Asibitin Aminu Kano ya gudanar da dashen dodon kunne na farko
Aikin dai shine irinsa na farko a jihar kuma irinsa na biyu a Arewacin Najeriya.
Asibitin Koyarwa na Malam Aminu Kano dake Kano (AKTH) a karshen mako ya gudanar da dashen dodon kunne a kan mutum biyu a jihar.
Dashen dai an yi shi ne da nufin dawowa da mutanen jinsu bayan da a baya suka kurumce gaba daya.
Ana sa ran dai za su dawo su rika ji da zarar sun warke.
Aikin, wanda shine irinsa na farko a jihar kuma na biyu a Arewacin Najeriya ya gudana ne karkashin jagorancin wasu fitattun likitocin kunne daga kasar Jordan, Farfesa Al-Zoubi Firas da Dakta Davide Profefa da kuma tallafin wasu likitoci daga asibitin.
A cewar Farfesa Al-Zoubi wanda shine ya jagoranci aikin, dashen zai taimakawa marasa lafiyar wajen karbar sauti daga waje zuwa cikin dodon kunnen nasu.
Ya ce, “Na’urar za ta rika karbar sauti ne daga wajen kunne ta hanyar amfani da wata na’urar da aka dasa musu daga wajen, sannan ta sarrafa tare da aika wannan sautin zuwa dodon kunnen, zuwa jijiyoyin kunnen.
“Wannan wani gagarumin ci gaba ne da zai canza rayuwar marasa lafiyan daga wadanda basa ji kwata-kwata zuwa wadanda za su iya ji kuma su yi magana.
“Babban abin sha’awar shine zai canza rayuwarsu gaba daya. Har yanzu ba a cika yin irin wannan aikin a kasashe masu tasowa da dama ba, amma za mu yi aiki kafada da kafada da mutane da kungiyoyi masu zaman kansu don magance wannan matsalar,” inji Farfesa Al-Zoubi.
Ya yi alkawarin cewa za su ci gaba hada gwiwa da asibitin har sai lokitocinsa sun fara gudanar da aikin da kansu.
Shima da yake tsokaci, shugaban asibitin na Aminu Kano, Farfesa Abdulrahman Abba Sheshe ya ce sun jima suna mafarkin ganin wannan rana, inda ya ce yanzu mutane ba sai sun fita ketare ba tun da za a iya yi musu aikin a kudade masu rahusa.
Kazalika, shugaban sashen kula da kunne, hanci da makogwaro (ENT) na asibitin, Dakta Muhammad Ghazali Hashim cewa ya yi shekaru uku kenan suna yunkurin ganin an fara aikin.
Daga nan sai ya yi kira ga masu hannu da shuni daga ciki da wajen jihar da su tallafa wa marasa lafiyar don ganin an yi musu aikin saboda matukar tsadar da yake da ita.
Aminiya ta rawaito cewa wadanda aka yi wa aikin da suka hada da yaro mai shekaru uku da kuma wata yarinya mai shekaru shida ana sa ran su fara ji da zarar sun warke nan da wata daya.