Asibiti ya yi kuskuren kashe majinyata 200 a Austiraliya
Wani asibiti a kasar Austiraliya, ya aike da sakonnin tabbatar da mutuwar majinyata 200 da ke kwance a asibitin, duk da cewa suna nan a raye. Daga bisani hukumomin asibitin suka gano shirmen da aka tafka a asibitin na Austin da ke Austiraliya, wanda kuma birnin shi ne mafi girma na biyu a kasar baya […]
Wani asibiti a kasar Austiraliya, ya aike da sakonnin tabbatar da mutuwar majinyata 200 da ke kwance a asibitin, duk da cewa suna nan a raye. Daga bisani hukumomin asibitin suka gano shirmen da aka tafka a asibitin na Austin da ke Austiraliya, wanda kuma birnin shi ne mafi girma na biyu a kasar baya ga Melbourne. Asibitin dai ya yi kuskure kashe majinyatan, bayan da aka aike wa iyalansu da likitoci.
Wannan kuskuren kasha majinyatan ya auku ne a sanadiyyar amfani da wata masarrafan kwamfuta da asibitin ke amfani da ita, inda aka tsarata, da zarar an salami majinci ko kuma ya mutu daga asibiti, sai ta bayar da sanarwa, a cewar sashen aikewa da sakonni na asibitin Austin, a wata sanarwar da ta bayar.
Hukumar gudanarwar asibitin ta roki gafara kan wannan kuskure da ta tafka. “Muna neman afuwa ga daukacin majinyatan ake kwance a sassan asibitin da al’amarin ya shafa, musamman ma ganin cwa mun gano wannan kuskure,” a cewar sanarwar.
Ita kuwa kungiyar Jami’an Kula da Lafiya ta Austiraliya, ta nuna rashin amincewarta, musamman ganin cewa wannan al’amari ya haifar da tashin hankali ga iyalai da likitoci. Sai dai wani dan majalisa ya kare jami’an asibitin da suka tafka kuskuren, inda ya bayyana cewa, lamarin na nuni da dimbin aikin da ya yi wa jami’an lafiya yawa, kamar yadda Kamfanin Dillancin Labarai na Reuters ya ruwaito.