin goyon baya a tsakanin masu mu’mala da kafofin sada zumunta na intanet a kasar Sin.
A sanarwar da aka wallafa cikin wannan watan, asibitin ya bukaci lafiyayyun mutane da su bayar da gudunmuwar bahayar su ga asibitin. Sannan an bayar da takaitaccen bayani cewa, ana bukatar kashin ne don yin dashen kwayoyin halittu da ba a ganin su sai da tabaron likita ga marasa lafiya, da ke fama da ciwon hanji da matsalar narkewar abincin da suke ci.
A cewar wani likita, mai suna Pan, wanda aka dora wa alhakin kula da wannan lamarin, ya yi nuni da cewa, asibitin na amfani da dabarar dashen kashin lafiyayyun mutane, wato (Fecal Microbiota Transplant) – FMT a karo na farko wajen warkar da wani yaro da ya yi fama da daurewar hanji, wato colitis, cikoin shekarar 2013. Daga bisani asibitin ya ware sashen kula da lafiya kula da hanji, don haka ake tattara kashin lafiyayyun mutane, ta yadda za su dammar warkar da dimbin mutane daga cuta/Pan ya bayyana wa jaridar mtasan Beijin, ta Beijing Youth Daily, cewa, iyalan majinyata da jami’an kula da lafiya suna bayar da gudunmuwa a halin yanzu. Sai dai ya ce wannan ba zai isa biyan bukaytar da ake da ita ba, don haka asibitin ya yanke neman taimako daga dimbin jama’a. Ganin cewa matattar dashen kasha a hanji na wknzuwa ne cikibn sa’a biyu, sai aka kebenta al’amarin ga mutanen da ke zaune a birnin Shangai kawai.